Giaccherini ya koma Napoli da taka-leda

Image caption Emanuele Giaccherini

Dan kwallon Sunderland da kuma tawagar Italiya, Emanuele Giaccherini, ya koma Napoli da murza-leda kan yarjeniyar shekara uku.

Giaccherini mai shekara 31, ya koma Sunderland a shekarar 2013 daga Juventus kan kudi fan miyan shida da dubu dari biyar.

Ya buga wa Sunderland wasanni 43, ya kuma ci kwallaye biyar, inda ta bayar da shi aro a bara ga kungiyar Bologna mai buga gasar Serie A ta Italiya.

Dn wasan ya yi wa tawagar Italiya wasanni 29, ya kuma ci mata kwallo a karawar da ta yi da Belgium a gasar nahiyar Turai da aka kammala a Faransa.