N'Golo Kante ya koma Chelsea

Image caption N'Golo Kante ya bar Leicester City zuwa Chelsea kan fam miliyan 30

Dan wasan tsakiya na Leicester City N'Golo Kante ya koma kulob din Chelsea akan kudi fam miliya 30.

Dan kwallon ya kuma sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar.

Dan wasan, wanda ya buga wasanni 40 a kakar bara wacce Leicester ta lashe gasar Premier, ya koma kungiyar ne kan fam miliyan shida daga Caen.

Kante, mai shekaru 25, yana cikin tawagar Faransa da ta kai zagayen karshe na gasar cin kofin kasashen Turai da aka kammala kwanan nan.

Dan wasan yace, "Na ji dadi da na samu damar komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai.''

Ya kara da cewa, "Da ma na dade ina burin ganin hakan ya tabbata.''