Shaw ya dawo buga wa Man United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luke Shaw

Luke Shaw ya murmure ya kuma dawo buga wa Manchester United kwallo a wasan sada zumunta da ta yi da Wigan, bayan da ya yi jinyar watanni 10.

Rabonda Shaw mai tsaron baya, ya yi murza-leda tun karyewa da ya yi a kafarsa a cikin watan Satumba, amma ya buga zagayen farko a karawa da Wigan din.

Suma sabbin 'yan wkwallon da United ta dauko a bana, Henrikh Mkhitaryan da Eric Bailly sun fara yi wa United wasannin farko a fafatawar da aka yi a gidan Wigan.

United ce ta samu nasara a wasan sada zumuntar da ci 2-0, inda Will Keane da kuma Andreas Pereira ne suka ci mata kwallayen.

Zlatan Ibrahimovic, wadda ya koma United da taka-leda a bana, bai buga karawar ba, sakamakon hutu da aka bai wadan kwallon, bayan da ya buga gasar nahiyar Turai.