Tarihin Paul Le Guen dan kasar Faransa

Paul Le Guen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paul Le Guen ya rike kulob-kulob da dama a Turai

Mutumin da ya yi watsi da zaben da Hukumar Kwallon Kafa ta Nigeria ta yi masa domin ya kasance sabon kocin Super Eagles, Paul Le Guen, ya dade ana fafata wa da shi a fagen tamaula.

Kocin dan kasar Faransa, mai shekara 52, wanda da ace ya amince da sharuddan aikin da hukumar ta gindaya masa,to da zai samu taimakon Salisu Yusuf.

Daman dai jaridar kasar Faransa ta L'Equipe ta ce akwai yiwuwar kocin ya yi watsi da nadin na sa.

Le Guen ya taka leda a kulob din Brest, Nantes da Paris Saint Germain, sannan ya murza wa Faransa leda sau 17.

Kocin ya kuma kai tawagar Kamaru zuwa gasar cin kofin duniya da aka yi a Afirka ta Kudu a shekara ta 2010.

Ya kuma jagoranci kungiyoyi da suka hada da Stade Rennes, Olympique Lyonnais - wadda ta lashe gasar Ligue 1 ta Faransa sau uku.

Kazalika ya horas da PSG da Rangers ta Scotland, da kuma tawagar kwallon kasar Oman.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Salisu Yusuf ya lashe wasanni biyu da ya yi a matsayin kocin riko

Shi kuma Saliyu Yusuf, mutumin da ya kamata ya yi aiki tare da Le Guen din ya buga wa tawagar 'yan kasa da shekara 20 ta Najeriya kwallo, kuma ya rike tawagar Super Eagles a matsayin kocin-riko.

Da dai Le Guen ya karbi mukamin to da kalubalen da ke gabansa a karon farko, shi ne wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya da Najeriya za ta kara da Zambia a Lusaka a ranar 3 ga watan Oktoba.

Kasar na cikin rukunin B mai tsauri wanda ya kunshi Aljeriya da Kamaru wadanda, tare da Najeriya duka sun halarci gasar kofin duniya da aka yi a Brazil a 2014.

A yanzu Super Eagles na mataki 70 a jerin kasashen da suka fi iya taka-leda da hukumar Fifa ke fitarwa.

Kuma wannan ba karamin koma baya ba ne ganin irin rawar da kasar ta taka a baya.