NFF ta nada Paul Le Guen kocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paul Le Guen ya horas da kungiyar wasa ta Kamaru.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada dan kasar Faransa, Paul Le Guen, a matsayin kocin Super Eagles.

Hukumar ta kuma nada Salisu Yusuf, a matsayin karamin koci.

Wannan ya biyo bayan zaman da kwamitin hukumar ya yi a ranar Litinin.

Babu tabbas ko Salisu Yusuf, wanda shi ne kocin rikon kwarya na Super Eagles, ko zai karbi sabon mukamin nasa domin a baya ya shaidawa BBC cewa ba zai sake aiki karkashin wani ba.

Mutane uku ne dai aka zayyana sunayensu a jerin masu neman kujerar ta kocin Super Eagles.