Grigg da Pogba sun yi kan-kan-kan a Turai

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Portugal ce ta dauki kofi a 2016

Dan wasan Northern Ireland, Will Grigg ya samu kuri'u da yawansu suka yi dai-dai da na dan wasan tsakiya na Faransa, Paul Pogba, dangane da wanda ya cancanci zama gwarzo a gasar kwallon kafa ta turai.

'Yan jarida daga kungiyoyi 55 dai sun zabi 'yan wasa guda biyar da suka fi ko wadanne a gasar kakar da ta gabata.

Pogba na kungiyar wasa ta Juventus da Grigg na kungiyar Wigan sun zo na 25 kowannen su daga cikin 'yan wasa 37.

Gareth Bale da Lionel Messi kuwa sun yi kan-kan-kan a mataki na 10.

Pogba dai bai buga wasa ba a gasar Euro 2016, sai dai wakar da aka rera masa ce ta yi tashe.