Russia ta yi magudi a gwajin shan kwaya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 2014 ne aka yi gasar ta Olympics a Sochi da ke Russia.

Wani rahoto da hukumar Hana Shan kwaya lokacin wasanni ta Duniya ta fitar, ya nuna cewa kasar Russia ta yi rufa-rufa wajen gwajin shan kwaya mai kara kuzari da aka yi wa 'yan wasanta, a lokacin gasar Olympics ta 2014 da aka yi a Sochi.

Rahoton ya ce ma'aikatar wasanni ta kasar ce ta yi rufa-rufa lokacin daukar samfirin fitsarin 'yan wasan kuma har daga karshe aka batar da samfirin.

Rahotan ya ce tun a karshen shekarar 2011 zuwa lokacin London 2012 har kuma lokacin gasar ta Sochi da aka yi a 2014.

Shugaban Kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya, Thomas Bach ya bayyana rahoton da wani abu mai razanarwa wanda kuma ya bata kimar wasannin Olympics.

Mista Thomas ya kara da shan alwashin daukar tsauraran matakai wajen hukunta duk wadanda aka samu da hannu a badakalar.