Arsenal za ta sayi Rob Holding

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rob Holding a wasan da Bolton ya taka da Charlton Athletic

Kulob din Arsenal ya taya dan wasan da ya fi kowanne kwarewa na Bolton, Rob Holding, a kan kusan fan miliyan biyu.

Dan wasan mai shekara 20 ya kasance a jerin 'yan wasan Ingila 'yan kasa da shekara 21 wadanda suka lashe gasar Toulon a lokacin hunturu.

Holding shi ne dan wasan da ya lashe dan kwallon da ya fi kowanne a kulob din na Bolton, a kakar wasan da ta gabata.

Tauraruwar dan wasan ta fara haskawa tun a farkon wasannin kakar da ta gabata.