Rio 2016: Shin ko za a dakatar da Russia?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a fara gasar Olympics ta Rio ranar 5 ga Agusta.

A ranar Talatar nan ne ake sa ran Kwamitin wasannin Olympics na Duniya, IOC, zai sanar da kodai za a haramtawa 'yan wasan Russia shiga gasar wasannin Olympics da za a fara ranar 5 ga watan Agusta, a Rio, bisa dalilan wuru-wuru.

Hukuma mai hana shan kwaya mai kara kuzari a lokacin wasa ta nemi da a haramtawa 'yan wasan Russia shiga gasar Olympics da za a fara ranar biyar ga watan Agusta.

Hakan dai ya biyo bayan rahoton da hukumar ta fitar wanda ya nuna gwamnatin Russia ta yi rufa-rufa a lokacin daukar samfirin fitsarin 'yan wasan nata domin gwaji.

Rahoton hukumar dai ya gano cewa Russia ta shekara hudu tana irin wannan rufa-rufa.