Liverpool ta sayi Klavan daga Augsburg

Ragnar Klavan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Klavan ne dan wasa na biyar da Liverpool ta saya a bana

Liverpool ta sayi dan wasan baya na Estonia Ragnar Klavan kan yarjejeniyar shekara uku daga kulob din Augsburg na Jamus.

Dan wasan, wanda ya wakilici kasarsa sau 112, ya koma Ingila ne kan fan miliyan hudu.

Klavan mai shekara 30, ya murza-leda sau fiye da 100 a Augsburg tun lokacin da ya koma daga kulob din AZ na Holland a 2012.

Shi ne dan wasa na biyar da Liverpool ta dauka a bana.

Ya shaida wa shafin internet na kulob din cewa: "Na shafe shekara 22 ina fatan komowa gasar Premier, da kasancewa a wannan kulob mai cike da tarihi".

Kocin Liverpool Jurgen Klopp na son ya karfafa bayansa tun lokacin da ya sallami Kolo Toure, sannan ya sayar da Martin Skrtel ga Fenerbahce.

Kuma ba za a fara kakar bana ba da Mamadou Sakho wanda yake fama da rauni.