Man City za ta kara da Man United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara wasannin Premier a watan Agusta

A ranar 25 ga Yuli, Manchester City za ta fafata da Manchester United a wasannin sada zumunta kafin fara gasar Premier a watan Agusta.

Za dai ayi karawar ne a filin wasa na Bird's Nest da ke birnin Beijing na China.

Kungiyoyin da ke buga gasar Premier Ingila dai za su yi rangadi zuwa kasashe da birane da nisansu ya kai mil 172,413, domin buga wasannin sada zumunci tare da yawon bude ido.

Kungiyoyin dai za su yi rangadin ne kafin fara wasannin Premier na kakar kwallo mai kamawa.

Kulob din Tottenham ne zai yi tafiyar da ta fi ta kowacce kungiya nisa wato mil 22,468.

Wuraren da 'yan wasan Tottenham din dai za su je sun hada da Australia.

Chelsea ne kuma yake biye wa Tottenham, a inda 'yan wasansa za su yi tafiya mai nisan mil14,345.

Kungiyoyin dai za su kai ziyara kasashe 14, a inda za su buga wasanni 17 a Amurka.

Watford ce za ta yi tafiyar da ta fi ta kowacce kungiyar rashin nisa, a inda 'yan wasan kulob din za su yi tafiyar mil 1,632, domin su buga wasannin shida.

Leicester City kuwa mai rike da kambun Premier, zai fara taka wasansa da Oxford United, a filin wasa na Kassam.

'Yan wasan kuma za su taka leda da Celtic da PSG da Bercelona da dai sauran su.