Swansea ta amince da zuwan Birighitti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Birighini gola ne a Newcastle Jets

Swansea City ya rattaba hannu a kan zuwan dan wasan kasar Australia, Mark Birighitti, kulub din bayan da kwantaraginsa ya kara.

Dan wasan mai shekara 25 ya amince ya koma Swansea a kan kwantaragin shekara biyu, bayan da kwantaraginsa ya kare da kulob din Newcastle Jets na Australia.

A bara dai, Birighitti ya je kulob din Varese, a inda kuma a nan ne suka hadu da kocin Swansea, Gabriel Ambrosetti.

Birighitti ne dai na daya daga cikin masu tsaron ragar Newcastle Jets da suka fi yin fice.