An fara gasar kwallon guragu ta Nigeria

Image caption Kano ta ci Kaduna 5-1 a karawar farko na wasan

An kaddamar da gasar kwallon guragu da ake kira Para soccer karo na farko a birnin Kano a ranar Talata.

An bude gasar bana da fafatawa da mai masaukin baki jihar Kano ta doke Kaduna da ci 5-1 a rufaffen filin wasa da ke Kofar Mata.

Shugaban wasan kwallon guragu na Kasa Musbahu Lawan Didi ya ce wasan da suke yi zai taimaka wajen wayar da kan al'umma kan cutar Polio.

Haka kuma ya kara da ce war gasar za ta taimaka wajen kawar da bara da rage kalubalen da guragun ke fuskanta a rayuwa.

Shugaban hukumar wasanni na jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima, ya ce sun karbi bakuncin wasannin ne domin 'yan kwallon da za su wakilci jihar a gasar wasanni ta kasa da za a yi a cikin watan Nuwamba su kara samun kwarewa.

Kimanin jihohi 19 ne za su fafata a gasar da za a yi kwanaki 10 ana gumurzu a jihar ta Kano.

A filaye uku za a gudanar da wasannin da suka hada da filin da ke Ado Bayero Square da na Kofar Na'isa da kuma na kofar Mata.