Ko mata sun fi maza yawan magana mara ma'ana?

Mata a wani taro kan 'yancin fadar albarkacin baki Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mata na amfani da akalla kalmomi dubu 20 a rana, in an kwatanta da kalmomi dubu bakwai da maza ke furtawa. A kalla dai wannan kintace ne daga mashahuran littattafan kimiyya.

Kwararrun masana ne suka baza rahoton, kuma bayani ne da ke tabbatar da zaton da ake yi wa mata na bata kwanaki wajen tsegumi, yayin da maza suka jajirce kan hakan, ba tare da an tattauna ba. Ko haka ne hakikanin lamarin?

Za a iya kimanta surutu ta hanyoyi daban-daban. Za ka iya kai mutane dakin bincike ka ba su taken abin da za su tattauna akai, inda za ka dauki maganganunsu. Ko ka dauki maganganun da suke yi kullum a gida.

Za ka iya kididddige kalmomin magana da lokacin da ko wanne mutum ya sayar wajen magana, da yawan zagayowa kan mutum a wajen tattaunawa, ko kimanta kalmomin da ya yi a zagaye guda.

Ta hanyar cure sakamakon nazarin yara 73, masu bincike a Amurka sun gano 'yan mata na magana fiye da maza, amma kima kadan.

Ko wannan bambancin dan kadan ya bayyana lokacin da suke magana da iyaye, don bai bayyana a lokacin tattaunawarsu da abokai ba. Ta yiwu muhimmin lamarin ya bijiro ne kafin shekara biyu da rabi, ma'ana kawai bambancin na nuni da saurin maganar da maza da mata ke yi na bunkasar harshe ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Idan bambancin kadan ne a tsakanin yara, ya lamarin yake ga manya?

Lokacin da Campbell Leaper daga Jami'ar California da ke Santa Cruz, kwararren mai tantance alakar dabi'a da tunanin kwakwalwa ya gano bambanci kadan a tsakanin yara, sai ya bibiyi kadin nau'ukan binciken da dama (a meta-analysis) kan batun, ta bayyana maza sun fi yawan magana.

Sai dai a wannan karon bambancin ma kadan ne. Kuma ta tabbata karara nazarin dakin bincike da aka bai wa gungun mutane taken abin da za su tattauna a kai ya samar da dimbin bambance-bambance fiye da wadanda aka gudanar kan tsarin harkokin rayuwa.

Wannan na nuni da cewa ta yiwu maza sun fi natsuwa a yanyin da ba a saba ba, wato na dakin bincike.

Sakamakon aikin Leaper ya karfafi bibiyar nazari 56 da masanin sarrafa harshe Deborah da kwararren mai tantance dabi'ar zamantakewa da alakar aikin kwakwalwa Janice Drakich suka wallafa littafi a shekarar 1993 kan salon tattaunawar mace da namiji.

Nau'ukan nazarin biyu ne kawai suka gano cewa mata sun fi maza yawan magana, yayin da guda 34 suka nuna cewa maza sun fi mata yawan magana, a kalla a wasu wurare, ko da yake an samu sabani a wajen nazarce-nazarce al'amarin da ya haifar da wahala wajen kwatantata su.

Nazarin tattaunawar hakikanin harkokin rayuwa a al'adance ya fi wuyar sha'ani, saboda bukatar samun wadanda za su halarto a tattara bayanai kan tattaunawarsu.

Amma Masanin tantance dabi'a da alakar aikin kwakwalwa James Pennebaker na Jami'ar Texas da ke Austin ya bullo da wata dabarar daukar bayanai cikin dakika 30 na sautin surutai a ko wanne minti 12 da rabi.

Mutane ba za su iya kashe na'urar daukar magana ba, don haka ita ce mafi nagartar tsarin tattara hakikanin abin da ke faruwa.

A binciken da aka wallafa a mujallar kimiyya cikin shekarar 2007, Oennebaker ya gano cewa a sa'a'o'i 17 da mata ke farke gwajin da aka gudanar a Amurka da Mexico mata na furta a kalla kalmomi 16,215 yayin da maza ke magana da kalmomi 15,669. Haka wannan bambancin kadan ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ba daukacin ko wacce irin tattaunawa ke daukar salo guda ba. Ta yiwu muhimmin abin lura shi ne wane ne ke saurare.

Nazarin tantance tattaunawar garuruwan tarurruka da Janet Holmes ta Jami'ar Victoria da ke Wellington a New Zealand ta gudanar, ya nuna cewa maza ne ke tambayar a kalla kashi uku bisa hudu na tambayoyi.

Yayin da mata suka samu kaso biyu bisa uku a wajen masu sauraro. Su kansu masu sauraren sun rabu kan doron jinsi, inda maza dai suka tambayi kashi biyu bisa uku na tambayoyin da aka yi.

Duk da cewa daukacin hujjojin sun saba wa juna, an ja mu zuwa ga cewa mata sun fi yawan magana.

A gaskiya dai bangare daya na rayuwa ne kawai ake sa ran samun dimbin bambance-bambance a tsakanin jinsin, amma in aka dauki gundarin binciken, sai a ga cewa, maza da mata sun fi kamanceceniya da juna fiye da yadda aka fi sani da aka yarda da shi.

Da masu bincike suka ruwaito a farkon wannan shekarar cewa mata 'yan shekara hudu sun kwashi kaso 30 cikin 100 na nau'in abincin protein da ke da muhimmanci ga bunkasar harshe da iya magana a wani bangare na kwakwalwa, wani yanki na mashahuran kafafen yada labarai sun yi saurin bayyana lamarin a matsayin hujjar da ta nuna mata ba sa iya tsagaitawa da magana.

Gaskiyar lamari binciken bai bayyana komai game mata ko maza a kan lamarin ba. Muhimman mutanen da suka halarta magulmata ne (masu tsegumi), amma an gwada maza da mata 10.

Su ma wadanda suka rubuta sakamakon binciken sun yi gargadi kan yawan karatun nazarin, da cewar ko kimar bambance-bambancen da ke tsakanin mutane yawan 'protein' na da tasirin a bunkasar sarrafa harshe abin bibiya ne a binciken da za a gudanar nan gaba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ko daga ina aka samo cewa maza na furta kalmomi 7,000 a rana mata kuwa 20,000? An zakulo su ne daga littafi mai taken Kwakwalwar mace (The Female Brain), wanda Louann Brizendine ta wallafa a 2006, kwararrriyar a fannin sakonnin kwakwalwa a Jami'ar California da ke San Francisco, ana ta yawan nazarinsa.

Lokacin da Mark Libermann, Farfesan sarrafa harshe a Jami'ar Pennsylvania ya bi bahasin amfani da kididdigar alkaluma, wadanda akwai sakacin dogara da littattafan bayanai, Brizendine ya amince da shi, inda ya yi alkawarin tsame su a wallafar littafin da za a yi gaba.

Liebermann ya yi kokarin gano tushen kididdigar lamarin ya ci tura, sai dai kwatankwacin irin wannan ikirarin a shekarar 1993 ya bayyana a karamar makalar sharawarin aure. Babu kimar tabbatacciyar hujjar kimiyya a ciki.

Labarai masu alaka