Ko madara na kwantar da yamutsin ciki?

madara Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption madara

Sa'adda duk tsananin rashin lafiya ya hanaka cin abinci ko murzawar ciki, abu mafi sauki ka kwankwadi kofin madara mai kauri don kwantar da yamutsin ciki?

Tana saukaka zafin ciki, ko ba komai ka samu abinci mai gina jiki.

Tsawon shekaru ana amfani da wannan magani a kasashen da madara ta shahara.

Sai dai a shekarun 1980, likitoci kan umarci masu fama da gyambon ciki na hanji su sha madara don ta saukaka musu rugugin ciki.

A gaskiya madara tana da sinadarin acid kadan, amma bai kai yawan iskar rugugin acid din da ciki ke fitarwa ba.

Don haka aka dade da dauka cewa madara na narkar da karfin rugugin acid da saukake zafin ciwo.

Madara na taimakawa wajen samar da saukin wucin gadi wajen kwantar da rugugin iskar acid, amma bincike ya nuna cewa madara na kara tuttudo yawan acid wanda zai iya sanya maka rashin lafiya bayan samun saukin wucin gadi.

A shekarar 1976 managarcin binciken da aka gudanar kan wasu mutum 10 da aka yi gwaji kansu don kawo karshen lamarin.

Da ba su ci komai ba, sai aka dura musu madara ta siririn bututtu ta hanci. Bayan sa'a guda aka zuko abin da ke cikinsu waje, inda aka auna yawan rugugin iskar acid cikin kowane minti biyar.

Masu binciken sun gano cewa madara na haifar da karuwar rugugin acid cikin sa'a uku, al'amarin da ke tabbatar da dalilin da ya sanya mutanen da ke fama da gyambon ci (ulcer) ke jin zafi sa'a'o'i kadan bayan cin abinci.

Ba madara kadai ba. Bincike ya kwatanta gahawa (coffee) da shayi da giya da madara, inda aka gano duk suna tuttudo da karuwar acid.

Barasa da madara na da matukar tasirin rugugin, al'amarin da ke nuni da cewa, wani abin mamaki ma'aunin tantance kimar rugugin acid (PH) a ruwa ba shi da sirrin gano yadda ake samar da shi.

Shin wadanne sinadarai ne a cikin madara da ke haifar wa cikin rugugin acid? Masu bincike a 1976 sun bi kadin (gudajin kakiden kitsen) manshanu wan da suka kwatanta da madara mai manshanu da wadda bata da shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daukacin nau'ukan biyun sun haifar da acid.

Ko mene ne tasirin sinadarin Calcium?

Da aka yi gwaji da madara mai karancin calcium, an samu karancin acid, amma akwai yanayi na daban. Marasa lafiyar da ke fama da gyambon cikin hanji, amma alamu ba su nuna ba, sun fi samar da sinadarin acid.

Sauran sinadarin da ka iya hana madara kawar da yamutsin ciki shi ne 'Protein Casein' Shi ma ana ganin yana fitar da sinadarin 'gastrin' wanda ke shawo kan bijirowar rugugin acid ko sanya wa kwayoyin halittar ciki karsashi, wadanda ke da tasirin fitar da acid.

Ko ta wace fuska, an daina bayar da madara a matsayin maganin gyambon ciki saboda akwai yiwuwar tasirinta ya zama sabanin kawar da zafin ciwo.

Za ta iya ta'azzara tsananminsa. A shekarar 1986 marasa lafiyar da ke fama da gyambon ciki sun shafe makonni hudu a asibiti ana yi musu magani a matsayin gwajin shawo kan matsalar.

Daya daga cikin rukunin mutanen da suka yi sa'a madara kawai aka rika ba su - lita biyu kowace rana, wadda aka rika kara wa sukari idan sun bukata.

Daya rukunin kuwa an rika ba su abinci a asibiti, kuma dukkansu an rika ba su kayan marmari na 'ya'yan ita ce, ta yadda aka samar da daidaiton yawan makamashin da rukuni biyun ke samu.

A karshen makonni hudu an yi amfani da na'urar duba gyambon ciki.

Muhimmin al'amari shi ne mutane da aka rika ba su abinci mai kyau sun warke, sai wasu 'yan kadan da suka ji sauki a rukunin masu shan madara.

Alamu sun nuna madara ta hana su warke.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption madara

Idan kana da lafiya, har yanzu yana da kyau ka rika shan madara, domin tana samar da nau'in Protein da sinadarin Calcium.

Sai dai kwankwadar madara da yawa na haifar da matsala?

A shekarar 1980, manyan mutane 21,000 a birnin Tromso da ke qasar Norway an yi musu gwajin lafiya wanda aka ci gaba da bibiya har tsawon shekara bakwai, inda mutum 328 suka kamu da gyambon ciki.

An gano cewa yawan shan madara (akalla kofi hudu ko fiye) ta yiwu ya haifar musu da cutar, musamman a tsakanin maza.

Sannan babu bambanci ko kofin cike yake da gudajin manshanu ko babu.

Ko da yake madara na yi wa ciki lullubin wucin gadi, don haka yawan rugugin acid a ciki kan sanya ka dan ji sauki, sai dai saukin ba zai dade fiye da mintuna 20 ko fiye da haka ba.

Wannan na nuni da cewa madara na da alfanu, amma ba kawar da yamutsin ciki ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images