Babur din da ke jin kansa kamar mota

Hakkin mallakar hoto trefor

Babur din Tripl , mai kafa uku, kirar kasar Denmark, wanda ke jin kansa kamar mota yana aiki da lantarki ga kuma wurin dakon kaya fiye da mota samfurin Marsandi (dafa-duka ko doguwa) E-Class.

David K Gibson ya yi kicibis da babur din.

Hakkin mallakar hoto trefor

A duk lokacin da ka bukaci a kawo maka wani kaya da ka saya daga wani kanti ko gidan abinci na makulashe, hakan na nufin kara cika titunan cikin birni. Wani ne zai taso takanas ya kawo abin har kofar gidanka, wanda hakan na nufin karin cunkoson abin hawa da karin kara (hayaniya) da kuma hayaki mai gurbata yanayi.

A kan hakan ne wani kamfanin Denmark, Trefor Drive ya samar da mafitar kauce wa kusan dukkanin wadannan matsaloli, ya kirkiro da wannan babu mai taya uku, wanda yake iya dibar kaya kamar yadda mota za ta iya.

Wannan babur (tripl), mai tayoyi biyu a gaba da daya a baya, wanda kuma yana amfani da wutar lantarki ne, yana iya gudun cin kilomita 28 a sa'a daya.

Tsawonsa ya kai kafa takwas, fadinsa ya kai kafa hudu, nauyinsa ya kai kilogram 301.185, tayarsa ta baya ce inji ke juyawa, kuma ba kamar sauran wasu baburan masu kafa-uku-uku ba shi yana iya yin baya kamar mota.

Idan aka yi masa cajin lantarki na sa'a takwas, ko kuma idan ana sauri da wata cajar tsawon sa'a biyar da rabi, zai yi tafiyar nisan mil 60 ko kuma kilomita 96.5606, wanda hakan ya isa ya yi aikin kai kayayyaki a tsawon rana a cikin birni.

Hakkin mallakar hoto Trefor

Za a iya sauya akwatin dibar kayan daidai da yadda ake bukata, kamar ko kayan sanyi za a dauka ko masu dimi ko ma dai wane irin kaya ne.

Akwatin na iya daukar kaya a murabba'in fadin kafa 36 kuma mai nauyin kilogram 199.581, wanda hakan ya fi abin da doguwar mota(dafa-duka) sanfurin Marsandi kirar E-class za ta iya dauka.

Tsarin kirar babur din ba ga birane kadai ya dace ba har ma da mutane, ta yadda mutum zai iya hawa a saukake ba sai ya daga kafa sama, kamar yadda ake hawa keke mai sangalali ko babur ba.

Hakkin mallakar hoto Trefor

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The motor scooter that thinks it's a van