Abubuwa 10 da za a rasa a zamanin mota mai tuka kanta

Hakkin mallakar hoto AP

Mota me tuka kanta za ta yi wa motar da direba ke tukawa abin da ita mota mai direba ta yi wa jaki da doki da kuma keken doki.

Ga binciken Matthew Phenix

Ko an ki ko an so, mota maras direba, mai tuka kanta tana nan tafe. A wurin bikin baje kolin kayan laturoni da aka yi a Las Vegas a wannan shekara ta 2016, kamfanin Marsandi (Mercedes-Benz), ya sanar da cewa sabuwar motarsa samfurin E-Class ta samu lasisin tuki na motoci masu tuka kansu na Nevada (Nevada Autonomous Driver's License), hakan ya sa ta zama motar farko (ta kasuwa) da ta samu lasisin.

A wannan taro dai sabon kamfanin da ke kera motoci masu amfani da lantarki, Faraday Future, ya bayyana cewa motocin da zai kera nan gaba, zai tsara su yadda za a iya sanya musu fasahar mota mai tuka kanta.

Haka shi ma kamfanin motoci na Koriya, Kia ya kirkiro da wata sabuwar motar mai tuka kanta mai suna Drive Wise.

To a yayin da muke tunani da shirin shiga zamanin motoci marassa direba, da nazarin yadda za su sauya tunaninmu a kan komai kama daga inshora (ta hadarin mota) da dokokin hanya, zai dace mu duba sauye-sauyen da wadanda za su yi amfani da motocin za su ci moriya, su ma.

Yaran zamanin mota mai tuka kanta, za su huta da maganar koyon tukin mota kamar yadda na yau suke yi, za su rasa da dama daga cikin dabi'u da mu'amulla da al'adu masu kyau da marassa kyau wadanda suka shafi tukin mota.

1. Tarar laifin gudu

Mota mai tuka kanta ba za a tilasta mata gudun da ya wuce ka'ida ba, wai don saboda wanda ke cikinta zai yi lattin zuwa wani wuri, ko yana jin fitsari ko bayan gida ba.

2. Lasisin tuki

Zamanin mota maras direba zai kawo karshen zuwa makarantar koyon tuki. Wanda hakan zai sa a rabu da lasisin direba, da maganar hoto maras kyau ko a ce hotonka ya yi wani iri kamar ba kai ba.

3. Batan hanya

Fasahar nuna wuri, mai amfani da intanet (GPS) wadda ta zama ruwan dare a yanzu, ballantana a mota maras matuki za ta taimaka, mutum ya daina batan inda za shi, musamman ma yadda a yanzu mutane ba sa iya amfani da takardar taswirar wurare. Saboda haka maganar ka bi wata hanya ko kwana ka bata a mota za ta zama tarihi.

4. Ajiye mota yadda bai dace ba

Yaran zamanin mota mai tuka kanta, za su rika fitowa daga mota ne kawai bayan ta kai su inda aka tsara mata ta je, sai su kyale motar ta nemi wurin da ya dace ta saka kanta ta tsaya. Kuma idan wurin da ake biya ne ta biya da kanta, ta hanyar 'yan danne-danne na lambobin asusun bankin mai ita.

Hakkin mallakar hoto Google
5. Nuna wa direba bambanci

A zamanin da ke tafe na mota maras direba, kowace mota za ta rika tafiya ne iri daya, saboda haka ba maganar nuna wariya ko bambanci misali ka ji an ce, ''ba mamaki ai mace ce ke tukin'' ko ''ai tsoho ne direban'' ko ''yaro ne ai direban'' ko '' direban kauye ne ba mamaki'' da sauransu.

6. Lotsa kumatun mota

Motoci marassa direba suna da fasaha ba ta sanin wurin da suke ba kadai, har ma ta yadda za su rika magana ko sadarwa a tsakaninsu da sauran motoci irinsu akai akai, domin kaucewa karo ko gogar junansu.

7 Mahaukacin gudu ko ganganci

Mota maras matuki ba za ta iya bin motar da ke gabanta ba gab da gab (bamba tu bamba kamar yadda wasu ke cewa a Hausa), ko taka birki kwatsam a gaban wata motar ba, ko ta sha kan sauran motoci marassa direba ba. Ba za su rika tafiya da gudun tsiya ko tafiya sannu-sannu ba, kuma ba za su taba kade ko kaza ba.

8. Satar mota

Mukulli? Haba wa! Ba dai a wannan zamanin ba, ai mota mai tuka kanta za ta kunna kanta ne daga zarar ta karanta zanen yatsunka, da daukar hoton kwayar idonka da kuma jin muryarka.

Akwai kuma wadda za a yi amfani da fasahar sadarwar zuciya da zuciya a matsayin mukullinta. Ma'ana za ta yi amfani da zuciyar mai ita ne kawai a matsayin mukulli.

Kuma za ta rika lura da yanayin wuri akai akai ta yadda za ta iya dauke kanta daga wuri ta gudu kafin barawo ya sace ta.

9. Kade dabbobi

Motoci masu tuka kansu ba za su rika taka-tsantsan da nuna cikakken sanin muhallin da suke ba kadai, za su zama masu kuzarin da ya fi na mutum ma, kuma wannan fasaha za ta iya taimakawa wajen ganin ba su rika kade dabbobi ba.

10 Mai lura da lokacin tsere

Ina amfanin iya sarrafa sitiyari idan mota ba ta da sitiyarin? Kuma mene ne amfanin na'urar tantance gudun mota idan duka motoci gudunsa daya? Haka kuma wasu abubuwan da za a rabu da su, sun hada da mugun tsere a titi da gudun gasar kawai tsakanin direbobi da makamantansu.

Hakkin mallakar hoto Google

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Ten things the driverless generation will never experience