Ana farfaɗo da tsoffin tayoyi a ƙasashen duniya

Hakkin mallakar hoto Simon Maina AFP Getty

A kowace shekara kusan tayoyi biliyan ɗaya da miliyan 500 ne na motoci manya da ƙanana ake zubarwa. Amma yanzu an samo wasu hanyoyi na sake sarrafa wannan shara mai wuyar kaudawa, ta hanyoyi masu ban sha'awa da inganci.

Ga nazarin Ken Wysocky

Abu ne da za ka dauka wani na banbarakwai ka yi tunanin cewa za a yi amfani da tsoffin tayoyi a matsayin wata hanya ta yin takalma na ado masu nagarta da kuma kujeru da tebura na ado a daki.

A yanzu daga Kenya zuwa Indiya zuwa Detroit zuwa Sweden, mutane masu dabara da basira da kuma tattali cikin sauki suna sarrafa daya daga cikin sharar da ta ke ruwan dare kuma mai wuyar kaudawa zuwa abubuwan ado da kare lafiya da kuma neman kudi.

Masu yin takalma a Kenya, yanzu sun bukasa sana'arsu ta yin takalma silifa masu kyau da inganci da ake kira da suna akala, da tsoffin tayoyi, inda za ka ga suna ta cinikinsu a titinan birnin Nairobi, a kan abin da ya kama daga dala biyu zuwa biyar, kusan naira 700 zuwa 1900, wanda hakan yake kasa da farashin sauran takalma da ake yi a masana'antu, amma kuma ya ninka na kamfani kusan sau goma inganci.

Shekara da shekaru an san 'yan kabilar Masai, wadanda suke kudancin Kenya da arewacin Tanzania, da amfani da irin wadannan takalma, wadanda ake kuma kiransu da suna 'thousand milers', ma'ana takalman tafiyar mil dubu, inda suke keta dazuka da su.

Za ka ga takalmin ya yi fice a intanet idan ka shiga shafukan masu talla ta intanet, e-tailers, inda za ka ga sunayen kananan masana'antu masu yin takalman kamar Maasai Treads da Akala Sandals da soleRebels, wadanda takalman mata na wadannan samfuran, wadanda aka yi dunduniyarsu da tsoffin tayoyi sun kai dala 80.

Akwai kuma kamfanin Detroit Threads, inda Rabaran Faith Fowler ta dauki salon yin wannan takalmi. A cibiyar yi wa al'umma hidima ta Cass Community Social Services a Detroit ta Amurka, malamar addinin kiristar ta dauki ma'aikata gommai aiki, wadanda suke sarrafa tsoffin tayoyi suke yin silifa da ake sayar da duk kafa daya a kan dala 25.

Kamfaninsu na Green Industries na samun tsoffin tayoyi kusan dubu 35 a duk shekara. Takalman da ake sayarwa jama'a a birane, wadanda suka gaji da sayen takalma na manyan kamfanoni, daliban jami'ar Michigan da ke Ann Arbor da kuma kwalejin Creative Studies da ke Detroit ne suke zayyana su.

Hakkin mallakar hoto Simon MainaAFPGetty Images

A Mumbai da ke Indiya, wani mai sana'ar yin takalman ne da sauran abubuwa, Anu Tandon Viera, ya kafa 'yar karamar masana'antarsa da ya sanya wa suna Retyrement Plan, inda ma'aikatansa suke sarrafa tsoffin tayoyi da sauran kayan shara da ake iya sake sarrafawa, inda yake yin kujeru da tebura.

A wata sigar kuma, wani kamfanin kasar Sweden mai suna Apokalyps Labotek, yana yin amfani da tsoffin tayoyi miliyan hudu ne da ake zubarwa a kasar a duk shekara, inda yake sarrafa su wajen yin ledar rufe daben daki wadda ake ado da ita.

Kamfanin yana nika tayoyin ne ya hada da wani garin robobin da wasu sinadaran ya yi roba ko ledar rufe daben daki wadda karfinta ya kai na irin takalmin tsoffin tayoyin da ake yi a Kenya (thousand miler).

A yanzu kamfanin Bridgestone da sauran kamfanonin taya suna kokarin kirkiro wata taya wadda ba za a rika buga mata iska ba, wadda kuma za a iya sake sarrafa ta, abin da zai kawo karshen matsalar sharar da tsoffin tayoyi ke jawowa, na rashin sanin yadda za a yi da sharar (in ban da takalman na yanzu), wadda ke da wuyar kaudawa fiye da motar boksuwaja kunkuru (Volkswagen Beetle).

To amma ga masu sana'ar sarrrafa tsoffin tayoyin kada hankali ya tashi, kan farg abar rasa abin da kuke sarrafawa kuna yin takalman da sauran abubuwa, domin an yi kiyasin akwai biliyoyin tsoffin tayoyi da suke watse a duniya.

Saboda wannann daya daga cikin sharar da ake sarrafawa ce wadda ba za ta kare ba a nan kusa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Around the world, discarded tyres tread again