Arziki rigar kaya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Sai dai idan iyayenka masu arziki ne, da wuya a ce a wani lokaci a rayuwarka ba ka taba fatan zama attajiri ba.

Burin wasu a rayuwa shi ne mallakar dimbin dukiya domin kece raini da sheke aya ko morewa rayuwa da mallakar manyan gidaje na gani na fada masu kayan alatu, ga motoci na alfarma da jiragen sama ga kuma tarin kudi da za su iya yin duk abin da suke so a kuma lokacin da suka ga dama.

To shin idan buri ya cika, dukiya ta taru, ya rayuwa take kasancewa ga irin wadannan mutane da suka taka tudun-mun-tsira? Za mu shiga wannan fage na tambaya da amsa domin jin yadda lamarin yake, ko zama mai arziki wani abu ne mai amfani?

A kan ce da tsiya gara arziki, to amma fa lamarin ba kamar yadda mutane suke tsammani yake ba. In ji wani.

Kudi su kan sa mutum ya sauya, wani ya zama na gari, wani kuma ya lalace.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Carol philo, ta ga yadda dare daya iyayenta da ke fama da fatara da talauci suka zama hamshakan attajirai bayan da suka bude wani kamfanin buga takardu a cikin wani daki a gidansu na kwana. Ribar da suka samu ta sa kudi ya shiga ransu sosai da sosai. Kullum burinsu shi ne kudinsu ya karu.

''Kudin ya shiga ran babata matuka, ba sa taba isarta,'' in ji Philo kuma bayan wasu shekaru sai zumunci a tsakanin iyalin ya katse.''

Ganin yadda rayuwa ta fatara da talauci da kuma ta arziki take gaba daya, sai in ce abu ne mai kyau mutum ya samu wadatar zuci, amma zama attajiri ba abu ne mai dadi ba.''

Shi kuwa Murat Morrison bai yadda da wannan ra'ayi ba. Ya samu dukiya lokacin da ya sayar da kamfaninsa na manyan motoci a shekarun 1990.

Ya ce, ''abin da ya fahimta dukiya za ta ba shi har abada, shi ne jin dadi, domin kudi zai sai maka wadannan abubuwa biyu.'' in ji Morrison

Sai dai kuma ya kara da cewa, ''jin dadi ba farin ciki ba ne ko kuma wadata, domin bayan 'yan shekarau sai na ji ni holoko kamar ba ni da komai.''

Hakkin mallakar hoto Global Witness

Ya ce,'' duk da cewa abu ne mai kyau ka samu jin dadi amma mafi gamsarwa shi ne farin ciki.''

Paul Buchheit kuwa ya kara da cewa, ''dukiya tana fito da mutum a san halinsa na gaskiya.''

Ya ce, ''a takaice tana kara bayyana mutum a kara sanin halayyarsa da yadda yake.''

Sannan ya ce, ''idan ya kasance kana da wani buri a rayuwa da ba kawai fatan ka samu kudi ka hole ba ko ka ji dadi kawai ba, to dukiya za ta ba ka 'yancin cimma burin nan naka.''

Arziki rigar kaya

Illar rayuwa cikin dukiya za ta iya fin amfanin dukiyar. ''Wata illa da ke tattare da dukiya ita ce, ba za ka iya yin korafi ko kuka na rashin wani abu ba sam-sam,'' kamar yadda wani da bai bayyana sunansa ba ya rubuta.

Ya ce, ''tun da mutane da dama sun dauka idan kana da kudi kafi karfin komai, ba za su dauka akwai wani abu da ke damun ka ba a rayuwa ko kuma kana da wata bukata, duk da cewa kai dan adama ne, mutane ba sa daukar ka haka.''

Hakkin mallakar hoto AFP

Sauran matsalolin da ke tattare da dukiya kuma su ne, bukatun abokai da 'yan uwa. ''Idan ka samu dukiya mutane da dama za su dora burinsu a kanka, zai yi wuya ka gane cewa mutum yana kaunarka ne ko kuma sonka ne don abin hannunka.'' in ji mutumin wanda bai bayyana sunan nasa ba.

Ya kara da cewa, ''idan ba ka yi aure ba to kana da aikin kokarin ganowa ko wadda za ka aura tana sonka ne don abin hannunka.''

Duk da haka kudi na da amfani;

Duk da matsalolin da ke tattare da dukiya ko kudi, wasu da aka ji ta bakinsu da dama sun ce yana da amfani matuka.

''Arziki ya fi rashinsa, amma kuma fa ba kamar yadda kake dauka ba.'' harwayau in ji wanda bai bayyana sunan nasa ba, wanda ya ce, ya samu dala miliyan 15 bayan sayar da wani karamin kamfaninsa.

Ya ce, '' abu na farko da za ka ji idan kana da arziki shi ne ba za ka taba samun damuwa ba cewa ba ka da kudi. Amma fa duk da haka akwai abubuwan da ba za ka iya saya ba, amma za ka yi ta burin ka kai matsayin da za ka iya sayensu. Kuma za ka rika sayen abubuwan ba tare da ka yi tunanin tsadarsu ba.''

Christopher Angus, wanda ya ce, ya samu dukiyarsa ne bayan da ya sayar da wasu kananan kamfanoninsa, cewa ya yi,'' gara in mallaki kudi da in rasa su, domin a shekara bakwai da ta wuce, kudi sun ba ni 'yanci da damar da mutane da yawa ba za su samu ba a rayuwarsu.''

Ya ce, ''misali a shekara daya kawai na dauki hutu na tafi yawan shakatawa sau 25, kuma a wasu lokuta na kashe dala dubu 20 a dare daya a otal.''

Karin buri

Idan mutum ya samu dukiya to burinsa sai ya karu. ''Komai yana da irin kalubale da ke tattare da shi. Yawan dukiyarka yawan bukatunka.''

Hakkin mallakar hoto TVP ROADS POLICING

''Idan a watan farko da samun dukiyarka ka sayi mota kirar Audi, ko ka yi kalaci a wani gidan abinci mai tsada, za ka ji dadi sosai, to amma da an kwana biyu ka saba da su, sai ka ji kana bukatar wasu daban wadannan ba sa burge ka kuma.'' In ji wanda bai bayyana sunan nasa ba.

Christopher Angus, wanda ya ce, ya samu kudin da bai ma san abin da zai yi da su ba tun yana dan shekara 20 da wani abu, ya ce yana samun dukiyar sai kuma abubuwa suka gundure shi.

Ya ce, '' ina samun kudin sai kuma na daina jin sha'awar da nake ji ta mallakar abubuwa na alfarma masu tsada wadanda kafin na samu kudin ba zan iya mallaka ba.''

''Sai na ji mota daya ta alfarma da sauran abubuwa ba su ishe ni ba, cikin shekara uku na sayi wasu motocin alfarmar guda biyar da wasu motocin na kasaita.''

'' Daga nan sai kawai na rika jin sha'awar sayen irin wadan nan abubuwa na kasaita domin in jawo mutane jikina su rika debe min kewa saboda abin da nake da shi da kuma abin da zan ba su.''

Dukiya tana sa kewa

Hakkin mallakar hoto AP

Wani mutumin kuma da ya mallaki sama da dala miliyan 20, ya ce, dukiya ta zamar masa wani nauyi. Ya ce, ya samu dukiyarsa yana dan sama da shekara 30.

Ya ce, '' burina shi ne na yi dukiya kuma na same ta, to amma da na same ta sai na ji daban, doki da zakuwar da na yi na same ta sai naga duk ba ta kai yadda na yi tsammani ba.''

Ya ce, idan da na samu dukiyar ne a hankali a hankali da nafi jin dadinta da kuma ganin amfaninta a rayuwata gaba daya.''

Ya kara da cewa, ''to amma duk da wannan ita dukiya idan ka same ta to fa ba ka son ka rabu da ita, ka koma gidan jiya, kana son har abada ka kasance da ita.''

Ga mai sha'awar karanta wannan labarin a Ingilishi latsa nan The downsides of being rich