Sirrin koyan wani harshe

Hakkin mallakar hoto Getty

Kai ne ka samu wata dama ta neman a dauke ka a wani aiki a kasar waje to amma kash ba ka iya yaren wannan kasar ba kuma ga shi lokaci yana kure maka. Ya zaka yi ?

Za ka ga abin kamar ba mai yuwuwa ba ne, amma kwararru a fannin harshe suna ganin abu ne mai sauki ka koyi muhimman abubuwa na yare a cikin 'yan makwanni kuma har ma ka kware a harshen na kasar waje a cikin

watanni.

Duk da cewa dai ba lalle ka kware a harshen ba ta yadda za ka iya fahimtar wakoki da karanta littattafan da aka rubuta da harshen na ainahi a cikin dan wannan lokaci, za ka iya sanin 'yan abubuwa na yaren da suke dai-dai da

bukatunka, ko da kuwa kana aiki ne da ofishin jakadanci ko wani babban kamfani.

Wasu mutanen ba sa shan wahala ko dadewa wajen sanin yadda za su dan tattauna ko hira akan wasu labarai na al'amuran yau da kullum da dan kasa a birnin Rum ko kuma 'yar tattaunawa da sabbin abokansu na aiki

Faransawa a birnin Paris.

Farawa;

Wani lokaci tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya domin yin aiki kan tilasta mutum ya san dabarun da zai bi wajen lakantar harsuna da dama.

Benny Lewis, wanda injiniya ne, ya koyi harsuna bakwai, da suka hada da Spaniyanci da Faransanci da Jamusanci, har ma kuma ya kusa lakantar wasu daga cikinsu kamar daman yarensa ne na gado ciki har da Sinanci.

Harshen farko na waje da Lewis ya koya shi ne Spaniyanci, wanda ya koya a shekara daya da 'yan watanni kawai, amma kuma ya koyi sauran harsunan ciki har da Sinanci a kasa da wannan lokaci.

Sirrin yad da ake koyon harshe;

Hakkin mallakar hoto Getty

Farko idan yana son ya koyi harshe yana rubuta abubuwa ne a takardu akan irin tambayoyi ko abubuwan da wani bako zai iya tambayarsa, wato yadda zai amsa wa duk wanda ya yi masa wata tambaya.

Yadda Lewis ya lakanci harsunan kasashe daban-daban na duniya har ta kai yana yin aikin tafinta ko fassara wasu rubuce-rubuce na aikin injiniya.

Kwararru sun ce amfani da kananan littattafan koyon harshe da kuma amfani da hanyoyin koyon harshe na intanet suna da amfani sosai a wannan mataki na koyon yare, saboda za ka koyi kalmomi ka kuma samu kwarin gwiwar

magana da masu harshen.

Lewis ya ce da farko matsalata ita jin tsoro ko rashin karfin halin jarraba magana da harshen, amma a hamnkali a hankali sai na saba.

Masana sun ce in dai kana son ka iya yare to dole ne sai ka kawar da tsoro ka zama mai karfin hali, baka damu da duk wani kuskure da za ka yi ba.

Micheal Geisler matamakin shugaban makarantun koyon harsuna na Kwalejin Middlebury da ke Vermont a Amurka ya ce, ''mutane da yawa ba sa ci gaba idan ba su bude bakinsu ba.''

Wato ba ta yadda za su ci gaba wajen iya harshe har sai suna jarraba magana da shi, ba tare da jin kunyar duk wani kuskure da za ka yi ba.

Lokacin da Lewis ya fara koyon harshen Spaniya ya ce, magana ya rika yi ba kakkautawa.

Ya ce, ''da farko na rika jirkita kalmomi to amma cikin 'yan kwanaki sai na fara fahimtar yadda yakama na yi, har ta kai zan iya shiga kanti in ce burushina na wanke hakori ya karye ina son a sauya min.'' Ya kara da cewa, ''duk inda

ka je mutane suna hakuri da kai.''

Sai ka dage;

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Geisler yana ganin dagewa ita ce hanyar kwarewa a harshen da ba naka ba cikin sauri.

Ya ce, idan ta dage ta hanyar karatu da sauraren rediyo ko magana da mutane za ka ga kana samun cigaba cikin hanzari.

A kwalejin Middlebury ana sa dalibai su rika shiga wasu abubuwa na daban da karatunsu, da suka hada da wasanni da wasan kwaikwayo a cikin harshen da suke koyo.

Ana amfani da irin wadannan dabaru da hanyoyi a makarantar harkokin waje ta Amurka da ke Washington, DC, wadda ke ba da horo ga jami'an diflomasiyyar Amurka da ma'aikatan harkokin waje na Amurkan na harsunan waje.

Masana na ganin idan kana kokarin magana da harshen da kake son koyo a kai a kai za ka lakance sosai cikin dan kankanin lokaci da za ka iya hira da shi sosai.

James North na makarantar harkokin wajen Amurkan, ya ce ana karfafa wa dalibai gwiwa su rika mu'amulla da 'yan kasa, ma'ana masu harshen.

Ya kara da cewa, ''kana bukatar ba wai ka sa kanka ba kadai har ma da zuciyarka.'' Misali za ka iya sa kanka wani aiki na taimakon jama'a ko ka rika mu'amulla da 'yan garin a wuraren cin abinci da unguwanni.''

Wani babban abu ma shi ne a manyan birane na kasashen Turawa, akwai shirye-shirye da ake yi sau da dama a cikin mako, inda ake hada hada masu koyon harshe da sauran mutane suna tattaunawa da mua'mulla da juna.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Haka kuma akwai shafuka na intanet na koyon harsuna da suka hada da, italki.com da lang-8.com da kuma voxswap.com.

''Da koyo akan iya.'' in ji North, wanda ya kara da cewa, to amma kana bukatar duk abin da kake koyo ya kasance kana da wanda zai ce maka wannan ka yi daidai amma wannan ga yadda za ka yi ko za ka ce.

Kana bukatar tambayar wadanda kake magana da su, abin da ka fada daidai ne ko ba daidai ba ne, kuma ka nuna musu cewa ba za ka damu ba idan sun gyara maka yadda kake furta kalmomi da kuma ka'idar nahawun harshen.

Ko da ike dai masana sun ce ba sai ka damu da maganar nahawu ba a wannan mataki na koyo.

Lewis ya ce, ka yi amfani da harshen da farko a gaba ka mayar da hankali kan nahawu.

A lokacin da kai matsayin ka fahimci nahawun, ya bayar da sunayen shafukan intanet da za a iya amfani da su domin koyon nahawun.

Wadannan shafukan sun hada da radiolingua.com ko languagepod101.com

A yayin da kake koyon harshe ka tabbatar kana sauraren rediyo da kallon talabijin na harshen da kake koyo.

Masana sun bayar da shawarar cewa, idan a matakin farko kake, sai ka rika karanta littattafan yara da kallon finafinan da ka sani wadanda aka yi da harshen.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Secrets of learning a language — quickly