Ko akwai matakan cin nasara?

Hakkin mallakar hoto alamy

Idan a ce akwai wasu ka'idoji ko matakan da za a bi da wadanda za a kauce wa da za su kai mutum ga nasara ya zama jagora na gari, za ka bi?

Shin akwai wata dabara ta cimma nasara ga shugaba? Akwai wasu ka'idoji da matakai da tabbas mutum ya bi su ko ya kiyaye da su zai kai tudun-mun-tsira? Ko kuma akwai jerin wasu abubuwa da mutum zai guje wa ya kauce fadawa matsala.

Watakila za a iya cewa akwai duka wadannan. Wannan batu ne da masana suke da ta fada a kai.

Ga abin da wadansu masanan suka bayyana.

James Altucher, dan kasuwa:

Kafin ka fahimci nasara, sai ka lura kura-kuran da wadanda suke yin rashin nasara ko faduwa a kai a kai suke yi, in ji Altucher, a rubutun da ya yi mai taken 'Abubuwa 10 da mutanen da suka yi nasara ba sa yi' (10 Things Successfl People Never Do).

Ya lissafa wasu daga cikin abubuwan da mutanen ba sa nasara a harkokinsu suke yi su kuma sake maimaitawa wadanda ke jawo musu wannan matsala.

''Sun yarda da ita kanta kalmar rashin nasara. Rayuwarmu ba ta kai wa har tsawon lokacin da za mu yi rashin nasara, kamar a ce wata duniya yau ta kai shekara biliyan hudu amma ba ta haifar da wani abu mai rai ba, ba abin da zan kira wannan duniya sai in ce ta kasa wato ba ta yi nasara ba,'' in ji Altucher.

''Duk wani abu da ka sani gwaji ne. kana kuskure kana gyara. Idan ka yi kuskure yau kuma ka sake yi gobe, hakan zai ba ka damar gane kura-kuranka ka kauce musu''

''Mutanen da ba su ci gaba ba, ko marassa nasara ba sa alkawari mai yawa kuma suna samarwa da yawa fiye da kima.

Ba wanda ba a yi wa karyar cewa wai idan kana son ka ci nasara, sai ka zama mai alkawari kadan da kuma samarwa da yawa.

Wannan shi ne rashin amana mafi muni,'' kamar yadda Altucher ya rubuta.

Ya ce, ''Dole ne ka yi alkawari fiye da kima kuma ka samar fiye da kima. Alkawari fiye da kima shi zai bambanta ka da mutanen da ba sa alkawari fiye da kima.

Kuma samarwa fiye da kima ita za ta bambanta ka da mutanen da suke samarwa kawai.

Abu ne mai sauki ka dan yi alkawari fiye da kima kuma ka dan samar fiye da kima saboda ba wanda yake yin hakan.''

''Marassa nasara su ne ki karbar dukkanin bashi. Marassa nasara wadanda suka kasa ba su da madogara,'' in ji Altucher.

''Ka rika ba sauran mutanen duk bashin a ko da yaushe. Ka zama kai ne mai bayar da bashi. Kamar dai banki kawai. Bashi kamar kudi ne. Idan kai ne banki a karshe kai ne za ka zama da dukkanin kudin.''

''Ba su da littafin rubuta abubuwa. 'yar takarda kawai nake rikewa ko da yaushe. In a da irin wannan 'yar karamar takadda sama da 100,'' kamar yadda ya rubuta.

Sau nawa wata babbar dabara take zuwa tunaninka kuma kana ganin 'dabara ce mai kyau ba zan taba manta ta ba' sai kuma ka manta ta?''

Marshall Goldsmith wanda marubuci ne kuma kwararren mai bayar da horo:

Saboda karuwar bukatar mutane a kan shugabanni, ba ka da wadataccen lokacin da za ka mayar da hankalinka wajen aiwatar da sauye-sauyen da kake bukata aikinka ya yi nasara,'' kamar yadda Goldsmith ya rubuta a kasidarsa mai taken, 'Abubuwa takwas da shugabannin da suka yi nasara suke yi'.

''Za ka ga cewa yayin da burin da fatan mutane a kanka ke karuwa, ba ka da isasshen lokacin samar da cigaba, kuma bukatar inganta kwarewarka ta shugabanci na karuwa fiye da da.''

Domin maganin hakan, kamar yadda ya rubuta,''dole ne ka yi amfani da abin da ke kewaye da kai kuma ka nemi taimakon na kusa da kai...dle ne ka nemi taimakonsu''.

Domin samun yin hakan, kuma ka ci gaba da bunkasa a matsayinka na shugaba, kamar yadda Goldsmith ya bayyana akwai matakai takwas da dole ne ka yi amfani da su. Na farko daga cikin masu yawa a cikinsu su ne:

''Ka yi tambaya. Ka tambayi mutane 'ta yaya zan bunkasa kaina (shugaba ko abokin hadin gwiwa ko abokin aiki da sauransu)?','' kamar yadda ya rubuta.

''Ka saurara. Ka saurari amsarsu.

''Ka yi tunani. Ka yi tunani tare da duba gudummawarsu? Me take nufi?''

Ka gode wa mutane a bisa gudummawar da suka ba ka kuma ka karbi gudummawar hannu bibbiyu idan suka ba ka. Da zarar ka yi haka, ya rubuta, dole ne ka yi:

''Da shigo da wasu. Ka sa mutane su tallafa wa kokarnka na kawo sauyi.

''Ka rika bibiya. Ka rika bibiyar al'amaru a kai a kai wanda ta hakan masu ruwa da tsaki za su ga kyawawan matakan da kake dauka daga shawarwarin da suke ba ka.''

Za a ga abin mai sauki ne, in ji Goldsmith, haka kuma abu ne mai sauki a yi amfani da shi, abin da ya sa hakan ya sa ya zama abu mai sauki ka sauya domin ka inganta.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is there a checklist for success?