Ka taba fuskantar wariya a neman aiki?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Iyalai kuma ma'aikatan kamfanonin Rupert Murdoch

Yadda alaka ko 'yan uwantaka ke taka rawa a wurin daukar mutum aiki abu ne da kusan yake a ko ina, sai dai inda lamarin bai bayyana a fili ba.

Matt Chittock ya bincika yadda abin yake

A duk inda kake aiki a duniya, nuna bambanci na fifita abokai ko 'yan uwa a kan wasu kila na daga al'adar aikin wannan wuri walau a fili ko boye.

Ka tambayi Ana Patricia Botin wadda ta gaji babanta a shugabancin babban bankin kasuwanci na Spaniya Santander.

Ko Rupert Murdoch wanda ya dora 'ya'yansa a shugabancin kamfanonin yada labarai na News Corp da 21st Century Fox.

Ko kuma dai ka tambayi duk mutum daya daga cikin biyar a 'yan majalisar dokokin Burtaniya da suke daukar wani nasu a mastsayin ma'aikatan ofishinsu.

Duk da cewa wannan ta'ada ta fifita 'yan uwa wurin daukar aiki aba ce da ta zama ruwan dare a kasashen duniya, wasu sun bambanta yadda suke daukar lamarin.

Misali a Amurka, dokokin tarayya sun hana ma'aikatan gwamnati daukar wani daga cikin iyalansu aiki, amma kuma ba a haramta hakan ba a aikin da ba na gwamnati ba.

Kuma a Burtaniya da Amurka duk mai kamfanin da ya kara wa abokansa ko danginsa girma sama da sauran ma'aikata zai iya fuskantar kara mai tsanani ta tuhumar nuna bambanci.

KARIN BAYANI: Labarai shida na nuna bambanci

A China hukumar yaki da cin hanci da rashawa tana daukar tsattsauran mataki a kan rashawa da nuna san kai ga dangi a daukar aiki, inda take sa ido sosai a kan manya da ta ce suna tafiyar da manyan harkokin kasuwanci.

Amma kuma a kasashe irin su Italiya da Spaniya a dauke ka aiki ko a ciyar da kai gaba a wurin aiki sabda dangantaka maimakon kwarewarka ba abu ne da hukuma ta damu da shi ba. Ana ma daukar hakan a matsayin wani abu da aka saba.

Valerie Berset-Price haifaffiyar Switzerland, wadda ta kirkiro kamfanin harkokin ma'aikata na Professional Passport, wanda yake taimaka wa kamfanoni kan matsalar bambancin al'ada, ta ce a inda ta girma, ''idan zaka iya bayar da shawarar daukar wani aboki ko dan uwa aiki ko kuma dauko hayarsa sai ka yi hakan. Wata dama ce ta sama musu mafaka.''

Amma kuma a lokacin da ta koma Amurka ta yi karatu a kan harkokin kasuwanci, ta yi mamaki yadda manhajar karatun ta ke jaddada illar nuna fifiko ga 'yan uwa a wurin daukar aiki har ma a wasu hukumomin ake daukar abin a matsayin babban laifi.

Kafin wannan lokacin ban taba sanin ma abin da kalmar nuna fifiko take nufi ba,'' ta ce.

A lokacin da ta fara harkokinta ita ma sai ta yi mamaki cewa abokai, wadanda suke manyan mukamai, misali a fitattun manyan kamfanoni ba sa son bayar da shawara a ba wa kamfaninta aiki.

''Wannan ba wai domin ba sa son na cigaba ba ne, ko ba sa so na ko kuma sun yarda da abin da nake'' in ji Berset-Price. ''Sun yi hakan ne saboda ka'idar kamfaninsu ta ce ban cancanci duk wani aiki ba a wurin saboda ni kawarsu ce ko kuma ina da dangantaka da su.''

Bambancin yadda ake kallon wannan lamari ya dogara ne ga al'adar wuri.

A kasashen da ake daukar dangantaka tsakanin iyalai da muhimmanci, ana ganin wannan nuna bambanci ko fifiko ga 'yan uwa a matsayin wani abu da yake tamkar al'ada wanda ya dace ta yadda 'yan uwa za su taimaka wa juna.

''A Spaniya da wuya a ce an yi wata gogayya a fili ta daukar aiki tsakanin jama'a,'' kamar yadda Joe Haslma, babban darekta kuma mai makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta IE Business School da ke Madrid wanda ke zaune da kuma aiki a birnin Milan na Italiya.

''Kuma ba a daukar cewa kashi dari bisa dari aiki naka ne, abu ne kamar dai a ce kana rike wa wani dan uwa ne kawai.

A nan idan wani dan uwa ko dangi ba shi da aiki ana kallon haka a matsayin wata matsala ta iyalin baki daya.

Saboda haka akwai lokaci da dama da ake bai wa mutumin da bai kai a ba shi aiki ba amma sai a dauke shi saboda yana da dangantaka da wani ko kai tsaye ko kuma ta wata hanya.''

Wannan tsari yana da amfaninsa. Kamar yadda Haslam ya bayyana, dantakar 'yan uwa tana kara tabbatar da biyayya, saboda haka masu kamfani ba za su damu cewa gasa za ta sakaya wadanda suke kwararru ba.

Haka kuma abu ne mai sauki ka dauko wani daga inda aka riga aka sani maimakon ka bi matakan daukar ma'aikata da aka saba bi.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Duk da haka wannan al'ada ta nuna bambanci za ta iya haifar da matsala ga tattalin arziki gaba daya.

Da farko dai za ta iya korar masu zuba jari na waje, kamar yadda wasu alkaluma na rahoto kan yaki da rashawa na kungiyar kasashen Turai EU na 2014 ya nuna, kashi 67 cikin dari na masu zuba jari na kallon dabi'ar nuna fifikon a matsayin 'babbar matsala' idan kana tafiyar da kamfani a Girka.

Wata babbar matsala kuma ita ce rashawar da ke tafiya tare da dabi'ar nuna bambancin ka iya jawo asarar rayuka.

Kamar yadda bayanai suka nuna yawan mutuwar yara a kasashen da rashawa ta yi katutu ya kai kusan kashi daya bisa uku fiye da yadda ake samu a kasashen da ba su da rashawa sosai.

''A Italiya lallai kana bukatar sanin wani kafin ka samu aiki,' in ji wani mai kamfanin saye da sayar da gidaje a Italiya Gabriel Fabrizio Sbalbi.

''Wannan ya fi faruwa ma a kan matasan da suka gama jami'a wadanda ba su san kowa ba. Kuma wannan na nufin matasa masu ilimi sosai (kusan 60,000 a shekara) suna barin kasar domin neman aiki a wata kasar.''

Sbalbi yana ganin yawan rashin aikin yi shi ne ke haddasa wannan hijira ta matasa, domin rashin aiki tsakanin matasa ya kai kashi 44.2 cikin dari a watan Yuni na 2015. Amma kuma dabi'ar la'akari da dangantaka wurin daukar aiki ita ma na taka rawa.

Wani bincike na 2013 daga ma'aikatar kwadago ta Italiya ya nuna cewa kashi 61 cikin dari na kamfanoni sun dogara ne ga turo musu mutum daga wani dan uwa wurin daukar mutane aiki.

Kuma Sbalbi ya ce a bangaren ayyukan gwamnati kuwa wasu ayyukan an dauke su kamar gado tsakanin dangi ko iyalai.

A dau misalin labarin abin da ya yi kaurin suna wanda aka gano cewa a Jami'ar Palermo sama da rabin malamanta suna da akalla wani dan uwa da yake aiki a makarantar.

Ko da yake daukar wani dan uwa ko dangi wanda yake da cancanta ba wani abu ba ne, amma idan babbar cancantarsa ita ce sunansa na biyu(wato 'yan uwantaka) ba shakka hakan ya toshe wa wadanda suka fi shi cancanta damar samun aikin, kamar yadda Jane Sunley wata mai kamfanin daukar ma'aikata aiki a Landan Purple Cubed ta bayyana.

Wannan na iya zama babbar matsala ga tsarin kamfani saboda za ka rasa mutanen da za su kawo sabbin dabaru da fasaha kamfanin.

Haka kuma a kasuwar duniya inda kake mu'amulla da mutane daban-daban, wannan zai yi wuya idan aka ce dukkanin ma'aikatanka sun zo daga bangare daya ne.''

Ba za ka iya jure wa dabi'ar nuna fifiko ga 'yan uwa ba a inda kake? Za ka iya bin sahun mutanen da suke kaura zuwa wasu kasashen su nemi aiki inda ba a damu da alakarka da wani babba ba a wurin aiki.

Wannan shi ne abin da Sbalbi ya yi a lokacin matsalar karayar tattalin arziki ta duniya, inda ya bar Italiya ya koma Mexico ya kafa kamfaninsa na dillancin gidaje.

''Ba wanda ya sanni ko kamfanin, amma kuma duk da haka mutane na zuwa wurinmu su nemi gida saboda sun ga kyawun irin abin da za mu iya,' ya ce.

''Idan har ana son haka ta faru a Italiya sai mun sauya tsarinmu gaba daya.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Where 'a job is never regarded as 100% yours'