Mutane sama da miliyan 2.3 na neman aikin 368

Hakkin mallakar hoto alamy

Kana jin wani kalubale ne ka nemi aikin da kake burin yi da mutane sama da 12? To ina kuma ace mutanen da kake neman aikin da su sun kai miliyan biyu da dubu 300.

Gwamnatin jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya ce ta sanar da gurbin aikin da ta samu takardun masu sha'awar shiga aikin a watan Satumba, kamar yadda jaridar Financial Times ta ruwaito.

Sanarwar daukar aikin ta kananan ayyuka ce wadda aka sanya a intanet mai gurbin mutane 368 da za su yi aikin gadi da kai shayi ga baki.

Albashin watan farko na aikin dala 240 kwatankwacin kudin Indiyan rupee 15,600, ne wanda ya zarta kiyasin bankin duniya na mafi karancin abin da ma'aikaci ke samu a Indiyan na dala 135.

Ba mu yi tsammanin lamarin zai kai haka ba

Sanarwar daukar aikin wadda aka sanya a intanet ta nemi mutanen da suke daga shekara 18 zuwa 40 wadanda suka yi makaranta akalla tsawon shekara biyar kuma suka iya tuka keke ne.

Sama da mutane 250 daga cikin wadanda suka aika da takardunsu na neman aikin suna da takardar shedar digirin digirgir ne (dakta ko phd), 25,000 kuma suna da digiri na biyu (masters), kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ko da yake yawan rashin aikin yi a Indiya yana kasa da kashi biyar ne cikin dari, amma duk da haka sabbin guraban aiki kadan ne, saboda yawan al'ummar kasar ta Indiya da kuma tsauraran dokokin kwadago, kamar yaddalabarin ya nuna.

A kasar ta Indiya aikin gwamnati ya fi na kamfanoni da masu zaman kansu daraja, saboda na gwamnati ya fi albashi da kuma dorewa, inji gwamnan babban bankin kasar, Raghuram Rajan wanda ya sheda wa jaridar ta Finan cila Times.

Sakataren gwamnatin jihar da za ta dauki ma'aikatan Prabhat Mittal ya sheda wa jaridar cewa, '' ba mu yi tsammanin samun yawan mutane haka ba.

A 2006 a gurbin aiki kusan 260 mun samu takardun nema 100,000. Amma a shekara tara yawan ya karu.''

Ba shakka ba lalle ba ne ka samu kanka a gasar neman aiki da mutane miliyan biyu, amma ka yi fice a fagen neman aiki tsakanin mutane a sassa daban-daban na duniya abu ne mai wuya.

Sai dai akwai hanyoyi da dama da za ka tsara takardarka ta neman aikin ta yadda za ta zama daban.

Da farko ya kamata ka nemi aikin da ka san ya dace da kwarewarka. Ka yi kokarin tsara takardar jerin bayanin rayuwarka (cv), yadda zai zama kamar takaitaccen labarin rayuwarka maimakon jerin bayananka kawai.

Duk irin wannan takarda taka ka tabbatar ka tsara ta yadda za ta dace da irin kamfani da aikin da kake nema, ta yadda za ta nuna cewa kai mai ilimi ne kuma kana da sha'awar aikin da gaske.

Wani dan rawa William Sjogren, wani salo na daban ya dauka a lokacin da ya aika da takardarsa ta neman wani aiki, inda ya dauki hoton bidiyo na shi da budurwarsa suna rawa da takardun da ke dauke da bayanan kansu manne a bayansu.

Duk da cewa ba lalle hakan ya birge wasu masu daukar aiki ba, amma dai ya yi fice kuma ya zama daban tare da nuna basirarsu.

Idan ka tsara takardarka (cv) sai ka yi kokarin samo wata dabara kuma da za ta sa ka samu gayyatar tantancewa daukar aikin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why 2.3 million people wanted this job