Ko tausar kyanwa na maganin gajiya?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kana fama da gajiya? Ka yi aiki ka gaji? Kana fama da kadaici? Watakila kana bukatar ka dan yi nishadi da wasa ne da kyanwa, domin maganin gajiyar wurin aiki da debe kewa.

Manyan shagunan kyanwowi, wani sabon salo ne na samar da nishadi da hutu ga mutanen da ke fama da wata damuwa ko kadaici ko gajiya ta dawainiyar aiki.

Kuma wannan salo yanzu ya fara tashe a wasu manyan birane na duniya.

Tsari ne mai sauki. Za ka je irin wadan nan shaguna ne ka biya domin ka zauna tsawon sa'a daya ko fiye da haka, cikin yanayi mai dadi tare da kyanwowi iri daban-daban, kana shan ruwan lemon da ka fi so kuma kana dan wasa da shafa kyanwowin nan.

Hakkin mallakar hoto Getty

Courtney Hatt, wata mai sha'awar dabbobi wadda kuma tsohuwar ma'aikaciyar wani kamfanin fasaha ce a San Francisco, ita ta bude shagon hutawa da kyanwowi na farko a birnin a watan Yuni.

Shagon nata mai suna KitTea yana da wani daki mai kyanwowi iri daban-daban inda mutum zai biya tsawon sa'a daya ko sama da haka ya rika dan kewayawa daga nan zuwa can da kywanwown da yake sha'awa kuma yana wasa da su.

Kuma duk magen da mutum yake so ya dauke ta a matsayin riko za a iya ba shi. Ana kuma sayar da shayi na musamman irin na mutanen Japan a wani sashe na wurin.

Hakkin mallakar hoto peter bowes
Image caption Wata kyanwa a shagon kyanwowi na San Francisco, KitTea

''Idan ka shiga shaguna na shakatawa da sauran bukatun jama'a na kuma ka zo irin wannan wurin da ke cike da kyanwowi za ka ji babban bambanci ta yadda kake mu'amulla da mutane da kuma walwala,'' inji Hatt.

Ta ce, ''mutane suna samun sabbin abokanai a nan, abin sha'awa ne idan ka ga yadda ake yi a nan.''

Hatt tana ganin wannan wata hanya ce ta samun hutu daga irin rayuwar da ta yi fama da ita ta aiki a kananan kamfanonin fasaha.

''Abu ne da zai kwantar maka da hankali ka samu natsuwa cikin sauki,'' ta ce.

Wannan irin hanya ta maganin gajiya ta hanyar wasa ko hutawa da dabbobi, ta samo asali ne daga Japan, inda aka fara bude manyan shagunan sana'ar shekaru 20 da suka wuce.

Sai dai ba kamar wannan babban shago na KitTea da ire-irensa masu kyanwowin ba a sauran biranen Amurka, su na Japan ana yinsu ne domin amfanin mutanen da ba a yarda su ajiye dabbobi a 'yan kananan gidajen da suke ba.

Wadan nan manyan shagunan hutawa da kyanwowi a kan iya samun irinsu a Landan da Melbourne da New York da Paris da kuma wasu biranen na duniya.

Bayan nasarar da ta yi ta kaddamar da asusun bude wurin, Hatt ta ce masu zuba jari da suka zarta yadda ake bukata, sun nuna sha'awarsu ta sa jari.

Duk da cewa farko-farkon bude shagon kenan amma wadanda suka kafa shi sun ce suna samun ciniki.

A lokacin ganiyar hada-hada har wasu ne ke jira, kafina a zo kansu.

Hakkin mallakar hoto dan edblom
Image caption Wata mage a shagon kyanwowi na San Francisco, KitTea

Wurin yana da ka'idar cewa ba za ka damu kyanwar da take barci ba, kuma akwai ma'aikata da ke kula da jin dadin magunan.

Wannan kasuwancin ba lalle ya dace da kowa ba, musamman wadanda ba su da ilimi sosai a kan dabi'ar dabbobi ba.

''Ba abu ne mai sauki kamar yadda mutane ke dauka ba,'' inji Jacqueline Munera, wata kwararriyar masaniya kan halayyar dabbobi a Tampa da ke Florida.

''A Japan, yawancin shagunan kywanwar kusan suna da yawan kyanwowi ne daidai yadda ya kamata.

Amma a nan Amurka inda manufar abin ita ce a samu mutanen da za su rika karbar kyanwowin domin riko kamar nasu, za a rika samun yanayin yau wannan kyanwar ta tafi gobe kuma an kawo wata.''

Munera ta ce sabo da kyanwowin da ake sauya wa wuri ko kai su wani wuri abu ne da zai iya haifar da matsala babba, domin ba lalle ba ne su rika yarda da mutum.'

Kyanwowin da suka girma za su iya samun matsala ta sabo da sauran kyanwowi da kuma mutane.

Wannan abu ne da Munera ta ce ya kamata a sanya ido a kansa sosai domin kare dabbobin daga shiga yanayi na damuwa.

Ko wannan kasuwancin zai dace da kai? Kana iya latsa kibiyar da ke saman labarin na Ingilishi domin ganin hoton bidiyo don kara koyon yadda ake bude babban shago irin wannan na kyanwowi.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan Is a cafe full of cats the cure for stressed-out workers?