Kada ka furta wannan a wurin aiki

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Dukkaninmu ta taba faruwa da mu: kai ne ka furta wata magana da karfi a wurin aikinku kuma nan da nan sai ka yi nadamar fadarta.

Ga manyan shugabannin kamfanoni, katobara na iya bata sunan kamfanin, wanda hakan kuma zai iya sa darajar hannun jarin kamfanin ta fadi.

A kan kowa ma, fadin abin da bai dace ba ga abokan aiki, ko sakin baki sakaka ka rika bayanai da maganganu masu yawa abu ne da zai iya kunyata ka, ko ya jefa tsoro a ofishin.

Wannan batu ne da masana a shafin nan na zumunta da muhawara tsakanin ma'aikata a intanet Linkedln, suka duba a baya-bayan nan, inda suka tabo abubuwan da shugabannin wuraren aiki bai kamata su ambata ba, da maganganu na sirrin mutum da bai kamata ka fada wa kowa a ofishinku ba, da kuma wasu kalmomin kasuwanci na salo da ya kamata mutum ya kauce wa.

Ga abin da wasu daga cikinsu suka bayyana:

David Kerpen, babban jami'in kamfanin Likeable Local

Kerpen ya tuna da wani lokaci da bai ji dadi ba, bayan da ta waya ya gaya wa wani ma'aikaci cewa ya kamata ya zama mai faran-faran da jama'a.

''Furta wannan kalma ba wani abu ba ne, matsalar kawai ita ce yadda na gaya masa ne, a gaban sauran abokan aiki,'' kamar yadda ya rubuta a jerin abubuwa 17 da shugaba a wurin aiki bai kamata ya fada ba.

''Dole ne shugabanni su san cewa dukkanin ma'aikata suna koyi da su ne. Duk abin da shugaba ya ce, za a yayata shi, saboda shugaba ne ya fade shi,'' kamar yadda Kerpen ya rubuta.

Kerpen ya bukaci shuwagabanni da sauran manyan jami'ai ko jagorori su ba shi jerin abubuwan da bai kamata shugabannin wurin aiki su fada ba. Ga wasu daga cikinsu:

'' Ni ne shugaba. Ba wanda zai so ya yi aiki da kamfani ko hukumar da ba ta yabawa da kokarin ma'aikaci ko mutunta shi. Idan abokan aikinka na son aikin da za a rika yi musu gadara da ba da umarni, to da sun shiga aikin soji.

In dai kai ba soja ba ne to bai kamata ka rika yi wa ma'aikata magana da iko da gadara ba.''

''Me yake damunka? Abu ne mai sauki ranka ya baci idan wani ma'aikacinka ya yi wani abu ba daidai ba, amma wannan tambaya, kai tsaye tana sa ya dauka a zuciyarsa kana da shakku a kan kwarewa ko cancantarsa da aikin.

Tambayar ba kawai tana nuna cewa yana da rashin kwarewa ko wata babbar matsala ba a wurinka, tana nuna ba ka da sauran yarda a kan cancantarsa. Daga nan ka karya masa lago, sai aikinsa ya rika komawa baya.''

''Wannan karamin ciniki ne ko kwastoma ne (mai mu'amulla da mu). Babban kuskure ne ka koya wa ma'aikatanta yadda za su rika ba da fifiko ga wani mai sayen kayanku ko harka da kamfaninku a kan wadanda ba su kai shi ciniki ko matsayi ba.

Wannan zai sa kamfaninka ya rika mu'amulla maras kyau da wasu masu sayen kayanku ko mu'amulla da ku.

Sannan kuma za a rika musu tsakanin ma'aikatanka a kan wanda zai kula da wannan cinikin da wancan (wasu za su so su rika kula da na manyan mutane).''

''Aikinka na kyau. Idan ma'aikaci ya nemi jin bayani ko yadda kake ganin aikinsa ke gudana, kada ka taba gaya masa cewa, aikinsa na kyau.

Idan mutum ya yi maka wannan tambaya yana son sanin inda zai kara bunkasa aikinsa ne.

Saboda haka kai tsaye ka yaba wa ma'aikaci da irin wannan kalma, ba tare da ka nuna masa inda zai inganta aikinsa ba, asara ce ta wata dama.''

Ga wasu daga cikin abubuwan da Bernard Marr, Shugaban cibiyar nazarin harkokin ma'aikata ta Advanced Performance Institute, shi kuma ya gabatar.

Bayyana wa abokan aikinka abubuwan da ba su dace ba, zai iya yi maka illa, kamar ka yi kirari ka soka wa kanka wuka ne, tare da mayar da sana'arka saniyar ware, kamar yadda Marr ya rubuta.

''Duk da cewa abu ne mai kyau ka rika barkwanci da hira da abokan aiki, amma kuma yana da kyau ka san iyakar da za ka tsaya,'' kamar yadda ya rubuta a kasidarsa mai suna Gargadi! Abubuwan da bai kamata ka gaya wa kowa a wurin aiki ba (Warning! The Things You Must Not Tell Anyone At Work).

''Ba ina ba ka shawarar cewa ka zama kamar butum-butumi ba ne, wanda ba ya bayyana wa kowa wani abu na rayuwarsa a wurin aiki ba,'' ya rubuta. Amma ka yi hankali, kamar yadda ya ba da shawara.

Marr ya gabatar da abubuwa goma da mutum bai kamata ya gaya wa kowa ba a wurin aikinsa. Ga wasu daga cikinsu.

'' Kada ka taba yin magana a kan kudi a wurin aiki, bayani ne a game da albashinka, ko kan abin da ka kashe ne a kan aikin gidanka ko mota ko wata sabuwar na'ura ka saya.

Magana a kan kudi na iya haddasa kyashi ko bakin ciki ko wani ko wasu su tsane ka a wurin aikin,'' ya rubuta.

Soyayya : Abin da ya shafi mu'amullarka ta soyayya ko aure, ba abu ne da za ka kawo shi ofis ba. ''Zai iya kasancewa kana da soyayyar da kake matukar jin dadi ko kuma ba ka jin dadin aure ko soyayyarka da wata, to kada ka sake ka tattauna wannan magana da wani a wurin aikinka,'' Marr ya ce.

Addini: Wani karin abin kuma da za ka kaurace wa magana akai a ofis shi ne addini. ''Abun alfahari ne mutane suna da addinan da suke bi, amma ka tuna cewa yawancin yake-yake bambancin addini ne ke jawo su,'' kamar yadda Marr ya rubuta.

Sai kuma Richard A Moran shugaban kanfanin Accretive Solutions.

Harkokin kasuwanci na duniya cike suke da kalmomi na salo ''wadanda kusan sun zama jiki a wurinmu har idanuwanmu kan kafe wurin kallonsu,'' Moran ya rubuta a jerin kalmomi uku da aka fi jin tsoro a harkar kasuwanci. Amma wadannan ba kalmomi ba ne da ya kamata mu damu da su, kamar yadda ya rubuta.

''Wasu kalmomi sukan dauki hankalinmu kamar yadda alamar jar wutar lantarki da ke harbawa.

Kalmomin sun zama kamar ba su da wata illa har ake amfani da su akai-akai, amma kuma sukan sa mu dakatar da duk abin da muke yi idan an ambace su,'' Kamar yadda Moran ya rubuta.

Daga cikin kalmomi ukun da aka fi tsoro? Abin takaici (unfortunately).

'' Wannan kalma ce da ke jan hankali matuka, da kusan a ce ita ce kalma daya da za mu ji ko mu gani a cikin sako mu san cewa akwai wani abu maras dadi da zai biyo baya ko ya faru.

Ga mutumin da yake fafutukar neman aiki, tana nufin, an yi watsi da shi komai kyawun takardunsa, ko mutane nawa ne suka nemi aikin tare da shi, '' kamar yadda Moran ya ce.

Haka kuma wannan kalma tana da wata ma'anar maras dadi. '' Idan aka sanya ta a wasikar email ta ma'aikata, tana nufin ana shirin sallamar ma'aikata ko kuma wani sauyi maras dadi zai kasance.

Ko kuma tana nufin na'urar shayi ko gahawa ta ma'aikata ta lalace, ko matar da ke yi wa ma'aikata tausa idan suna da wata larura ta jiki ta kamfanin ba ta da lafiya.

Kalma ce dai, wadda a ko da yaushe take nufin wani labari maras dadi na gab da zuwa,'' kamar yadda ya rubuta.

''Abin takaici, ita wannan kalma ta abin takaici ana yawan amfani da ita.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Don't say this at work