Shin akwai abokantaka a kasuwanci?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Tambaya: Wani abokinka ne ya bude sabon kanti, kuma ya nemi da ka rinka sayen kaya a wurinsa.Kana son ka taimaka masa harkar ta bunkasa, ta hanyar zama daya daga cikin masu sayayya a kantin, to amma sai ka ga kayan da tsada.

Haka kuma kana ganin tsarin da ya dauka na kasuwanci bai dace ba, domin ba ka ganin zai dore.

To a nan za ka yi masa alkunya ne saboda shi abokinka ne ka rika sayen kayan da tsada, wadanda watakila ma ba ka bukatarsu?

Za ka iya ba shi shawara (wadda bai nema ba) ne, kan yadda zai inganta harkar tasa, ba tare da sayen kayan nasa ba?

Amsa: Fara wata harkar kasuwanci abu ne mai wuyar gaske wanda kuma yawanci yake bukatar mutum ya ajiye girman kai, ya nemi taimako.

Abu ne da aka sani cewa idan mutum ya fara kasuwanci, zai tunkari mutanen da ke da kusanci da shi, ya yi musu talla, domin su rika sayen kayan nasa.

Wannan zai iya haifar da wani yanayi na rashin jin dadi ko takura, idan ba sa son sayen kayan, kuma suna dari-darin gaya masa dalili.

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Kayan kantin kawarki suna da tsada sosai. Za ki iya gaya mata gaskiya?

'' Ba na jin abu ne da ya zama dole a abokantaka ka rika ba wa abokin naka kudi domin tafiyar da harkar kasuwancinsa wadda ba za ta mike ba, kuma ma idan tafiya ta yi tafiya za ta durkushe.

Amma ina ganin nauyi ne da ya rataya a wuyanka a matsayin aboki na gari, ka taimaka wa na kusa da kai,'' in ji Barak Richman, farfesa a harkokin kasuwanci da aikin lauya a jami'ar Duke.

Farfesan ya ce, muhimman abubuwan da dan kasuwa yake da su, su ne kashin bayan nasarar kasuwancinsa.

Abubuwan kuwa sun hada cewa mutum ya zaman yana da tarin abokai na aiki da wadanda ba na aiki ba.

Duk wata sabuwar harkar kasuwanci na bukatar abubuwan da suka jibanci kudi, kamar jari da bayanai da kuma kwarewa da mu'amullar shi mai harkar.

Wannan kwarewa ta shafi, dabara da tunanin yadda za a yi abu da hanyar samun bayanai daga masu sayen kayan da sauransu da kwarin gwiwa ko karfin halin tafiyar da harkar, in ji Richman.

Ba karamin taimako za ka yi wa abokin naka ba idan a tsanake ta siyasa ka masa bayanin abin da ya sa ba za ka iya zama mai sayen kayan nasa ba (ko kwastomansa ba), maimakon kawai ka kaucewa tambayar, idan ya ce maka me ya sa ba ka sayen kayansa?

Ko bayan dalilin maganar abokantaka da zamantakewa, ka ba wa mutum bayani na gaskiya kan yadda kake ji da kayan da yake sayarwa ko farashinsu ko kuma aikin da yake yi da kudin da ake biyansa na samar da aikin abu ne mai matukar muhimmanci ga duk wani dan kasuwa.

Idan farashin da yake sayar da kayan ko yake caza idan aiki ne, ya yi tsada da yawa, wanda hakan barazana ce ga kasuwancin nasa, zai fi kyau abokin naka ya sani da wuri maimakon sai abu ya yi nisa.

Ka dauki wannan a matsayin wani muhimmin mataki da wadanda suka fara wata sabuwar harkar kasuwanci suke amfani da shi wajen gyara kayansu da kuma daidaita farashinsu.

Saboda haka wannan dama ce a wurinka ta ka taka wannan rawa a harkar kasuwancin abokinka.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Samun sakamako abu ne mai muhimmanci ga 'yan kasuwa

''Yawancin harkokin kasuwanci suna daidaituwa da inganta ne a hankali a hankali, bayan wani lokaci.

''Kuma da yawa suna shawo kan kalubale na farkon kafa kasuwancin tare da taimakon sauran jama'a,'' Richman ya ce.

Idan abokinka ba zai iya tuntubarka ba da sauran mutane domin gaya mishi gaskiya ko ba shi shawara da ta dace, zai gamu da gagarumar matsala a duniya.

Ka fito fili keke da keke ka gaya masa cewa, za ka so a ce kana siyayya a wurinsa amma kayansa sun yi tsada.

Daga nan kuma sai ka bayyana masa korafinka a kan tsarin kasuwancin nasa.

Ko ya dauki shawararka ko bai dauka ba, ka ci gaba da mu'amulla da shi kamar yadda kuke yi a da, in dai har baibata ransa ba.

Idan kuma ya dauki wannan shawara da ka ba shi a matsayin cin mutunci, to lalle harkar kasuwanci ba ta dace da shi ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Navigating the awkward line between friend and customer