Yadda China ta kashe dala biliyan daya a minti takwas

Yadda China ta kashe dala biliyan daya a minti takwas

Babban kamfanin sayar da kaya ta intanet Alibaba ya kafa saban tarihi na yawan ciniki a ranar da ake wa lakabi da ranar wadanda ba su da aure, wadda rana ce ta hutu ta masu sayayya a China, 11 ga watan Nuwamba.

Ga wasu daga cikin alkaluman da aka tattara na tarin siyayyar da ta wakana a wannan rana da aka fi sayayyar kaya ta intanet a duniya ta wannan shekara a kasar ta Sin.

A wurin Turawan yammacin duniya, shafin sayayyar intanet din na Chanan ko kusa bai kai wadanda kusan ake da su a ko ina ba na Amazon ko eBay, amma a Sin din Alibaba ya danne takwarorinsa na Amurkan idan ana maganar yawan ciniki na rana daya.

Wannan rana ta sayayya ta intanet wadda ake kira ''Singles Day'' da Ingilishi a Chana, wadda take daidai da ranar Cyber Monday a Amurka, ta yi gagarumin suna sosai tun 2009.

Ranar da ake bikinta duk ran 11 ga watan Nuwamba a kowace shekara, ta samo asalin sunanta ne daga alamar mutane hudu da ba su da aure, wadda ake wa lakabi da ''Bare Sticks'', wadda ake alamantawa da lamba daya har guda hudu (1111), na wannan rana.

A shekarar da ta wuce ta 2014 masu sayayya sun kashe dala biliyan tara da miliyan 300 a wannan rana.

A wannan shekarar kuwa cinikin ya zarta na bara da dala biliyan biyar. Ci gaba da karanta wasu daga cikin alkaluma masu daukar hankali na alamar sha'awar da al'ummar Chana suke yi ta siyayya ta intanet.

Hakkin mallakar hoto Kieran Nash
Image caption A minti takwas masu sayayya ta intanet suka yi wa Alibaba cinikin dala biliyan takwas a China
Hakkin mallakar hoto Kieran Nash
Image caption Jumullar cinikin dala biliyan 14 da miliyan 300,000 aka yi wa Alibaba a rana daya a China
Hakkin mallakar hoto Kieran Nash
Image caption Ciniki mafi yawa da aka yi a Amurka a rana daya ta intanet shi ne na dala bliyan biyu da miliyan dubu hudu, ranar sayayya ta intanet, daya ga watan Disamba na 2014
Hakkin mallakar hoto Kieran Nash
Image caption Cikin dakika 18 cinikin ya wuce na dala miliyan 15 da dubu dari bakwai da biyu
Hakkin mallakar hoto Kieran Nash
Image caption 11.11 ita ce ranar marassa aure, wato ranar sayayya ta Intanet a China wadda mai kantin Alibaba Jack Ma ya kirkiro
Hakkin mallakar hoto Kieran Nash
Image caption Miliyan 45 ne yawan mutanen da aka fi samu a lokaci guda yayin sayayyar ta intanet a China a wannan rana.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How China spent $1 billion in eight minutes