Yadda za ka koyi sammako da son Litinin

Hakkin mallakar hoto alamy

Idan aka ba mu damar zabi tsakanin kara barcin mintina goma ko kuma mu tashi da sassafe, yawancinmu, za mu zabi sake mikewa a gado ne, a ko da yaushe.

To amma ko sirrin samun nasarar aikin da kake yi a rayuwa za a iya cewa ya dogara ne ga tashi da wuri, da koyon kaunar safiyar Litinin( ranar da ake cewa ma'aikata na tsoro) ?

Mun bukaci amsa daga wasu masu karatu domin samun shawarwari kan yadda mutum zai iya zama mai tashi da sassafe.

Ardell Della Loggia, wadda ke harkar dillancin a Seattle da ke Amurka, ta rubuto cewa, dole ta zama mai tashi da sassafe da kuma shafe dare ba ta yi barci, saboda masu mu'amulla da ita a kan harkar gidaje suna bukatarta a ofis tsakanin karfe tara na safe zuwa biyar na yamma.

Ta ce, ''dabarar da nake yi ta tashi da sassafe da kuma rashin kwanciya da wuri, ita ce ta barcin rana, yawanci daga karfe biyu zuwa hudu.

Sannan na fi son yin ayyuka masu matsi na takurawa da safe, wadanda yawanci amsa tambayoyi ne ta imail (email)'' ta ce.

Idan kana son ka rika tashi da sassafe kana aiki kuma ka kasance maras kwanciya da wuri (da daddare), kuma aikinka yana da sarari kamar yadda nake, to ka jarraba barcin rana.

Wannan ita ce hanyar da mutane da yawa da ke tashi da sassafe kuma suke shafe tsawon dare ba su kwanta ba, suke cin moriyar biyun.

Dabarar tashi da sassafe ita ce ka tsara lokacin kwanciyarka da daddare da kyau, kamar yadda wani mai karatu Andy Ooi, wanda ya bayyana jerin 'yan kananan hanyoyi da dabarun da za ka yi amfani da su ka zama kwararren gwarzon barci.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ka koyi yadda za ka ji dadin duhu. ''Kashe wayar nan, da talabijin da kwamfuta da dukkanin wutar dakin minti 10 zuwa 30 kafin lokacin da ka saba kwanciya. Sai ka zauna a kan doguwar kujerarka ta daki,'' in ji Ooi.

Ka tabbatar ba wata fitala da ke kunne a dakin naka, ya yi duhu sosai. ''Ga saki labulen dakin mai sanya duhu, sannan kuma ka tabbatar ba alamar wani abu da ke haske a dakin.''

Ka haramta fasaha a dakinka (na kwana), abin da ke nufin ba maganar yin Facebook ko Whatsapp.

Ka kawar da duk wata damuwa daga zuciyarka, sannan ka zama mai cike da kwarin gwiwa da kyakkyawan fata kafin ka kwanta.

Ya ce, ''da nakan je in kwanta a gado ina tunanin cewa, 'kai! Wai barcin sa'a biyar kawai zan yi. Na gashi kuma na gaji sosai',''

''Maimakon ka rika korafi da tunanin damuwa, ka kasance cike da kyakkyawan fata a lokacin da za ka kwanta,'' in ji Ooi.

''Ka daina tunanin kalubalen da ke gabanka na gobe. Kawai ka yi tunanin yadda za ka murkushe duk abubuwan da za ka fuskanta washegarin.''

Wasu kuwa cewa suka yi hanyar da suke samun kyakkyawan barci, su tashi da safe garau, ita ce ta watsi da dabi'ar da ta zame musu jiki.

''Na yi watsi da shan gahawa na dan lokaci,''in ji Andreas Blixt

''Wani abin sha'awa da ke faruwa a duk lokacin da na yi haka, shi ne sai na rika tashi da sassafe.''

Ya ce idan yana shan gahawa, sai ya dage ya rika tashi da karfe goma na safe, amma idan ya dakata da sha sai ya rika tashi da karfe takwas na safiya ko ma kafin hakan, ''kuma in rika ji na wasai fiye da yadda idan na sha gahawa.''

Blixt ya ce, ''haka abin yake yi min a duk lokacin da na bar gahawa, ina ganin abin a jarraba ne.

Ba gahawa kawai nake bari ba a wannan lokacin, hatta shayi da kayayyakin shaye-shaye masu kara kuzari ma kaurace musu nake, ko da sukari idan bai zama dole ba, ba ruwana da shi.''

Sable de Oliveira ya n=bayar da shawarar shan wani abu mai yawa ne kafin kwanciya sannan ka ajiye wayarka can nesa da gadonka.

Ya ce, ''kasancewar kana cike da tunanin za ka iya tashi ka je ka dauki wayar ka kashe, tare da bukatar zuwa bandaki za su hana ka shantakewa ka yi ta sharar barci har ka makara.''

Tayar da kuzarinka

Da zarar ka farka daga barci sai ka yi mika, ka mommotsa jikinka, ta haka za ka wartsake da kyau.

Bruno Valle ya kawo wata dabara mai sauki guda daya, inda ya ce, idan kana son tashi da wuri, sai ka saita kararrawar wayarka zuwa daidai lokacin da kake son farkawa daga barcin, da zarar ta kada, sai ka bude idonka, ka dauki wayar, ka karanta wasikunka na imail (email).

Ya ce, ''wannan zai sa ka wartsake da kyau, domin za ka ga abubuwa da dama da za su sa ka wartsake, kamar sunan shugabanka na wurin aiki, da abubuwan da ake bukatar ka yi da matsaloli da wasiku masu bata rai,'' in ji Valle

Shi ma Spencer Pettus ya zabi tashi ne ''da zarar kararrawar wayarka ta kada.''

Ya ce wannan shi ne lokaci mafi muhimmanci na aikinka, ko ka kwanta da wuri ko ba ka kwanta da wuri ba.

Yana ganin hanyar da ta fi dacewa da yin hakan ita ce, da zarar ka farka, sai kawai ka yi mika da furta wata kalma: ko kuma kamar yadda shi yake yi 'Yeeeeeeeeeh!' Za ka wartsake sosai.

Amma kuma Pettus ya yi gargadin cewa kada ka yi hakan idan ba kai kadai kake gadon ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Can you become a morning person?