Kasuwar hijabi ta bude a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Fitacciyar mata ce a Malaysia wadda ta ke da miliyoyin masu sha'awar yadda ta ke gabatar da abubuwan da ta yi fice a kai.

A duk lokacin da ta bayyana a talabijin, nan da nan sai masu sha'awarta su ruka tururuwa zuwa kantina suna sayen duk abin da ta sa na ado, a wannan fita da ta yi a ranar, ciki har da hijabinta.

Noor Neelofa Mohd Noor wadda aka fi sani da Neelofa sarauniyar kyau ce Musulma 'yar shekara 26, tauraruwar fim kuma mai gabatar da shiri a talabijin wadda ke da mabiya miliyan daya da dubu 400 a shafin Twitter da kuma miliyan biyu da dubu 200 a Facebook.

'Yar kasuwa ce sannan kuma ita ce fuskar kamfanin tufafi da kayan ado na Naelofar Hijab na iyalan gidansu.

A cikin shekara daya kacal kamfanin ya zama daya daga cikin manyan fitattun kamfanoni yin hijabi da kallabi na Malaysia, kuma yana shirin fara fitar da kayansa zuwa kasuwannin kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto Muhammad Zameer
Image caption Fitacciyar 'yar Malaysia, Neelofa sanye da hijabin Naelofar

Malaysia inda kusan kashi 60 cikin dari na al'ummarta Musulmi ne, ba ita kadai ba ce kasar da ke samun wannan bunkasa ta kasuwar abin da ya zama cikammakin tufa ta kamala ta mata Musulmi.

An yi kiyasin a shekara ta 2014 cinikin da aka yi a kasuwancin na hijabi ya kai na dala biliyan 230 a fadin duniya, kuma an yi hasashen zai kai na dala biliyan 327 zuwa shekara ta 2020.

Bukatar hijabin na karuwa saboda a yanzu mata Musulmi na son rufe kansu.

A sauran kasashen da Musulmi su ke da rinjaye, mata da yawa su ma suna sanya hijabi domin bin umarnin Al'kur'ani na maza da mata su suturta jikinsu su zama masu mutunci da kamala.

Duk da cewa mayafi (hijabi ) alama ce ta addini, a yanzu ya kuma zama wani abu na ado.

Kuma bunkasar kasuwar wadanda a ke yayi ta bude babbar harkar kasuwanci wadda ke habaka.

Cinikin da aka yi a kamfanin na Naelofar, inda babu hijabin da ya wuce dala 24, ya kai na dala miliyan 11.8 a 2015, sama da linki biyu na abin da iyalin suka sa rai.

Kamfanin yana sayar da kayansa a babban kantinsa da kuma ta hannun diloli 700 a fadin kasar.

Suna sayarwa ta intanet sannan kuma suna kai wa ko 'ina a ke bukata a duniya.

Yadda su ke da diloli a Singapore da Brunei da Landan da Australiya da Holland da Amurka, burin kamfanin na Naeolfar, shi ne kayansa ya yi fice a duniya.

Hakkin mallakar hoto khoo min jee

''Abin ya bamu mamaki,'' in ji Noor Nabila mai shekara 30, yayar Neelofa, kuma wadda ke rike da mukamin manajar daraktar kamfanin NH Prima International, babban kamfanin da Naelofar ke karkashinsa.

Ta ce ''Abin ya wuce hankalinmu matuka yadda muka samu wannan karbuwa.''

Har ma wani suna aka sa wa mai sayen kayansu sosai, wadanda ke ado iri-iri da hijabin, hijabista.

Wannan habaka ta sha'awar hijabi yayi ne da zai kai ga sanya kaya irin na al'ada na Musulmi a tsakanin matan addinin ba iya Gabas ta tsakiya da Kudancin Asiya kadai ba.

An samu irin wannan sauyi a shekaru 30 da suka gabata ta yadda aka rika fassara addinin bisa koyarwarsa ta ainahi a kasashe da yawa.

Hakkin mallakar hoto Muhammad Zameer

Alia Khan ta majalisar kungiyar masu harkar tufafin ado na Musulmi, tana ganin ''zamani ne ya zo na komawa ga al'ada mai kyau.''

Majalisar tana da mutane kusan 5,000, kuma daya bisa uku daga cikinsu kwararru adon tufafi ne daga kasashe 40.

A fadin duniya, Khan ta ce, ''bukatar (tufafin ado da kamala) na da girma sosai.''

Turkiyya ita ce babbar kasuwar kayan tufafin Musulmi. Kasuwar Indonesiya ma na bunkasa sosai kuma kasar na son zama jagaba a wannan kasuwa a duniya.

Dian Pelangi wadda ta koyi sana'ar yin tufafin ado na Musulmi a Paris, wadda ta ke da mabiya miliyan biyu da rabi a shafin Instgaram, ita ce kan gaba a iya tufafin ado na kamala a Indonesiya.

Kuma a kwanan nan mujallar kayan ado (tufafi) da ke Biritaniya mai suna 'Business of Fashion', ta sa sunanta a jerin mutane 500 wadanda suka fi fice da kuma tasiri a harkar tufafin ado.

Tana da kantuna 14 a Indonesiya da kuma daya a Malaysiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dian Pelangi ita ce jagaba a zayyana kayan ado na mata na kamala a Indonesiya

Mata masu sanya hijabi su ma yanzu sun bayyana a kasashen Turai, inda Musulmi ba su da yawa.

A watan Satumba da ya wuce, mai tallata kayan zamani 'yar Biritaniya Mariah Idrissi, ta zama mace ta farko sanye da hijabi da ta fito a wata talla ta kamfanin H&M, kamfanin sayar da tufafi mafi girma na biyu a duniya.

A bikin makon tufafin ado na shekara ta 2015, 'yan matan nan uku 'yan uwa da suka fito da kayan nan da suka yi fice na Malaysia da a ke kira Mimpikita, sun gudanar da nuninsu na farko, inda a ke ganin sun fi jan hankali da hijaban da suka sanya fiye da sauran kayan da suka tallata.

Su ma masu zayyanar adon tufafi na Turai sun nuna sha'awarsu ta tufafin mata Musulmi, inda a 2014 kamfanin DKNY ya kaddamar da kasuwar sayayyar azumi.

Sauran kamfanonin tufafi na Turai irin su Tommy Hilfiger da Mango su ma sun bi sahu, inda suka sayar da tufafin Musulmi a lokacin azumin Ramadan.

Shi kuwa kamfanin Japan Uniqlo ya hada hannu ne da mai yin kayan ado 'yar Biritaniya, Hana Tajima, suka yi wasu kaya irin na Musulmi, wadanda suka hada da hijabi da kebaya (wasu irin kayan gargajiya).

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mariah Idrissi

''Kowa yana son ya yi ado na daban,'' abin da Zulfiye Tufa, mai yada labarai ta intanet, kuma mai yin tufafin ado 'yar Australiya, ta gaya wa 'yan kwamiti kan tufafin Musulmi, a wurin taron duniya na tattalin arziki na Musulmi da aka yi a watan Nuwamba na 2015.

Ta ce, ''ba lalle ba ne su nemi wani abu da ke cikin wadanda a ke yayi, amma dai suna son su bi zamani. Yana shafar yadda a ke kallonsu, musamman a akasashen Yammacin duniya.''

Hakkin mallakar hoto Getty

Wata 'yar Malaysia Vivy Yusof mai shekara 27, ta fara sanya hijabi shekara biyu da ta wuce, bayan da ta haihu.

Kasancewar ta rasa irin tsarin hijabin da ta ke so, sai ta yanke shawarar yin nata na kanta, inda ta mayar da hankali wajen amfani da yadi mai tsada da tsari na zamani, wanda zai dace da mata ma'aikata da matan da ba Musulmi ba ma.

Ta sanya wa kayan sunan kungiyar abokanta na babbar makaranta dUCk, kuma da kaddamar da kayan a watan Mayu na 2014.

Ta ce, '' abu ne mai wuya na samo wani (hijabi) irin na birni wanda ya karbu a duniya.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan matan malaysia 'yan uwa uku da suka kirkiro kayan kamfanin Mimpikita, a taron makon nunin tufafi na Landan na 2015

Yawancinsu duk sun yi yawa a kasuwa Ina son in kirkiri wani iri ne wanda ya dan dara saura, mai dan matsayi na masu hali, kuma in nuna cewa sanya hijabi zai iya zama abin alfahari.''

Tana sanya tallar sabbin kayan da ta yi a intanet nan da nan suka kare, kuma mata sukan yi layi suna sayensu a duk lokacin da a ke sayar da su a taron bajekoli a babban birnin Malaysian.

Duk da cewa Vivy ba ta son bayar da bayani a kan cinikinta, amma ta ce tuni kamfanin nata ya fara samun riba.

Shafukan sada zumunta na intanet suna da muhimmanci wajen tallata kayan kamfani, kuma ta hakan ne da zarar kamfanin ya yi sabbin kaya ko ya sake kawo wadanda suka kare, sai ya tallata wa mabiyansa na Instagram 110,000, yayin da ita kanta Vivy ta ke da mabiya 356,000.

Hakkin mallakar hoto Duck Scarves

A kantin sayar da hijabin Naelofar a Kuala Lumpur tarin mutane da suka hada da tsoffin mata da mazajensu da yara da matasan mata sanye da wandunan jins suna ta neman wanda ya yi musu.

Noor Nabila wadda ita kanta ba ta sanya hijabi, a yanzu tana kokarin bunkasa kasuwar hijabin kamfanin nasu ta wuce Malaysia da Singapore da Brunei, kuma ta kuduri aniyar ganin hijabin Naelofa ya zama na daya a duniya.

Ta ce, ''idan mutane suka ce sabuwar kasuwa ce, lalle kam sabuwar kasuwar ce.''

Ta kara da cewa, ''ba shakka shafukan sada zumunta na intanet sun sauya kasuwar gaba daya.

A zamanin nan mutanen da su ke sanya hijabi ba kawai wadanda suka fito daga hamada ko kauye ba ne.

Za su iya kasancewa fitattun mutane, ko wadanda suka zama wani abu, kuma su sanya hijabin ba tare da wata matsala ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Turanci latsa nan. How Muslim headscarves became a fashion empire