Ya za ka yi da kwararren ma'aikacinka mai shan miyagun kwayoyi?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Kuna filin jirgin sama a kan hanyarku ta zuwa wani babban taro a wata kasa, sai daya daga cikin manyan jami'an kamfaninka ya matso kusa da kai ya ce maka, 'yallabai ina da matsalar shan miyagun kwayoyi, kuma ina tsoron shiga da su kasar da zamu je kada a kama ni.

Daga nan sai muka amince ba zai yi wannan tafiya, zai zauna a gida, ni zan gabatar da bangaren kasidar da a da muka tsara zai gabatar a wurin taron da za mu je.

A matsayina na shugaban kamfanin, ban ji dadin cewa tsawon lokaci ina tare da wannan babban jami'i na kamfanina da ya ke da wannan hali.

To mene ne ya kamata na yi a irin wannan hali?

Me ya sa babban jami'i na kamfani ya sa kansa a wannan hali da kuma kamfaninsa?

Chana R Schoenberger ta yi nazari

Amsa: Ya yi kyau da ya fada maka cewa yana dauke da miyagun kwayoyi tun kafin ku hau jirgin. Idan da an kama shi da za a tuhume shi da safara miyagun kwayoyi.

Da hakan zai zama wata matsala ta shari'a da kuma bata sunan kamfanin kamfanin.

Ga ra'ayin wasu mutane a kan abin da ya kamata ka yi.

Da zarar ka dawo daga wannan tafiya ba wata-wata kawai ka gana da lauyoyin kamfaninka da kuma sashen kula da ma'aikata ka sheda musu, sannan ka kori wannan babban jami'i.

Wannan shawarar Thorn Jenness mai horar da manyan jami'ai kuma masani kan harkokin ma'aikata a Huntington, ta New York a Amurka.

Idan akwai wasu batutuwa ko ka'idoji da za ka bi tukuna, to sai ka tura wannan ma'aikaci hutu ba tare da biyansa albashi ba, kafin ka warware su.

Hanyar ka'ida ta warware wannan matsala za ta iya bambanta daga kasa zuwa kasa.

''A wasu jihohin kamar New York, ba ka bukatar wani kwakkwaran dalili kafin ka kori ma'aikaci, sai dai idan akwai wata yarjejeniya da aka kulla da shi tun farko, wadda bisa sharadinta ne za a kore shi,'' in ji Jenness.

Masanin ya kara da cewa, ''yana da kyau ka kare sirrin wannan jami'i, a bisa haka, saboda haka zan neme shi ne cikin sirri ya ajiye aikin kawai, ya kama gabansa ba tare da kowa ya san me ya faru ba, kuma ni ma ba zan bayyana lamarin ba.''

Jenness ya ce, ba wani yabo da za a yi wa wannan babban jami'i wai don ya ya yi karfin hali ya fadi matsalarsa kafin shiga jirgin.

Ya ce, ai mutumin ya ma dauka cewa ba za a yi masa komai ba saboda ya fito fili ya bayyana cewa yana da wannan matsala ta ta'ammali da miyagun kwayoyi , alama ce ta rashin kyakkyawan tunaninsa.

Ya ce mutum ne da karara ya ke da matsalar da ta yi tsanani kuma har ya kusa cutar da kamfanin.

Kamfaninka shi ne mafi muhimmanci, shi ya kamata ka bi amma, ba wani mutum ba.

Amma yakana da sanin ya kamata, wadanda na daga cikin muhimman ka'idojin aiki, na bukatar ka kiyaye da lafiyar mutum, da sirrinsa da kuma walwalarsa.

Wannan bukata ce karara ta neman taimako da ma'aikacin ya nuna, to amma kana da alhakin kare kanka, da ma'aikatanka da kamfaninka.

Yin abin da ya kamata wanda ya ke kuma daidai bisa ka'idar doka ba yana nufin tsabar rashin tausayi ba ne.

Matuka abin da za ka yi wa wannan jami'i shi ne ka, duba idan za ka iya taimaka masa magance wannan matsala ta shan miyagun kwayoyi, ko da ka kore shi.

Ba karamin karfin hali ya yi ba da ya iya fitowa fili ya gaya maka cewa, yana ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Idan kamfaninka yana da dokoki da ka'idojin aiki, zai iya kasancewa dokokin sun haramta irin wannan dabi'a, wannan zai ba ka damar korarsa daga aiki.

Idan ba ka da irin wadannan dokoki to kamata ya yi ka yi su yanzu, kuma ka tabbata sun kunshi hukunci a kan batutuwa kamar wannan na ta'ammali da miyagun kwayoyi, in ji Jenness.

Bayan wannan ka kuma yi kokarin shirya wani taron karawa juna sani na manyan jami'an kamfaninka kan abubuwan da suka danganci bin ka'idojin aiki.

A yayin taron ka kawo masu jawabi da zasu yi magana kan kalubalen dokokin aiki da suka fuskanta a wurarensu da ya dda suka shawokan matsalolin.

Jenness ya ce, '' a yawancin lokaci hanyar magance matsalolin ba a fili suke ba karara kuma ba lalle a iya hasashensu ba, abu ne da ke bukatar tattaunawa a bayyana.''

Masanin ya ce, me yasa ma mutane suke irin wadannan halaye na rashin sanin ya kamata a harkar aikinsu? Kamar wannan ta'ada ta shan miyagun kwayoyi.

A karshe kwararren ya ce, ''yawancin lokaci manyan jami'an kamfani da sauran wuraren aiki suna yin abin da bai dace ba, inda za ka ga sun fi tunanin kansu maimakon illar da abin da suke yi za ta yi wa wurin da suke aiki.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Should you fire or help an employee with a drug addiction?