Sabuwar hanyar da ta fi wajen koyon harshe

Hakkin mallakar hoto alamy

Masarrafa ko hanyoyin shiga ayyukan intanet ko kwamfuta (uber da Airbnb da PlateCulture), na karuwa sosai da sosai a Indiya, kuma ta wadannan hanyoyi masu amfani da su suna kara kwarewa a harsunan da suke koyo.

Ga bayanin Lauren Razavi

A lokacin da Prashant Choudhary ya bar aiki da wani kamfanin inshora a Delhi ne domin ya kama sana'ar tukin tasi, ya dan fara kokarin magana da harshen Ingilishi mai dan kyau. Kafin ya fara tukin motar lamarin ba haka yake ba.

Choudhary ya bar aikin kamfanin inshorar ne saboda yana son ya dogara da kansa, kuma ya zama yana gudanar da rayuwarsa yadda yake so, to amma a sanadin sabuwar sana'ar tasa sai ya gamu da wani cigaba wanda bai yi tsammani ba.

A matsayinsa na direban tasi mai amfani da na'urar kididdigar kudin da fasinja zai biya (uber) ta kwamfuta, to sai ya kasance yana jin harshen Ingilishi a kullum.

Ta hakan ne ya ga cewa ya samu kyakkyawan cigaba wajen amfani da harshen Ingilishi.

Ya ce , ''ina jin dadin magana da Inglishi kuma a yawancin lokaci ina magana da wadanda nake dauka a motata da yaren.''

Ya kara da cewa, ''saboda ina amfani da wannan na'ura (uber) ya samu karin kwarin gwiwa na yin magana da Turancin.

''Ina haduwa da mutane wadanda suka fito daga kasashe masu yawa daban-daban, sannan ina tafiye-tafiye sosai, kuma haduwa da nake yi da fasinjoji iri daban-daban ba shakka ya taimaka mini kara fahimtar Ingilishin.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Choudhary daya ne daga cikin 'yan kasar Indiya a birane masu yawa kamar Delhi da Calcutta da Mumbai, wadanda yanzu suke aiki da hanyoyin hada-hadar cinikayya ta intanet (Uber da Airbnb da Fiverr da Rent the Runway).

Tun da da harshen Ingilishi ake amfani da wadannan manhajoji, 'yan Indiyar da suke amfani da su a kullum, suna samun cigaba a wajen amfani da harshen.

Bayan hira da tattaunawa da fasinjojinsa cikin harshen Ingilishi da kama tashoshin rediyo na yaren Choudhary, ya yi kyakkyawara dabara, da zabi yin amfani da wannan na'ura mai amfani da harshen Ingilishi, saboda zai rika sanin inda zai kai fasinjansa da harshen Turancin.

Da hakan ya zama daya daga cikin 'yan kasar ta Indiya da yawa da suke koyon harshen ta hanyar aikinsu na yau da kullum.

Irin wannan hanyar ce ake amfani da ita a Airbnb, wanda shafin intanet ne da ke ba wa masu mu'amulla da shi damar bayar da haya, ko kama hayar otal ko wani muhalli na gajeren lokaci, kuma da harshen Ingilishi ake amfani a shafin.

A yanzu akwai sama da gidaje 9,000 da aka bayar haya ta wannan hanya a kasar ta Indiya.

Mai magana da yawun kamfanin, Alison Wood ta ce, ''Magana da musayar al'ada na daga manyan alfanun da mutane da dama da ke amfani da tsarin ke cin moriya.

''Misali, wasu mutanen suna zabar yin tafiya ta kamfanin na Airbnb, domin hakan zai ba su damar yin mu'amulla da wasu yaran kuma da hakan za su samu damar iya wasu harsunan.''

Hakkin mallakar hoto bccf Flickr CC BYND 2.0
Image caption Wasu iyalan Indiya suna amfani da ayyukan shafin intanet na Airbnb domin 'ya'yansu na haduwa da wasu 'ya'yan kuma suna koyon wasu harsunan

Ram Kidambi ya bayar da hayar dakuna a gidansa da ke Hyderabad a kudancin Indiya ta hanyar Airbnb.

Ko da ya ke daman yana jin harshen na Ingilishi sosai, amma ya ce haduwa da Turawan Ingilishin ya taimaka masa wajen sanin sabbin sigogi na yaren da kuma lakantar yadda Turancin ya ke na Ingila da kuma na Amurka.

Haka shi ma tsarin gidan sayar da abinci na intanet na ''Start-up PLateCulture, wanda a cikinsa 'yan gari za su dafa wa bako abinci ya je gidan ya ci, yana bunkasa yaren na Ingilishi a fadin kasashe goma na Asiya da inda ake amfani da shi, wadanda suka hada da Indiya.

A yanzu shafin na harshen Ingilishi ne kawai ake da shi babu na wasu harsunan.

Wadda ta kafa tsarin Reda Stare, ta ce, ''muna karfafawa tare da ba da goyon baya ga duk wani kokari na musayar al'ada tsakanin masu dafa abinci da kuma baki, kuma hakika harshe na daya daga cikinsu.''

Ta kara da cewa, ''duk da dai wannan ba ya daga cikin tsarin cinikinmu da farko, amma muna farin cikin ganin wannan sabon fannin na koyon harshe ta shafin.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Malaman koyar da harshe ba sa mamaki a kan wannan sabon cigaba da aka samu, kuma suna daukarsa a matsayin wata hanya ta cigaba idan aka yi la'akari da ingantattun hanyoyin samun fasaha da aka yi a kasashe kamar su Indiya.

A kasa mai tasowa mutane da dama ba su da kudin da za su zuba jari a fannin cigaba kamar abin da ya shafi koyon harshe.

Amma samun hanyoyin intanet na samar da damar koyar da kai harshen Ingilishi, in ji Lea Aylett, darektan karatu a makarantar koyar da harsuna, ta 'The Language Gallery.'

''Koyo ta intanet abu ne da ya kunshi koyon harshen Ingilishin da kake bukata wajen tafiyar da harkokinta na yau da kullum da za ka iya fuskanta.

Cigaban da za ka samu na kai tsaye na koyon wani abu da kuma iya amfani da shi ta hanya mai amfani shi ne babban abin da ke kara karfafa wa mutum gwiwa.'' In ji Aylett

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The best new way to learn a language?