Anya ba yaudara wajen daukar aiki?

Hakkin mallakar hoto alamy

Ka nemi aiki sau daruruwan lokaci amma har yanzu babu ko daya da ka samu. Amma kuma da alkawarin za a waiwaye ka idan dama ta samu. An waiwayekan?

Abubuwa sun baci duk wani dan fata da ya rage maka ya dogara ne a wurin daya daga cikin tarin kamfanoni da hukumomin da ka nemi aiki da su, kuma kamfanin ya yi alkawarin ajiye takardarka da cewa nan gaba zai iya nemanka.

Shin irin wannan alkawari na da wani muhimmanci a wurinka? Ga abin da wasu daga cikin masu ziyarar shafukan BBC suka ce a kan tambayar.

Christine Choi ta rubuto cewa bisa saninta da kuma kwarewa a aiki da shafin intanet na Linked In, maganar za ta iya kasancewa da wani muhimmanci ko tasiri a wurin masu neman aiki

Ta ce,'' idan kamfanin ko jami'in da ke daukar aikin yana sha'awarka, sai dai ba ka dace da gurbin da ake neman cikewa ba a lokacin, zai sa ka a ransa, idan wata dama ta samu wadda za ka da ce da wurin sai ya neme ka.''

Kim Huynh tana ganin duk da cewa a wani lokaci, masu daukar aikin ba sa sake waiwayar takardarka ballantana su neme ka, a wani lokacin, wasu da gaske ne za su iya nemanka.

Huyhn na ganin yawanci idan babban kamfani ne ko hukuma ba sa sake nemanka.

''Suna son kawai ka da ka damu ne suka gaya maka haka, domin ka tafi ba tare da wani surutu ko zargi ba!''

''Amma idan kananan kamfanoni ne galibi suna rike da takardaraka, musamman ma idan da shugaban wurin kake mu'amullar neman aikin( ko kuma wanda kai tsaye za ka yi aikin ne a karkashinsa, idan ya samu).

Sun san aikin kuma sun san irin mutumin da suke bukata, saboda haka idan suka ga ba ka dace da shi ba a wanna lokacin, amma kuma ka ba su sha'awa, to suna sane da kai, da zarar dama ta samu za a neme ka.''

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Me yake zuciyar masu daukar aiki idan suka ce za mu iya waiwayar takardarka?

Huyhn na da shawara a nan ga masu neman aiki: ''Ka yi kokarin kulla kyakkyawar alaka, ta hanyar aikawa da sakon godiya ga mai daukar aikin ka kuma tambayi izininsa domin ka rika tuntubarsa daga lokaci zuwa lokaci ko da wata dama ta samu (za ka iya sanya shi cikin wadanda kake bi ta shafin Twitter da Linkedln).''

Mutuntawa

Marubuciya kuma tsohuwar mai daukar wa kamfanoni ma'aikata Amy Newman Smith, cewa ta yi, ita tana ganin masu daukar aiki galibi suna amfani da wannan magana ne saboda ba za su iya gaya maka cewa, ''yi hakuri ba ka dace da aikin ba ko kuma ma'aikacin da muke nema ba.''

Ko kuma ba za su iya fitowa fili su gaya maka cewa,'' kamar yadda muka gani a takardarka ka cika sauya wurin aiki kusan duk wata shida sai ka sauya wuri, a cikin shekaru ukun da suka gabata, wannan ne dalilin da ya sa muka ga bai ma kamata mu gana da kai ba.''

Newman ta bayyana cewa ita a lokacin da take aikin daukar ma'aikata, idan ka karbi takardun mutane (CV), tana auna takardar kowa a mataki daya zuwa biyar ( na daya shi ne ya fi), daga nan sai ta gayyaci ukun farko.

Ta ce '' a yawancin lokaci babu wani bambanci mai yawa tsakanin cancantar na lamba ta uku da na 4 da 5 da 6.''

A wani lokaci kamfaninta ya kan yi zaben tumun-dare, a dauki ma'aikacin da bai yi karko ba, saboda wasu masu neman aikin za su burge ka a yayin da kake yi musu tambayoyi na daukar aikin amma kuma sai ka ga idan an zo aikin ba su dace da gurbin ba sosai.

Ta ce to a nan maimakon ka sake sanya sanarwar neman ma'aikata, sai kawai ka koma ka dauko, sauran takardun wadanda suka nemi aikin ka sake zaba a ciki, in ji Newman Smith.

Dokoki sun bambanta daga kasa zuwa kasa. Slin Lee ita kuwa ta bayyana cewa a Amurka dokokin tarayya na hana nuna bambanci sun bukaci kamfanoni da su adana dukkanin takardun neman aiki na mutane akalla zuwa shekara daya ko da kuwa ba a dauki mutum aiki ba.

''Kuma idan akwai wata kara da aka shigar, to a nan kuma ana bukatar su adana dukkanin takardun da ke da nasaba da daukar aikin har sai an kammala shari'ar.

Yadda za ka iya juriya idan ba a dauke aiki ba.

A tsakiyar shekarun 1990 Daniel Dettmers ya kammala jami'a da digiri a fannin injiniya na nukiliya.

Ya ce, ''na aika da takardun neman aiki 108 zuwa cibiyoyin nukiliya 108 na Amurka, kuma an turo min da takardun kin dauka har 66 da alkawarin cewa, ''za mu ajiye takardarka idan ta kama mu neme ka idan gurbi ya samu.''

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Idan aka samu wani gurbin aiki, kamfani ya kan sake waiwayar takardun wadanda suka taba neman aiki a wurin, ba su samu ba

Babbar cibiya daya ce akalla ta cika wannan alkawari a shekara uku. Dettmers ya ce, a duk lokacin da wani gurbi na aiki ya samu, yana da damar a dauke shi, domin za a tura takardar tasa zuwa jami'in da ke aikin daukar ma'aikatan, sai ya yi watsi da ita, sannan kuma Dettmers ya ce sai a aiko masa wata takardar nuna kin daukarsa.

Ya ce, ''ana ma aiko min da takardar kin dauka na hatta a aikin da ban nema ba, na samu takardun kin dauka har guda 28.''

Wani abin alheri game da kin daukar aikin kamar yadda Dettmers ya rubuta shi ne, ''akwai wani gidan shaye-shaye da yake bayar da kyautar abin sha kan duk wata wasika ta kin daukar mutum aiki, wadda kamfani ya tura wa mutum. Na kan karbi goma a lokaci daya.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Do recruiters 'really' hang on to CVs when they promise to?