Ana hana mabada rago fata?

Hakkin mallakar hoto Hill Street Studios Getty
Image caption Allan-ba-ku-allan-karbe

Idan masu hali suka ba ka taimako za su yi tsammanin wani abu daga gare ka kai ma, kila tukuici. Idan ka yi kememe fa?

Ga nazarin Chana R Schoenberger

Tambaya: Idan zan tara wa kungiyata ta agaji da taimako kudin tallafi, wasu manyan masu bayar da agaji sukan kafe cewa tallafin da za su bayar yana da sharadi.

Idan misali suka yi alkawarin bayar da tallafin kudin gina wani sabon gini, za su iya cewa suna bukatar a bai wani kamfani da suka zaba aikin kwangilar, ko kuma sa iya ce mana mu yi amfani da kamfaninsu na lauyoyi wajen shirya takardun da suka shafi tallafin, domin kamfanin nasu ya samu kudi.

Ba ma son mu ki karbara tallafin kudi, amma kuma abu ne da ya sabawa ka'ida ka yarda da wadannan sharudda. Me ya kamata mu yi kenan?

Amsa: A matsayinmu na al'umma mun kirkiri wata al'ada ta gayyatar mutane su bayar da tallafi sannan kuma su samu tukuici na yabawa kan taimakon, kama daga bai wa mai taimakon takardar godiya zuwa sanya wa ginin sunansa.

Kungiyoyin agaji sun dogara ne wajen tara kudi domin tafiyar da ayyukansu, kuma za su iya cewa duk wani tsari na neman taimako wanda bai saba ka'ida ba abu ne mai kyau.

Hakkin mallakar hoto Gunay mutlu Getty

Amma bai kamata a ce taimako ya zama da son kai ba. Bayan yabo da godiya bai kamata a ce masu bayar agaji sun ci wata moriya ko a basu wani kudi daga asusun ba ta kowace hanya kuwa.

A duk lokacin da masu bayar da tallafi suka yi amfani da tallafin a matsayin wata hanya ta azurta kansu ko abokansu, to sai kama hanyar aikata ba daidai ba.

Agajin da suka bayar ba ya halatta musu yin hakan, lamarin sai ya sa ka ji ba dadi.

Kana da basira da ka bi kadin wannan dabi'a in ji Allison Daubel, masaniya kan harkokin kyautata dangantakar aiki a birnin New York.

Ta ce, ''abu mafi muhimmanci wurin tara kudin agaji shi ne masu bayar da tallafi su bayar da kudi, kuma a bayar da wannan tallafi ya zama cewa ba su yi amfani da dangantakar da ke tsakaninsu da masu tara kudin agajin ba, domin cin wata moriya ko kuma su amfana wa wani wani abu ba.''

Ta ce, ''abin da za ka yi shi ne ka gana da masu gudanar da harkokin kungiyar taka, ku yi wani tsari kan yadda za ku karbi taimako, ku nuna karara cewa ba za ku bari a gindaya muku wani sharadi na kudi ba.''

Ya kasance cewa kuna da wasu takardu na ka'idoji da za ku nuna wa duk wanda zai baku wani tallafi ya biyo da neman wata alfarma ta musamman.

''Ta hanyar fayyace irin taimakon da za ku karba, za ku fi samun kwanciyar hankali kan kudin da za ku tara, kuma ba shakka hakan zai kara kima da mutuncin kungiyar,'' in ji Daubel.

Wannan zai iya ware wasu masu bayar da taimakon, amma hakan shi ne zai zama nafi alheri ga kungiyar a gaba, kamar yadda ta ce.

Da farko za ka bukaci ka kori wasu wadanda za su iya ba da tallafin, amma idan tafiya tai nisa za ka jawo irin tallafin da kungiyarka ke nema, wanda ya dace da kima da al'adarka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. When the wealthy give, should they expect to receive?