Ka san tsirrai na magana da juna ta intanet?

Hakkin mallakar hoto Niggel Catlin Alamy
Image caption Zaren tsiron hunhuna (mycelia) kenan yana ratsawa a karkashin kasa tsakanin bishiyoyi da tsirrai (intanet)

Wata gagarumar hanya ce ta sadar da bayanai inda tsirrai suke sadarwa da taimakon juna da taimakonta. Tsiron hunhuna na karkashin kasa kenan.

Nick Fleming ya yi mana nazari

Gagarumar hanya ce ta da ke bunkasa sadarwa tsakanin tarin miliyoyin daidaikun jama'a.

Tana hada zumunci tsakanin wadanda suke warwatse a wurare daban-daban, su rika ganawa tare da taimakon juna. Haka kuma tana ba su damar aikata wasu nau'ukan sabbin laifuka.

To ba wai fa muna maganar intanet ba ne, muna magana ne a kan hunhuna (fungi). Hular kwado (mushroom) na daga nau'in halittar hunhuna da muka sani, kuma yawancin jikinta ya kunshi 'yan siraran abubuwa ne kamar zare (mycelium).

A yanzu mun gano cewa wadannan zarurruka suna aiki ne kamar layukan intanet ta karkashin kasa, inda suke hada saiwowin tsirrai ko shuke-shuke ko bishiyoyi da dama.

Wannan bishiyar da ke gonarku ko lambun gidanku watakila akwai zaren (mycelium) da ya hada ta da wata bishiyar da ke can nesa da ita a wani wurin.

Muna kara fahimtar yadda wannan hanyar sadarwa ta karkashin kasa ta tsirrai take, fahimtar da muka yi wa tsirran na kara sauyawa.

Bishiyoyi ko tsirrai ba wai kawai suna girma ba ne kawai kamar yadda muka dauka.

Ta hada saiwowinsu da wadannan zarurruka na karkashin kasa na tsiron na hular kwado za su iya taimakon makwabtansu ta hanyar musayar abinci da bayanai, ko ma su yi zagon kasa ga wasu tsirran da ba su yarda da su ba ta hanyar tura musu guba.

Wannan intanet ta bishiyoyi (wood wide web; www), ita ma tana da nata nau'in na laifuka da ake aikatawa ta hanyarta.

Hakkin mallakar hoto my catkins cc by 2.0
Image caption Saiwoyin bishiyoyi na iya samar da wata matattar sadarwa tsakanin bishiyoyin karkashin kasa

Kusan kashi 90 cikin dari na bishiyoyin da ke doron kasa suna da alaka ta cude-ni-in-cude-ka da wannan tsiron halitta da ke haifar da hunhuna (fungi).

Masanin kimiyyar halittu na karni na 19 dan kasar Jamus, Albert Bernard Frank ya kirkiro da wata kalma ''mycorrhiza'' domin bayyana wannan alaka, wadda a cikinta tsiron (fungus) yake yi wa saiwowin tsirran mulkin mallaka.

A wannan alaka (mycorrhiza) su tsirrai suna ba wannan tsiro abinci, yayin da shi kuma yake taimaka musu su tsotsi ruwa, sannan ya samar musu da sinadarai (phosphorus, nitrogen), ta hanyar wadannan zarurruka na shi na karkashin kasa.

Tun shekarun 1960 aka tabbatar cewa wannan alaka da ke tsakanin tsirrai da wannan halittar tsiro na taimaka wa daidaikun tsirrai su girma.

Matattarar sadarwa ta wannan halittar tsiron (fungi) tana kuma taimaka wa tsirrai su kara karfin garkuwarsu.

Wannan na kasancewa ne domin idan tsiron ya yi wa saiwoyin tsirran mulkin mallaka, sai ya sa a rika samar da guba mai alaka da bayar da kariya ga tsirran.

Kuma kulla alaka kadai da shuka za ta yi da wannan matattara ta tsiron na sa ta samu karin kariya daga cutuka.

Wannan ba shi kadai ba kenan. Mun san yadda wannan alaka take hada zumunta tsakanin tsirran da suke nesa da juna.

Kwarrare a kan wannan halittar tsiron (hunhuna), Paul Stamets, ya kira wannan matattara, ''intanet din kasa ta ainahi'', a wata kasida da ya gabatar a 2008.

Ya fara samun wannan tunani ne a shekarun 1970 a lokacin da yake nazari a kan tsiron halittar, ko kuma hunhuna da nau'rar lantark ta ganin abu a dakin binciken kimiyya.

Stamets ya lura da kamanceceniya tsakanin zarurrukan tsiron hunhunar na karkashin kasa (mycelia) da kuma ARPANET, nau'in intanet na farko na ma'aikatar tsaro ta Amurka.

Masu kallon fim za su iya tuna fim din James Cameron na shekara ta 2009 mai suna Avatar.

A fim din wanda aka yi a kurmi, dukkanin bishiyoyin cikinsa suna iya sadarwa da juna domin sun hadu ta saiwoyinsu.

Suna iya sadarwa da kuma amfani da abinci ko wani sinadari tare, saboda wata hadaka da suke da tsakanin saiwoyin bishiyoyin.

Idan muka koma duniya ta zahiri kuma za mu ga kamar abin da ke cikin wannan fim yana da alamun gaskiya.

Hakkin mallakar hoto photos 12 Alamy

A yanzu Simard ta yarda manyan bishiyoyi suna taimaka wa kanana ta hanyar amfani da abin da za a iya kira intanet ta karkashin kasa ta wannan tsiro mai zarurruka.

Masaniyar tana ganin in ba domin wannan taimakon ba tsirrai da dama ba za su rayu ba.

A nazarin 1997, tsirran da suke cikin inuwa, wadanda ake ganin za su gamu da karancin abinci sun sami karin sinadari (carbon ) daga bishiyoyin da suka yi musu inuwa.

Sai dai wani abu game da yadda sinadaran ke samun kananan tsirran daga bishiyoyin shi ne abin dubawa.

''Mun dai san cewa abin na faruwa, amma abin da ba mu gane ba sosai shi ne yadda yake wannan tafiya,'' in ji Lynne Boddy ta jami'ar Cardiff a Biritaniya.

Hakkin mallakar hoto Tracy Gunn Alamy
Image caption Shukar tumatur na iya karbar sako daga makwabtanta

Yayin da ake ci gaba da wannan muhawara, wasu masu binciken sun gano shedara da ke nuna cewa tsirrai za su iya yin ma fiye da haka, domin za su iya sadarwa da junansu ta hanyar wadannan zarurruka (mycelia).

A shekara ta 2010 Ren Sen Zeng na jami'ar aikin gona ta South China a Guangzhou ya gano cewa idan tsirrai suka hadu da wannan tsiro (fungi) mai guba, sai su tura sakon guba cikin wadannan zarurruka (mycelia), wanda ke gargadi ga makwabtansu domin su sani su shirya.

Ya gudanar da wannan nazari ne a kan shuke-shuken tumatur. Kuma an gano ba tumatur din ne kadai ke yin hakan ba.

Hakkin mallakar hoto shotstock Alamy

To amma kamar dai intanet ta mutane, ita ma intanet din ta wannan halittar tsiro dangin hunhuna (fungi) yana da aibi ko laifi irin nasa.

Intanet dinmu (mutane) tana da keta haddin sirri, sannan ana amfani da ita wajen aikata manyan laifuka, kuma akai akai ana watsa kwayoyin cutar kwamfuta ta hanyarta.

Haka shi ma hade-haden sadarwa na tsiron halittar ya nuna ba su kadai suke ba, kuma makwabtansu miyagu za su iya cutar da su.

Wani abu shi ne tsirrai za su iya yi wa junansu sata ta hanyar intanet din tasu.

Misali akwai tsirran da ba su da halittar nan da suke yin abincinsu da taimakonta (chlorophyll) saboda haka ba za su iya yin abinci kamar sauran takwarorinsu ba.

Saboda haka wadannan tsirrai (phantom orchid)suna samun sinadarin (carbon) da suke bukata daga bishiyoyin da suke kusa ta hanyar wannan zare (na fungi) wanda sun hadu da juna ta hanyarsa.

Wasu tsirran suna satar sinadarin ne daga sauran bishiyoyi idan suna son yin hakan. Laifukan intanet da tsirrai kan yi za su iya fin 'yar karamar sata ma.

Hakkin mallakar hoto fotozone Alamy

Tsirrai suna gogayya da makwabtansu wajen neman abinci ko sinadarai kamar ruwa da hasken rana. A wannan fada ne wasunsu suke zuba wa abokan hamayyar gubar da za ta cutar da su.

Wasu masana kimiyyar sun nuna shakka kan wannan maganar, wadda saboda haka ne a 2011 masaniyar kimiyyar guba, Kathryn Morris da abokan aikinta suka shirya gudanar da bincike kan maganar.

A binciken da suka yi sun ga lalle wadannan zarurraka (mycelia) suna kai wannan guba.

Su ma dabbobi za su iya amfani da wannan intanet ta tsirrai, domin wasu tsirran sukan fitar da wasu sinadarai domin janyo kananan halittun kwayar bakteriya (bacteria) da na wannan halitta ta tsiron hunhuna zuwa saiwoyinsu.

Amma kuma wasu kwari da tsutsotsi da ke neman saiwoyi masu dadi da za su ci, suna iya tarar wannan sako (sinadarai) su cinye.

Hakkin mallakar hoto All Canada Photos Alamy
Image caption Bishiyoyi da sauran tsirrai sun hadu da juna ta karkashin kasa

Sakamakon tarin shedun da ake ta samu masana kimiyyar halittu da dama sun fara amfani da kalmar ''wood wide web'' domin bayyana sadarwar wannan tsiron na hunhuna (fungi), wanda yake samarwa shuke-shuke da sauran halittu.

'' Wannan intanet ta tsirrai tana sa sadarwa tsakanin shuke-shuke, har ma wadanda ba nau'in juna ba ta yi sauri tare kuma da inganci,'' in ji Morris, wadda ta kara da cewa, ''bama tunaninta saboda abin da yake saman kasa ne kadai muka saba gani.

Amma yawancin tsirrai da bishiyoyin da kake gani, ta kasa sun hadu da juna ba lalle ta saiwoyinsu ba kai tsaye, amma ta wadannan zarurruka na halittar tsiron hunhunar (fungi).''

Wannan intanet ta hunhuna tana nuna misali ne na babban darasin kimiyyar halittu, inda halittun da ake ganin ba tare suke ba, amma kuma sukan kasance sun hadu da juna, kuma za su iya dogara da juna.

''Masana kimiyyar halittu da jimawa sun san cewa halittu sun kukkullu da kuma dogara da juna,'' in ji Boddy.

Intanet din ta tsirrai (wood wide web) ga alama wani bangare ne muhimmanci na yadda wannan sadarwa take.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Plants talk to each other using an internet of fungus