Ka san yadda za ka nemi hakkinka?

Hakkin mallakar hoto alamy

Wani abu na muhawara kan albashi, shi shi ne yadda za a bambanta kudin ma'aikacin sa'a sa'a da wanda yake na kwantiragi. Ta yaya za ka tabbatar ana biyanka hakkinka daidai, ba cuta ba cutarwa?

Chana R Schoenberger ta yi mana nazari.

Tambaya: Lokacin da nemi aiki, idan aka tsara biyana a kan kowa ce sa'a, burina shi ne na rika nawa ko jinkiri wurin yin aikin. Idan kuma an tsayar da yawan albashina, abin da zan yi, sai na rika kokarin gama aikin da wuri.

Shi kuwa wanda ya dauke ni aiki burinsa kishiyar nawa ne, ma'ana a tsarin biyan albashi sa'a sa'a, ni ina jinkirin aikin domin in tara sa'o'i da yawa, a biya ni kudi da yawa, shi kuwa so yake na rika sauri a aikin.

Idan kuma a tsarin da aka tsayar min da yawan albashin da za a rika biyana ne, burina shi ne na rika kokarin gama aikin da wuri, amma mai aikin kuwa ba ya so na gama da wuri.

To a nan akwai wata hanya da za mu magance wannan bambanci, ta yadda ba za mu saba ka'ida ba, kuma kowannenmu ya gamsu, ba cuta ba cutarwa?

Amsa: Bai dace ba ka je neman wani aiki kana mai daukar cewa wanda kuke tattaunawar daukarka aikin da shi yana son ya ci da guminka ne, ma'ana zai ki biyanka hakkinka yadda ya kamata.

Haka kai ma bai dace ba ka ci da gumin wanda za ka yi wa aikin, wato kada ka yi masa koro a aikin. Wannan ya hada da yadda za ku tsara albashin da ya kamata a rika biyanka, ba tare da cewa wani bangare ne a tsakaninku ya fi cin moriya ba.

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Abin shi ne ka bayyana karara dalilin da ka caji abin ka caza da kuma yadda ka yi cajin

Akwai bambanci tsakanin jibga wa ma'aikacinka karin aiki, da sunan ba shi karin albashi, wanda hakan wata dabara ce ta ci da guminsa, da kuma jan aiki ya ci gaba zuwa wani lokaci, domin a rika biyan ma'aikaci a kan sa'a sa'a (wato aikin bai kai sa'a daya ba amma sai a kara shi har ya kai sa'a), wanda wannan kusan wata zamba ce.

''Kara tsawon wa'adin aiki ba abu ne da ya dace ba,'' in ji Claire Steichen, kwararriyar mai ba da horo kan ayyuka a New York.

Haka kuma wanda za ka dauka aiki yana bukatar sanin abin da ya kunsa, da kuma tsawon wa'adin da ya kamata na aikin.

Muhimmin abu a nan shi ne a samu fahimta ko sadarwa sosai a kan dalilin da ya sa ka caji kudin da za a biya da kuma yadda za ka cajin kudin.

Steichen ta ce, '' idan mutane sun san yadda za su kimanta darajar aikin da suke yi, kuma su bayar da ka'idoji da darajar abin da wasu suka biya su na aiki, to da ba za a samu wata matsala ba.''

Kwararriyar ta bayar da shawara cewa , ''dauki abin da ka koya game da yadda ake biyan kudin aiki, ka tsara wa'adi idan kana yi wa wasu aiki, daga nan ka kiyasta lokacin da wannan aikin zai kai ka ka gama.'' Ta kara bayani da cewa, ''magana ce kawai da ta shafi fahimtar yawanm aiki da kuma sauke nauyin aikin da ya rataya a wuyanka (na mai aikin).''

Idan ka samu sabon mai gida ko kamfani da za ka yi wa aiki, ka yi kokarin bayyana masa yadda albashinka zai iya karuwa bisa la'akari da yadda aikin yake. Ta haka za ka kauce wa shammatarsa. Kuma ka dau kanka kamar babban mutum ba wani karamin yaro ba, idan wata matsala ta taso. Ta ce, ''ka fito fili ka yi magana sosai idan akwai rashin fahimtar juna.''

Idan ba ka da cikakkiyar masaniya kan yadda aikin zai kasance, to ku yi ciniki kan nawa za a biya ka idan aka kamalla aikin.

Bayan kammala aikin, idan mutumin ya ce yana son kari a kai ko ka yi wasu muhimman gyare-gyare, ka nuna masa cewa zai biya ka aikin sa'a sa'a a kai.

Ta haka an kiyaye hakkin kowa a cikinku, kai da kake aikin da kuma shi wanda za ka yi wa aikin, kuma dukkanninku daman kuna son ganin aikin ya yiwu yadda ya kamata ne ai.

Matsala daya da za ka iya fuskanta ita ce idan yawan aiki ko lokacin kammala aikin ya karu ba tare da tsammanin hakan ba. To a nan sai ka je wurin mai kamfanin ko wanda ya ba ka aikin ka nuna masa cewa ga fa sauyin da aka samu, saboda haka sai ku kara yarjejeniya a kan kudin da zai biya.

Amma kana bukatar bayanai na alkaluma domin tabbatar masa da gaskiyarka, saboda haka ka kiyaye da lokacin da kowa ne aiki yake daukarka da kuma duk wata yarjejeniya ko tattaunawa da kuka yi a baya, inda kamfanin ko wanda ya ba ka aikin ya bukaci fiye da abin da tun farko kuka tsara za ka yi.

Idan akan son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Hourly vs fixed contracts: the great rate debate