Zamanin kwamfuta ya zo karshe?

Hakkin mallakar hoto Getty

Sai wata rana kwamfutar tafi-da-gidanka (laptop). Biro da takarda kuma a sauka lafiya. Kusan abin da ya faru kenan a taron tattalin arziki na duniya (Davos) na 2016, inda ba abin da za ka gani a hannu da aljihun yawancin mahalatta taron sai kananan na'urori da suka hada da BlackBerry.

Ga bayanin Lucy Marcus

Su ne ke tafiyar da harkokin kamfanoni na dubban miliyoyin dala, su ne ke tafiyar da harkokin shugabancin kasashe, da zuba jarin miliyoyin dala a kasashen duniya. Ba za su taba shiga inda za a neme su a kasa samunsu ba (ta waya), kuma dole ne su kasance da shirin aiki a kowa ne lokaci. To wace fasaha wadannan mahalatta Davos suke dogara da ita harkokinsu ke tafiya yadda ya kamata?

Anne Richards babbar jami'ar zuba jari ta kamfanin Aberdeen Assett Management ta rabu da kwamfutarta ta tafi-da-gidanka (laptop) gaba daya, a maimakonta yanzu tana amfani da kwamfutar hannu ta iPad guda biyu.

Ta ce, ''ji nake waya ta yi min kankanta a hannu. Kuma ga shi masarrafar manhajoji (apps) sun fi yin aiki da kyau a iPad. Rabona da kwamfuta (laptop) an yi shekaru.''

Kamar yawancin mahalatta taron na Davos, a ko da yaushe tana kan hanya(aiki) kuma za ta iya yin sama da mako daya ba tare da wani abin aiki ba illa wadannan na hannunta. To amma me ya sa take amfani da iPad biyu?

Sai ta ce, ''Zan iya cigaba da aiki kan wani abu ko in bar shafin wata kasuwa a bude a guda daya, sannan kuma a dayar in rika bin wasikuna na email ba sai na rika sauya shafuka ba.''

Mutane da yawa da na tattauna da su suna amfani da 'yar kwamfutar hannu ta iPad da kuma wayar iPhone a ko da yaushe. Misali shugabar kamfanin tuntuba kan harkokin kasuwanci Bain & Company, Orit Gadiesh, ta ce kusan a kowa ne lokaci tana amfani da wayarta ta iPhone da kuma 'yar karamar kwamfutarta ta hannu ta iPad.

Hakkin mallakar hoto Bain and Company
Image caption Orit Gadiesh shugabar kamfanin Bain & Co

''Rayuwata sai ta cakude ta zama kamar gizan jiragen sama da na kasa da kuma motoci,'' in ji Jim Moffat, jagoran kamfanin Deloitte Global Consulting Business Leader.

Ya ce, ''wayata ta iPhone tana da muhimmanci, ko aika amsar wata wasika ta gaggawa zan yi ga abokan aiki ko abokan huldar kasuwanci, ko kuma sakon tes zan yi da iyalaina.''

Amma ya ce wannan ba shi kadai ba ne dalili, yana mai cewa, ''Ina kuma fatan za ta sa ni ma in zama ma'abocin shafukan sada zumunta da muhawara domin in burge 'ya'yana uku 'yan zamani.''

To ina kuma maganar jami'in da ke kula da harkokin sadarwa da hulda da jama'a na babban taron kasuwancin na duniya, Adrian Monck? Kana jin yana bukatar wani abu da ya fi wayar komai-da-ruwanka, musamman a ranar da ya fi aiki a shekara? Ko alama.

Ya ce ''iPhone6 Plus dina tana da komai.''

Ka fara jin alamar wani abu? ''wayata za ta iya karbar duk wasu wasiku sannan iPad na dauke da duk wasu rubuce-rubuce ta kuma tabbatar da tura su zuwa ga ma'aikatana,'' in ji David Boehmer na kamfanin Heidrick & Struggles.

Shi bai ma tsaya a nan ba domin har ma ya dan dara sauran takwarorinsa, saboda, tuni ya daina rike biro ko takarda.

Hakkin mallakar hoto World Economic Forum
Image caption Adrian Monck, jami'in hulda da jama'a na taron tattalin arzikin duniya kusan yana yin komai na shi ne da waya yanzu

Idan ka so ka ce ni dan kauye ne, domin ni har yanzu ina son rubutu da biro da takarda wani lokaci, kuma yadda na lura a wannan dakin taro ba ni kadai ba ne.

Na rubuta yawancin wannan labarin ne da biro da takarda, amma fa a zamanance. Na je da biro na zamani wanda duk rubutun da ka yi a kan allonsa na musamman, rubutun yana shiga wayarka ta wata manhaja, wadda ita kuma kai tsaye take fito da shi kamar wanda aka rubuta da kwamfuta.

Bayan wannan na'urar za ta kuma ba ka damar ka mayar da rubutun cikin murya, yadda za a iya sanya wa a rediyo.

Mutane sun yi mamaki lokacin da na ce musu ai ba irin bironsu ba ne, kuma duk wanda ya duba ya jarraba shi ya yi matukar sha'awarsa.

Don kada ka dauka cewa duk wanda ya halarci wannan taro na Davos yana da iPhone, ni kam zan iya cewa, wannan taro zai iya bugun kirji da cewa shi ne taron da ya fi yawan masu Blackberry da na taba gani a wuri daya.

A wurin mutane da yawa suna da waya biyu, Blackberry ta aiki da kuma iPhone ko kuma wayar tafi-da-gidanka ta sauran harkokinsa da ba na aiki ba.

Yawancin wadanda na tattauna da su, sun nuna cewa har yanzu kamfanoni sun fi yarda da tsarin kare bayanai ko tsaro na Blackberry, kuma masu amfani da wayar suna jin dadin madanninta (keyboard).

Haka kuma kusan duk wanda na hadu da shi a taron, wanda yake wani aiki mai bukatar tunani ko bayanai, ko kuma zai yi rubutu da yawa, kamar dan jarida, har yanzu yana nan da kwamfutarsa ta tafi-da-gidanka (laptop).

Na shiga shagon kamfanin Microsoft da aka samar a wurin taron, inda na ga kusan kowa a wurin wanda ya je ya dan ci wani abu da kuma amfani da intanet ta Wi-Fi yana amfani ne da kwamfutar (laptop).

Hanyoyi da wayoyin hannu na zamani masu abubuwa daban-daban da aka samar a yanzu sun saukaka wa mutane tafiya da tarin kaya.

Yadda mutane suke da damar daukar kowace na'ura walau kwamfuta ta tebur ko ta hannu da sauransu, ka samu duk abin da kake nema ko ka yi aikinka ba tare da wata matsala ba, wannan ya tabbatar da komawa kan wayoyin hannu da irin wadannan ayyuka cikin sauki a taron duniya na tattalin arziki (Davos) na 2016.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How two iPads and a smartphone became the new normal