Mutumin da ke jagoranci ba hannu ba kafa

Hakkin mallakar hoto Peter Bowes

''Ba ni da hannu da kafafuwa da zan iya amfani da su,'' kalaman mutumin da aka haifa ba hannuwa ko kafafuwa ke nan, wanda ya koyi yadda ake iyo a ruwa da wasan gudu kan kan igiyar teku da wasan sauka a lema da kuma iya magana a gaban dubban mutane.

Ga bayanin Peter Brown game da mutumin

Wannan mutumin ya dauki hankalin dumbin dubban mutanen da suka hallara domin kallonsa, da farko saboda yadda yake da barkwanci, sannan kuma da bayani mai sosa zuciya da kalamai masu karfafa zuciya. Sannan kuma uwa uba saboda ma yadda yake tsaye a nan.

Nick Vujicic, mai shekara 32, shugaban kungiyar masu tallata jawabin karfafa zuciya (Attitude is Altitude), an haife shi ne ba hannuwa ba kuma kafafuwa.

Amma kuma duk da haka yana gwagwarmayar tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum, inda misali yake iya goge bakinsa da burushi, ya kuma zama mai jawabi na karfafa gwiwa.

Ba dai wani bayani na likitoci ko kuma a fannin aikin likinta na yadda wannan nakasa ta Vujicic ke aukuwa a jikin mutum. Yana da wata 'yar alama ta abin da za a kwatanta da kafa a bangarensa na hagu, wadda ke kare shi daga faduwa.

Da wannan 'yar kafa, wadda yake iya tsayuwa, yakan iya buga rubutu da kwamfuta da daukar 'yan abubuwa da yatsun kafar, har ma da buga kwallo.

Mutumin da ya yi ikirarin cewa shi hatsabibi ne mai matukar sha'awar yin abubuwa na kasada ya kan yi wanka ko wasan linkaya a ruwa, kuma yana wasan saukowa da lema daga sama (sama jannati).

Ba haka kawai wannan mutum ya samu wannan karfin hali ba, domin ya yi fama da damuwa kuma an rika takura masa a makaranta, har ma ya yi yunkurin kashe kansa a lokacin yana dan shekara goma.

A hankali a hankali Vujicic ya yi kokari ya kawar da wannan damuwa daga ransa, kuma sakamakon wani abu da ya faru tsakaninsa da mai gadin kofar makarantarsu, ya ba shi kwarin gwiwar zama mai jawabi ga jama'a.

Mutumin mai farin jini dan kasar Australiya, a yanzu ya yi yawo a kasashen duniya inda yake gabatar da jawabai na karfafa wa mutane gwiwa (ba nakasasshe sai kasasshe), ga kungiyoyin 'yan kasuwa da 'yan makaranta.

A shekarata ta 2015 mawallafin littafin tarihin rayuwarsa, 'Love Without Limits' da 'attitude is Altitude' wanda ya ziyarci sama da kasashe 50 ya gabatar da dubban jawabai, yana zaune ne da matarsa Kanae da d'ya'yansu biyu a California.

Vujicic yana tafiyar da wata kungiyar yada wa'azin Kirisa, wadda ke sayar da jawabansa na karfafa gwiwa da yaki da cin zarafin kananan yara a makaranta.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The man who leads with no limbs