Ɗan bambancin da ke tsakanin martaba da Izza

Hakkin mallakar hoto iStock

Yana da kyau a ce mutum ya yarda da kansa amma kuma girman kai na iya zama sanadin faduwarsa. Ga yadda ya kamata ka yi mu'amulla da mutanen da suke ji da kansu.

Nazarin Maria Atanasov

Kana jin karanka ya kai tsaiko? To ba shakka yarda da kai ko ƙwarin gwiwa abu ne mai kyau, amma kuma idan ya kasance kai ne ka-san-komai na ofishinku to ka kwana da sanin cewa wata rana za ka rena kanka.

Musamman idan ko da yaushe ba ka taka-tsantsan, kana ji ka fi kowa sani. Abin da hakan zai haifar, ita ce izza, wadda za ta sa abokan aikinka su zama ba sa sha'awar aiki da kai.

Mun ji ta bakin wasu jama'a kan yadda mutum zai iya aiki da mai girman kai a wurin aiki da ma sauran harkokin yau da kullum.

''Mutane masu ji da kai suna buƙatar kulawa kamar yadda sauran mutane ke buƙatar iskar shaƙa,'' in ji Angie Neik. Ta ƙara da cewa, '' suna buƙatar a yaba musu a kuma nuna ana sha'awarsu, a riƙa jinjina musu kamar ƙarshen duniya kenan.

Ko da yaushe ka riƙa koɗa su.'' Idan ba haka ba, za ka kwana kana musu da su, har ka gaji (ba shakka za ku yi ta musu saboda masu girman kai ba su yarda da tattaunawa ba, ba sa mutunta ra'ayin kowa sai nasu).

Amma a tuna in ji Suretta Williams. ''Mutanen da suka isa, ba sa bugun ƙirji da cewa su su ne.''

ƙarfin hali!

Wani lokaci girman kai yana tasowa ne daga basira. Anna Butler cewa ta yi. ''Abin da na fahimta shi ne, yawancin masu girman kai, ko dai masu basira ne (ko suna ganin su masu basira ne), ko kuma waɗanda suka kai wani matsayi ne ko cimma nasara a rayuwa ko ma duka biyun.

''Su waɗanda suke ganin su masu basira ne ( daidai ko ba daidai ba) suna ƙoƙarin fahimtar abin da ya sa sauran mutane ba sa tunani irin nasu.

Haka su ma waɗanda suka kai wani matsayi a rayuwa kuma suke da girman kai, suna ƙoƙarin fahimtar abin da ya sa sauran mutane ba za su iya tashi tsaye kamar yadda suke gani sun yi ba, su ma su kai matsayin da suka kai.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ainahin yadda lamarin yake, ''duk wanda yake da girman kai, ya yi wa kansa bahaguwar fahimta ne, kuma yana jijji da kai ne domin a ɗauka shi ya isa. Amma a zahirin gaskiya dodorido kawai yake yi,'' kamar yadda Ian Withrow ya bayyana.

Ya ƙara da cewa, ''idan har kana son ka yi aiki da irin waɗannan mutanen, abin da zaka yi kawai kan wannan hali nasu, shi ne ka biye musu ko kuma ka zare musu ido.

Amma fa ka sani kafin ka yi nasara a hakan sai ka ɓata lokaci ka gane abin da ke sa irin waɗannan mutane wannan halayya da kuma abin da ke sa ka riƙa ɓata rai a kansu ko kuma ka yi ta neman hanyar da za ka rama abin da suke yi maka.''

Karya da gaskiya a bayyane karara

Ita kuwa Jill Uchiyama na ganin girman kai yawanci yana samo asali ne daga ra'ayin da ba shi da wata alama ta fatse-fatse, wato wadda ba ta fito fili karara ba. '' Yawanci mutanen da ra'ayinsu suke kishiyar juna su ne masu girman kai,'' ta ce.

''Abu ne da kowa zai iya yi, musamman matasa da dama (idan za mu faɗi gaskiya dukkanninmu mun yi haka), waɗanda suke jin su ai tuni ma sun riga sun san komai tun ba su kai matsayin ba!''

Ta ce, zai iya kasancewa mutum ba shi da tunani da sanin ya kamata. ''Ka ɗauki mutumin da ya sa abin sauraren kiɗa a kunnensa (earphone) sannan ya rufe idonsa, kuma a ce kana ƙoƙarin koyar da sauran ɗalibai da ke wannan aji da wannan mutum, yadda za su yi wani abu. To wannan shi ne daidai misalin abin, ka san cewa ranka zai yi matuƙar ɓaci.''

Uchiyama ta bayyana hanyoyi uku da za ka yi maganin wannan lamari:

1. Ka ja baya kawai ka bar shi kawai ya yi ta surutunsa, ka kawar da kanka, ka nuna kamar ba ka san yana wurin ba, ka tafi ka ba shi wuri. Amma ka nuna masa alamar cewa ba ka yarda da abin da yake cewa ba, kuma ba ka da lokacin sauraronsa.

2. Kawai ka ce, ''To shikenan.'' Ka yi murmushi ka tafi abinka. Hakan ya fi saurin maganin al'amarin.

3. Ka yi wani barkwanci. Misali ka ce. ''Ba shakka ina ganin John ya san duk wani abu da mutum ya sani a kan sha'anin siyasa. Amma ina ganin za mu iya tattauna a kai yanzu.''

Mutum ya kalli kansa

A wani lokacin ba lalle ba ne mutumin da ke ji da kansa ko mai girman kai ya ma san yadda kalmomin da yake amfani da su da yanayin maganar tasa ke shafar wasu.

Ankita Singh ita kuwa cewa ta yi, ''ina ganin hanyar da ta fi dacewa ka ɓullo wa jahili da mai girman kai ita ce, ka fito fili ka gaya musu yadda kake ji,''

Ka gaya masa kai tsaye abin da yake yi mai kyau da kuma abin da ya kamata a ce ya gyara, misali ya riƙa tauna magana kafin ya furta ta, ko ka gaya masa ya zai ji idan wani ya gaya masa abin da shi yake gaya wa mutane.''

Ka tsaya kan ra'ayinka

Idan mutumin (mai girman kai ko jahili) ya ci gaba da yin abin yake yi, to kai kada ka sauya ra'ayi, ka tsaya kan matsayinka, in ji Butler, wanda ya ce''kai dai ka tabbatar kana da sheda mai kyau a kan duk abin da yake yi ko fade.''

Hakkin mallakar hoto Lionsgate
Image caption Wasu mutanen kansu kawai suka sani

Butler ya ce ,'' na yi shugabanni da yawa a wurin aiki waɗanda masu ji da kai ne waɗanda kuma na kafe a kan ra'ayina da su, kuma duk da cewa ba sa son hakan, amma suna kiyayewa da abin da ya sa hakan, ya yi tasiri kan yadda suke daukana.

Ka mayar da abin ya zama abin dariya kawai

Idan ka jarraba duk wata dabara ka ga ba ta yi ba. ''Kawai ka yi dariya ka manta da abin,'' in ji Aakanksha Joshi. Ta ce, ''ni ina ɗaukar masu girman kai kamar wasu masu wasan bandariya ne kawai. Galibi suna yaudarar kansu ne kawai.

Misali, na san wanda a wurin aikinmu yake yawan son amfani da manya-manyan kalmomin Ingilishi. Mutum ne mai girman kai, kuma sau da dama ya kan yi wa mutane dariya a kan yadda suke Ingilishi, yadda yake ganin ba su kware ba da sauransu.

Mutum ne mai jijji da kai da san iyawa. Mutum ne da ke da wuyar sha'ani ka yi aiki da shi, kuma kusan yana ba wa dukkanninmu haushi.

''Wata rana muna tattaunawa a kan wani abu sai yana son ya ce, 'ya kamata ka fadada wannan tunanin (expand), maimakon ya yi amfani da kalma mai sauki, sai ya yi abin da ya saba na amfani da manyan kalmomi, (exacerbate)'. Abin ya ba ni dariya, kamar cikina ya yi ciwo saboda dariya.

''Tun daga nan sai ya daina ba ni haushi, na daina damuwa da abin da yake yi,'' in ji ta. ''Sai na dauke shi a matsayin wawan da bai san ma'anar kalmomin da yake amfani da su ba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The thin line between self-esteem and self-obsession