Za ka iya ajiye babbar wayarka ka koma irin ta da?

Hakkin mallakar hoto Getty

Manyan 'yan kasuwa da shugabanni da fitattun mutane da ma sauran jama'a gama-gari suna ƙin amfani da manyan wayoyi na komai-da-ruwanka, su yi amfani da ƙanana irin na da.

Nick Clayton ya duba dalilin hakan

Danny Groner yana cikin jirgin kasa a karkashin kasa kan hanyarsa ta zuwa tsakiyar birnin New York, ga shi kamar sauran jama'a na cikin jirgin amma kuma wani abu daya ya bambanta shi da su; wayar da yake amfani da ita tsohuwa ce irin ta da, wadda ake daga murfinta.

Yana daya daga cikin 'yan kalilan din mutanen da ba sa rike da wayarsu ta komai-da-ruwanka suna yin wani abu da ita a cikin jirgin nan. Kuma yana alfahari ba ya daga cikin sama da kashi biyu bisa uku na jama'ar Amurka da suke da babbar waya ta komai-da-ruwanka ba.

Kamar hamshakan attajiran 'yan kasuwa irin su Warren Buffett da Stephen Schwartzman wayar da Groner yake da ita tsohuwa ce, irin ta da, wadda ake kira da tura sakonnin tes (text) da ita kawai.

To amma fa kkar ka dauka Groner wani dattijo ne ko in ce tsoho. A matsayinsa na dan shekara 32, Groner na daga mutanen da kamfanonin da ke kera manyan wayoyin zamani suke hari.

Matashi ne, kuma manaja ne a kamfanin hoto na Shutterstock, wanda yake da darajar hannun jari ta dala biliyan daya da miliyan 200 a kasuwa, wanda kamfani ne da ake nuni da shi kan irin ci gaban da ya yi a kasuwa.

Ofishin Groner yana hedikwatar kamfanin a katafaren dogon ginin nan na Empire State Building, da ke Manhattan a tsakiyar birnin New York, kuma hawa biyu kamfanin ya kama a wannan gini.

Ofishi ne da ya kunshi wuraren motsa jiki da hutu da shakatawa. Duk da cewa Groner yana kewaye da fasaha iri-iri ta ko'ina a wannan hedikwata tasu, to amma ya fito fili ya bayyana karara irin amfanin da yake samu daga kin amfani da babbar wayar salula ta komai-da-ruwanka.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yar fim Scarlett Johansson da tsohuwar waya

Ya ce, ''ba na son in wahalar da kaina ba, ina aikin sa'o'i 13 zuwa 14 a rana, a gaban kwamfuta, wannan ya isa. Ba sai na kai sa'o'i 17 ba.''

Duk da yadda ya fi sha'awar tsohuwar waya irin ta da, ya yarda cewa ba ta yadda za a ce kowa zai bi irin wannan ra'ayi nasa, a yi watsi da manyan wayoyi.

Ya ce, ''idan kowa irina ne to da ba aikin da za a yi,'' duk da cewa yana ganin kin amfani da babbar wayar na taimaka masa a aiki.

Idan aka fadada bincike aka shigo da sauran ma'aikata, kuma aka duba tasirin kallon talabijin da kwamfutar tafi-da-gidanka, za a tabbatar da maganarsa.

Masu bincike sun nuna cewa, ''daga cikin dukkanin wadannan na'urori, wayar komai-da0ruwanka ta fi tasiri sosai.''

Wata masaniya kan tunanin dan adam a jami'ar Harvard ta Amurka, Dakta Holly Parker, tana ganin amfani da karamar waya irin ta da na iya taimaka wa mutane su bambance tsakanin gida da wurin aiki.

Malamar ta ce, tana ganin kamfanoni za su fi amfana idan suka ba wa ma'aikatansu damar samun hutu, su wartsake daga gajiyar aikin da suka yi a ofis.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Editar mujallar Vogue Anna Wintour tana da wayoyi da yawa amma ta fi son tsohuwar wayarta
Sabo da kayan da

''Yawan amfani da tsohuwar wayar dai wani mataki ne na mayar da martani ga yanayin da mutum ke ji cewa shi kamar bawa ne na wayarsa ta komai-da-ruwanka.

Daukar ra'ayin amfani da tsohuwar waya ba karamin karfin hali ba ne na ka nuna cewa kana da iko da kanka,'' in ji lauya kuma masani kan tsarin amfani da fasaha, David Ryan Polgar.

Amma kuma yana ganin akwai wasu hanyoyin na daban da za ka iya nuna cewa kana da iko a kan fasahar da ta zama kamar gobarar daji, wadda ke kutse a rayuwar jama'a.

Hanyar ita ce, kawai kada ka bar wayarka (babba) a kusa da kai ko da yaushe. Ya ce, ''kwararren masanin fasaha ko kwamfutar da ya zabi ya yi amfani da waya irin ta da da kuma mutumin da ya zabi ra'ayin kin amfani da babbar waya, abu ne da ke nuna iko da 'yanci, wato alama ce ta matsayi.''

Ba shakka wannan irin dabi'a ko yunkuri abu ne mai saukin fada wanda yawancin mutane ba za su iya aiwatarwa ba. Wasu ma na ganin kila abu ne da ya zama wajibi a sauya dokoki domin mutane su samu damar kashe manyan wayoyinsu. Faransa na daya daga cikin kasashen da ke tunanin daukar wannan mataki na yin dokar da za ta ba wa mutum damar kashe wayarsa.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Har yanzu mawakiya Rihanna tana amfani da tsohuwar waya ta da

Abin mamaki wannan shawara ba ta fito ne daga kungiyoyin kwadago ba, maimakon haka mataimakin darakta ne na babban kamfanin sadarwa na Faransa, Orange, Bruno Mettling, wanda a watan Satumba na shekarar da ta wuce ya mika wani rahoto kan aikin zamani ga ministan kwadago na Faransa.

A wata hira da aka yi da shi daga baya ta tashar rediyo ta Europe 1, ya ce ko da yake babu wata doka da ta tilasta wa ma'aikaci ya kasance ko da yaushe da babbar waya kuma a kunne, ta yadda za a iya mu'amulla da shi ta intanet da sauran hanyoyin zamani, amma wannan bai yi la'akari da ainahin yadda mu'amulla take ba tsakanin ma'aikata da shugabanninsu.

Ma'ana a yadda al'amura ke gudana shugabanni ko manajoji sukan dora wa ma'aikatansu wasu ayyuka ko da ba sa ofis, matukar dai akwai intanet.

Ko da an yi dokar abu ne mai wuya ga yawancinmu mu kasa duba wayarmu(babba), mu ga sakonninmu da wasikun email kafin mu kwanta.

Wannan ne ya sa Ellyn Shook, shugabar sashen kula da ma'aikata ta wani kamfanin tuntuba na kwararru, mai suna Accenture, ta rika amfani da karamar waya.

A farkon bazarar da ta wuce ne ta yi kokarin daina zuwa da babbar wayarta gadonta, amma ta kasa, sai ta sayo tsohuwar waya irin ta da. Wannan ba yana nufin ta maye gurbin babbar wayarta ba ne da wannan karamar dindindin, ta saye ta ne domin amfani da ita idan tana son ta huta da aiki, sai ta kashe babbar.

Hakan ya biya mata bukata, domin a dalilin hakan ta samu damar shakatawa duk tsawon ranakun karshen mako a bakin teku, ba tare da ta duba wayarta ba, in jita.

Shi kuwa Groner cewa ya yi sam-sam ba zai sayi babbar waya ba, Ya kara da cewa, ''mutane na ce min wai zan iya barin wayata a aljihu ba sai na kunnata ba. Amma fa ni ban yarda da kaina ba.''

Ya ce, ''indai har ina tare da ita, to za ta kama ni ne kamar yadda su ma ta kama su.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Should you dump your smartphone for a flip-phone?