Ka san sirrin tasirin rashin nasara?

Hakkin mallakar hoto Getty

Idan ka yi ƙoƙarin cimma wani buri ba ka yi nasara ba, to ka dage ka sake jarrabawa, in har ba ka dace ba, kada gwiwarka ta yi sanyi, ka nace.

Tun muna yara ake gaya mana maganganu na azanci na ƙarfafawa gwiwa.

To sai dai akwai wata sheda da ke tabbatar da cewa rashin nasara bayan rashin nasara na karfafawa mutum gwiwa tare da sa shi kirkirar wata dabara ta kaiwa ga nasara?

Tom Pohlmann, shugaban shashen dabaru na kamfanin Mu Sigma, wani kamfani na kididdiga, ya ce akwai sheda, kasancewar ya yi nazari mai zurfi a kan matsalar jerin rashin nasara.

Ya ce, '' Sauyin da ake samu cikin hanzari a harkokin kasuwanci yana sa kamfanoni cikin matsin lamba domin su kirkiro da wasu hanyoyi akai akai, da sabbin fasahohi, wadanda ke sa su shawo kan wannan matsala ta hanyar gwada dabarun daya bayan daya.''

Rahoton kamfanin na Mu Sigma, ya nuna cewa faduwa da wuri kuma akai akai ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen cimma nasara a hanyoyin kasuwanci da dama.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Faduwa kasa wanwar tana da amfaninta

Masu bincike na kamfanin na Mu Sigma, sun fassara wannan a bayaninsu, a matsayin karfin tsananin gwaji, suna masu ikirarin cewa kimiyya za ta iya nunawa a zahiri cewa rashin nasara na haifar da dabara ko kirkira (kirkirar hanyar da mutum zai yi nasara).

Kwararru (injiniyoyi) da ke aiki a kamfanonin hada magunguna da kamfanonin motoci da wasu kayayyaki sun kara tabbatar da wannan magana. Shugaban kamfanin Haydale mai yin inki (tawada) da fenti wanda ke Biritaniya da Amurka da Koriya ta Kudu, Ray Gibbs, ya ce, idan har kana son kirkiro wani kaya mai kyau da zai yi fice, dole sai ka yi ta jarraba hanyoyi daban-daban, kafin ka kai ga samunsa, kana ta gyra kura-kurenka.

Rashin nasara ba abu ne maras kyau ba a harka ta kasuwanci. Hanya ce ta gano yadda wani abu yake faruwa, wadda idan aka bi ta yadda ya dace za a yi nasara, in ji Pohlmann.

Hatta katafaren kamfanin Apple shi ma ya samu kasnsa na rashin nasara, kamar kwamfutarsa ta hannu ta farko, 'The Newton' wadda Steve Jobs ya kashe nan da nan.

Sake tunani a kan dabararka

''Mutane da yawa har yanzu suna dauka rashin nasara wata alama ce ta gazawar mutum saboda haka suke kokarin kauce mata ta kowa ne hali,'' in ji Andrew Filev, shugaban kamfanin Wrike, mai yin manhajar kwamfuta da ke Moutain View a California.

''Ya ce, amma idan ka dauki kafa harkar kasuwanci a matsayin jerin matakan gwaje-gwaje, za ka fara ganin cewa rashin nasara wani mataki ne da ya zama dole ka bi kafin ka kai ga nasara.''

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Damuwa kan wani rashin nasara? Kada ka damu zai iya zama alheri a nan gaba

Duk wata kirkira ta kunshi hadari. A ko da yaushe akwai hadarin da ke tattare da jarraba yin wani abu sabo, na cewa ba lalle ya yi aiki yadda ake so ba.

Daya daga cikin hanyoyin da wannan ya fi tasiri ita ce ta bangaren yin manhajar kwanfuta, domin ita ba kamar yin babban rusho (na girki) na iskar gas ko lantarki ko firiji ba, aikin yin manhaja abu ne mai sauki da za ka jarraba yin wani abu, ka tura wa masu amfani da manhajar, su duba su ga idan akwai wani wuri da ke bukatar ingantawa ko gyara.

Abu ya tsufa tun kafin ka kaddamar da shi

Dauki misalin masana'antar mota; ''Motocin kawa da alfarma sun tsufa a lokacin da ake kan hanyar kai su kasuwa. To amma ka duba kamfanonin mota kamar Tesla ta Elon Musk, nan da nan za ka ga sun sabunta manhajar kwamfutar motar ba da wani bata lokaci ba, kuma ta juye ta zama ta zamani,'' in ji Stitian Westlake, babban daraktan bincike na kungiyar NESTA, wadda, ke kirkiro sabbin hanyoyi na bunkasa kasuwanci a Biritaniya.

Westlake ya ce, abu ne kamar manhajar wayarka ta iPhone, wadda ka san cikin sauki za a iya sabunta ta, daga wani wuri, ba sai an hada ta da wata na'ura ba, kawai kai tsaye za ta zama daidai da wata sabuwa da aka kirkiro yanzu.

Kamfanonin kade-kade da na magunguna, su ma sun fara bin wannan hanya ta kokarin sabunta kayayyakinsu akai akai. ''Abu ne da za a iya ganin na takura, amma kuma mai kyau ne wanda kuma ya wajaba,'' in ji Pohlmann.

Ya ce, ''Hakan yana sa kamfanoni su sauya tsarinsu irin na da, su bi na zamani, na gwaji da koyo akai akai.'' Shi Pohlmann, a wurinsa kirkira kamar jifan abin da ke tafiya ne da mashi, ko dai ka dage ka yi jifan nan da kyau yadda za ka samu abin, ko kuma ka yi ta jefa mashin daya bayan daya har ka dace.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The hidden psychology of failure