Kana son kare kimarka? To kada ka faɗi wannan kalmar

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kana da basira ana mutunta ka kuma ga shi ka ƙware a aikinka. Sai kwatsam ka yi wata magana da ta zubar maka da wannan kima, aka fara raina ka a wurin aikin. To ta yaya za ka dawo da wannan kima taka, ko kuma ka ƙara wata katoɓarar da hatta kai kanka kake shakkun kima da cancantarka da aikin?

Dawo da martaba da kima na bukatar lokaci da kuma kwarewa. Wannan magana ce da yawancin kwararru a shafin Linkedln suka tattauna a kai. Ga abin da biyu daga cikinsu suka bayyana.

Da farko ga bayanin Dakta Travis Bradberry shugaban kamfanin TalentSmart. ''Akwai lokacin da dukkanninmu muke azarbabin amfani da kalmar da ba mu san ma'anarta ba sosai,'' Brodberry ya bayyana a rubutunsa mai taken 'jerin kalmomi 20 da mutane ke amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba, wadanda ke sa a rena mutum, (20 Misused Words That Make Smart People Look Dumb).

Wadannan kalmomin ba sune matsala ba ''Kalmar da muke dauka cewa muna amfani da ita yadda ya dace ita ta fi haddasa mana matsala. Muna watsa su da sunan burgewa a taruka da wasikun email da kuma muhimman takardu, kuma duk wanda ya ji ko ya karanta su sai ya ji wani daban.''

Ga wasu daga cikin irin kalmomin a harshen Ingilishi:

Kadan (fewer, less); ana amfani da kalmar farko ne(fewer) idan ana maganar abin da za a iya kirgawa, yayin da kalma ta biyu ake aiki da ita idan ana maganar abu gaba daya, misali wanda ba za a iya kirgawa ba.

Kunshi ko hada (comprise, compose); wadannan kalmomin biyu na daga wadanda aka fi yawan amfani da su ta yadda bai dace ba a harshen Ingilishi. Ta farko (comprise) na nufin ya hada da, misali mutanen da aka zaba sun hada da, yayin da ta biyun (compose) ke nufin, ya kunshi misali toka ta kunshi abu kaza.

Na nufin (imply, infer); Kalma ta farko na nufin kai ga yadda kake ganin abu ba tare da ka fade shi ba kai tsaye. Ita kumwa kalma ta biyu na nufin ka yanke hukunci kan ma'anar abu daga abin da wani yake gani .

Sabani, akasi, Katari, dace (ironic, coincidental); mutane da yawa na yi wa wadannan kalmomi gurguwar fahimta. Misali idan ka yi targade ana gobe za ka tafi wasan sulun kankara, a nan za ka yi amfani da kalma ta biyu ne (coincidental). Sannan kuma idan ka tafi wasan sulun kankara wani tsauni, sai kuma aka samu dusar kankara mai yawa a gidanka, to a nan za ka yi amfani da kalmar farko ne (ironic) a maganar.

Shi kuwa Brian Canavan wanda ya kafa kamfanin Optiva Coaching cewa ya yi, ''dukkaninmu mun taba shiga wannan yanayin a wani lokaci, inda za ka ga komai ya tabarbare, kimarka ta zube.''

A rubutun da ya yi (3 Simple Steps to Recover From a Confidence Crash) mai taken matakai uku da dawo da kima da kwarin gwiwa.

Canavan ya rubuta cewa akwai hanya mai sauki ta sake dawo da kima, ''farko dai ka san kanka.''

Ya ce ,'' ka rubuta jerin abubuwan da ka iya da wadanda ka kware a kansu, ka rubuta komai da ka sani za ka iya, komai kankantarsa.'' Da ka yi hakan, ''sai kuma ka rubuta jerin abubuwan da ka san cewa ba ka kware a kansu ba, sannan ka duba ka ga ko za ka iya ware musu lokaci domin ka iya su.''

Wannan jerin abubuwa shi ne zai zama a matsayin abin da z ai rika tuna maka abubuwan da ka sanya a gaba da kuma wadanda za ka koya ko ka nemi kwarewa a kansu.

A gaba sai Canavan ya ba da shawara da cewa, '' ka tsaya ka duba da kyau ka ga inda kake son ka kai a rayuwa da kuma harkar kasuwancinka.

To daga nan kuma sai ka hada jerin abubuwan da ka rubuta ka kware a kai da kuma abin da kake so ka cimma. '' Akwai wani abu da babu a ciki wanda kuma kake bukata? To sai ka sake komawa mataki na farko ka duba ka ga ko za ka sake mayar da hankali ka bunkasa kwarewarka a wadannan fannoni.''

A karshe Canavan ya ce, '' ka rarraba abubuwan da ka rubuta kake son ka cimma zuwa wasu kananan ayyuka. Saboda me? Saboda idan ka rasa kima ko karfin halinka ba za ka so a ce ka kasa cimma wani babban abu da ka sanya a gaba ba kuma. Kana bukatar ka sake karfafa zuciyarka.''

Ya ce, ''a saboda haka ne sai ka fara da wani buri ko aiki dan karami wanda za ka yi saukin samun nasararsa, domin samun nasarar wannan dan karamin buri zai karfafa maka zuciya.''

Canavan ya bayar da shawara cewa adana bayanan wadanna nasarori na 'yan kananan abubuwa da ka sanya a gaba, kana ganin ci gaban da ka samu zai karfafa maka gwiwa fiye da da.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Want to look smart? Don't say this