Illar zaman ofis ɗaya da abokan aiki

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ƙazanta ta barin ledoji da kofunan shayi ko gahawa a kan teburan da kuke amfani da su tare da surutu na daga matsalolin da za su dame ka a babban ofishin da jama'a ke zama tare, inda ba wanda yake da ofis na kansa.

Michelle Goodman ta yi nazari

Tebur mai kazanta ko kwandon shara mai wari kadan ne daga abubuwa marassa dadi da za ka gani a wurin aikin da ma'aikata suke a babban zaure daya maimakon inda kowa yake da ofishinsa.

Kamfanin sadarwa na Influence & Co wanda yake a Columbia da ke Missouri a Amurka, yana alfahari da yake tafiyar da aikinsa a irin wannan wagegen ofis.

''Ba wanda ya ke da teburin kansa,'' in ji Melanie Janisse, darakta a kamfanin mai shekara biyu wanda ya ke da ma'aikata 70. ''Shi kansa shugabanmu a wuri daya ya ke zama da masu neman sanin makamar aiki a ofishin.'' In ji ta.

A bangaren amfanin irin wannan tsarin na ofis kuwa za a yi maganar gudanar da aiki cikin gaskiya ko keke da keke ba kumbiya-kumbiya kuma ma'aikata na kasancewa cikin kuzari da annashuwa, baya ga yin aiki tare da hadin kai.

Sai dai ba a banza ake samun irin wannan yanayi ba, domin akwai matsalolin da ke tattare da wannan walwala da 'yanci na wurin aiki

Janisse ta ce, '' Ba wanda yake daukar alhakin kazantar da ake bari a tebura, kuma za ka ga kusan ko da yaushe ga takardu nan da kofunan ghawa da shayi a ko'ina a ofishin.''

Yadda kamfanoni suke yin wannan tsari yanzu na amfani da babban zaure daya a matsayin ofis na dukkanin ma'aikatansu, akwai yuwuwar wani ma'aikaci ya bata wa abokin aikinsa rai.

Bayan bata tebura da kazanta ko kwandon shara mai wari, sauran matsaloli sun hada da abokan aiki masu surutu, da abinci mai wari, da abokan aiki masu kazanta (wari), wadanda za ka ga sun je wuraren da ba a bukatarsu a ofishin.

Ga kuma ma'aikatan ma da za ka ga suna barin wasu abubuwan da za su iya ji wa mutum ciwo idan ya taka su a ofishin, kamar fil ko allura. Kate Lister, shugabar kamfanin Global Workplace Analytics, kwararru kan tsara ofisoshin ma'aikata wanda ke Carlsbad a California, ta ce ''Yawanci irin wadannan manyan ofisosi za ka ga kamar ajin makarantar kananan yara ne 'yan reno.''

Lister ta ce, ''Idan ana son ganin an ji dadin irin wannan wagegen ofis to sai an kafa wa ma'aikata wasu dokoki a kan komai, daga tsafta zuwa kama tebur da barin surutu a wani lokaci da ilmantar da ma'aikata dukkansu sun zama dole.

Hakkin mallakar hoto Getty

Kate North mataimakiyar shugaban kamfanin Work.com, wanda ke shirya wa ma'aikatan da ke da irin wannan ofis horo ta intanet, ta ce dole ne sai an ware ayyukan da ya kamata a rika yi a wuri kaza da wuri kaza daga wannan lokaci zuwa wancan lokaci, domin kada wani ma'aikaci ya je wurin da bai kamata ba a lokacin da bai dace ba har ya bata aikin wasu.

George Coffin na kamfanin laturoni na Plantronics na mai gudanar da harkokinsa a Afrika da Turai ya dauki tsarin karantar da ma'aikata ne tare kuma da tunatr da su a ki a ki kan dokokin aiki a irin wannan ofishi, domin tabbatar da ganin ma'aikatansa sun zama masu da'a ba tare da sun takura wa wani ba.

Lokacin da bangaren kamfnin wanda Coffin ke kula da shi, mai mutane 120 ya koma irin wnnan ofis na gaba daya a Biritaniya , a 2011, ya umarci ma'aikatansa da ko dai su rika dauke duk wat shara ko abin da ya lalace ko kuma su kirawo ma'aikatan da ke aikin gayaran wurin su kwashe.

Kamar yadda za ka yi tsammani ba kowa ba ne ya kiyaye da wannan doka. Wani rukunin ma'aikata sai ya kasance ba ya kula da tsaftar wurin a duk lokacin da 'yan rukunin suka yi amfani da wuri.

Wata rana sai suka yi amfani da wani bangare da ake taro a ofishin suka kuma bar shi kaca-kaca da yamma, kuma su ne za su yi amfani da shi washegari da safe, da Coffin ya gano su suka bata wurin sai ya sa aka bar shi haka. Da safiya ta yi suka zo taro, suka ga wurin ba gyara suka fara korafi, sai Coffin ya gaya musu ai su suka yi haka da wurin.

Coffin ya ce, ''Tun daga wannan rana 'yan wannan rukuni ba su kara ba ni matsala ba.

Tasirin abokan aiki

Matsin lambar abokan aiki zai iya sa a samu natsuwa a irin wannan ofis in ji North. Naomi Hirabayashi ta kamfanin DoSomething.org ita ma ta yarda da haka.

Domin tabbatar da wani lokaci na ntsuwa wanda kowa zai mayar da hankalinsa a kan aikin da ke gabansa domin ya kammala kafin karshen kowane sati, sai suka ware karfe 1:30 na yamma na kowace Alhamis.

A wannan lokaci na wannan rana ba wani ma'aikaci da zai yi wani surutu ko magana ko ma yin waya a kusa da wani, domin kada ya duke masa hnkali ko ya dame shi.

Kamfanin Influence & Co na New York, shi ma ya bullo da irin wannan tsari na yin shiru ranar kowace Laraba da safe. Haka kuma domin tabbatar da tsaftar wurin, kamfanin ya bullo da wani tsari inda duk ma'aikacin da aka samu da barin datti zai biya dala daya, inda ake sa kudin asusun liyafar ma'aiktan.

Shi kuwa kamfanin Plantronics a duk lokacin daka samu wani ma'aikaci da yake damun mutane da surutu ko wata dabi'a, sai Coffin ya kai kara wajen, shugaban da ke kula da bangaren ba tare da faden sunan ma'aikacin da ke saba doka ba, shi kuma ya yi wa 'yan bangaren gaba daya magana, ya jaddada musu dokar da ta hana wannan abu.

Coffin ya ce da wannan tsari ma'aikatan suna jin dadin yadda suke sa ido a kan junansu, suna kuma alfahari da yadda suke kula da tsaftar ofishin, kai kace kamar a rnr suk kama ofishin, wanda kuma tun 2011 suke.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Rubbish, chatter, squatters: The open office dark side