Ka san illar soyayyar bako da 'yar kasa?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Zuwana sabon wurin aikina a ƙasar waje sai shugabana ya gargaɗe ni cewa wasu daga cikin 'yan matan da ke aiki a ofishinmu za su iya nuna min soyayya.

Chana R Schoenberger ta yi nazari

Shugaban ya danganta hakan ga ɗimbin albashin da ake biyan ma'aikata 'yan ƙasashen waje. To abin dai kamar da ƙasa domin dai a yanzu wata budurwa da ke aiki a ofishin namu, ta miƙa min goron gayyata, tana son mu hadu a ƙarshen mako, bayan aiki, mu je yawon shaƙatawa.

Ina sonta kuma ita ma ina ganin tana sona, amma kuma ina ɗari-ɗari saboda ra'ayin shugabanmu a kan lamarin da kuma gargaɗin da ya yi min. Me ya kamata na yi?

Amsa: Akwai matsaloli biyu a kan wannan lamari. Da farko, a matsayinka na ɗan ƙasar waje, kana wata ƙasa ne daban saboda haka ba a san wace al'ada za a yi amfani da ita ba a nan: al'adar ƙasarka ko kuma ta ƙasar da ka je aikin?

Abu na biyu kuma shi ne, ka samu kanka a cikin soyayyar wurin aiki, wadda aba ce mai wuyar sha'ani ko da a wace ƙasa ce kuwa.

''Ka yi a sannu,'' in ji Amy Nicole Salvaggio, mataimakiyar farfesa a fannin kimiyyar tunanin ɗan adam a jami'ar New Haven da ke Connecticut a Amurka, wadda ta yi nazari a kan soyayyar wurin aiki.

Kowa a ofishin ya san ma'aikatan da ke soyayya a tsakaninsu, kuma, ''soyayya tsakanin ma'aikaci ɗan kasar waje da 'yar ƙasa za ta iya ɗaukar hankali sosai,'' in ji Salvaggio.

Domin sanin abin da ya kamata ka yi idan kana soyayya da 'yar ƙasa a al'adar ƙasar su yarinyar, sai ka tambayi wasu mutane a waje (ba wurin aikinku ba) yadda tsarinsu yake.

Wasu kamfanonin suna da tsarin taimaka wa ma'aikatansu 'yan waje kan yadda za su saba da yanayin ƙasar da suka je aiki.

To ƙwararrun da za su taimaka maka sanin garin, za su iya taimaka maka a kan wannan lamari. Ko kuma ka tambayi sauran baƙi da suka riga ka zuwa ƙasar yadda abin yake. Daga nan kuma sai ka kwatanta yadda al'adar take da ta ƙasarka.

Idan al'adun biyu sun sabawa wa juna, sai ka zabi me sassauci ka bi, ka bijirewa wadda ta yi tsauri.

Idan ma'aikata na soyayya a tsakaninsu, za ka ga ana zargin cewa ba sa mayar da hankalinsu a kan ayyukansu idan sun zo ofis. Wannan zai kawo saɓani da damuwa da ƙorafi idan sauran ma'aikata na ganin wahalar na ƙarewa ne a kansu, kamar yadda Salvaggio ta ce.

Abin takaicin shi ne, ''idan ɗaya daga cikinsu yana amfani da damar ne (soyayya) domin cin wata riba, to ka san cewa akwai ranar ƙin dillanci,'' Salvaggio ta yi gargaɗi.

Ita yarinyar 'yar ƙasa tana da wata manufa ne kamar son kuɗi, ko samun ƙarin girma, ko kuma tana son ya riƙa tura ta wani aiki na samu?

Idan amsar wannan tambaya a'a ce, wato yarinyar tana wannan soyayya da ma'aikacin ne ba domin cin wata moriya ba, to za ka iya cigaba da soyayyarka da ita, za ka iya watsi da duk wasu surutai da ake yi a ofishin, ta hanyar tabbatar da cewa aikinka na gudana yadda ya kamata.

Salvaggio ta ce, ka dage sosai a wurin aikinka kamar yadda kake yi a baya. Kada ka gaya wa shugabanka ko abokan aikinka cewa kana aiki tukuru kamar yadda kake yi da, kawai ka nuna musu a zahiri.

Kada ka ɓoye soyayyar da kake yi da ma'aikaciyar. Salvaggio ta ce, ''idan ta fito fili aka gane, shugabanka zai ga kamar ka yaudare shi; da farko, saboda zai ga ka ƙi ɗaukar shawararsa, na biyu kuma saboda ka nuna cewa ba ka yarda da shugaban naka ba sosai har ka gaya masa abin da ke tsakaninka da matar.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. A foreign affair: When expats date locals