Riga mai cajin waya na nan tafe a kasuwa

Hakkin mallakar hoto Bryan Derballa

Maganar nan da muke yi a yanzu, wasu masana na nan suna fafutukar yadda za su ƙirƙiro kayayyakin sanyawa kamar su safa da takalma da riguna masu fasahar zamani iri daban-daban, ciki har da riga mai cajin waya.

Elizabeth Garone ta yi mana nazari

A shekarar 1919 mutumin da ya kirkiro kungiyar masu hasashen yadda rayuwa za ta kasance a gaba a fannin fasaha na kasar Italiya Filippo Tommaso ya shammaci mutane a lokacin da ya sanya lakataye mai kwan lantarki, wanda shi da kansa ya kirkiro.

Masanin ya tsara shi ne ta yadda a duk lokacin da yake son jaddada wata kalma ko wata magana a lokacin da yake iawabi ga jama'a sai kwan lantarkin ya haska.

A yau kusan shekara dari bayan wannan fasaha, an samu abubuwa masu yawa da ke kunshe da fasahohi da dama, kuma ana ci gaba da kirkiro wasu daban-daban wadanda za a sanya su a saukake a tufafinmu da kuma rayuwarmu.

Misali a yau an kirkiro rigar da ke sauya yanayin sanyi ko zafi da ake ciki ta yadda za ta dace da yanayin da mutum yake bukata, idan ana sanyi sai ta sa mutum ya rika jin dumi sannan kuma idan ana zafi sai ta sa ya rika jin sanyi daidai gwargwadon yadda jikinsa zai so.

Akwai kuma maganar riga mai cajin waya, wadda idan mutum ya sanya ta, ba ya bukatar yawo da wani abu na cajin wayarsa. In dai yana sanye da ita za ta rika cajin wayarsa.

Hakkin mallakar hoto Bryan Derballa
Image caption Amanda Parkes ta ce, ''ana kirkirar kaya masu fasahar zamani a jikinsu ne musamman domin saukaka rayuwa.''

Kayayyakin sanya wa a jiki masu fasaha ba ana kokarin yinsu ba ne domin a nuna an gano fasahar yinsu ba ne sai dai domin nema wa jama'a jin dadi da saukin rayuwa in ji masaniyar fasahar tufafi Amanda Parkes, wadda ke New York.

Masaniyar ta kara da cewa, kaiwa ga wannan mataki, abu ne da ke bukatar hadin kai da gamayyar bangarori biyu wadanda suka yi hannun riga da juna, ma'ana wadanda kusan ba su da alaka da juna: tufafi da fasaha.

Parkes ta ce, ''ba wai ana nufin sai kowa ya zama kwararren masanin lantarki ba kuma ya kasance kwararren mai zayyana tufafi, magana ce kawai ta fahimtar aikin juna.''

Tuni dai bangarorin biyu suka fara karo da juna ta wasu hanyoyi masu ban sha'awa wadanda ba a yi tsammani ba, da kuma kayayyakin da ba lalle za a iya kiransu fasahar sanya wa a jiki ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Robar hannu mai fasahar zamani, wajen sanin bugun zuciya da tafiyar mutum

Kamfanin yin takalman mata masu tsayi da tsini da ke Los Angeles, Thesis Couture, yana sake tsarin yadda takalmin yake, ta yadda mata za su fi jin dadin sa shi, inda kamfanin ya tattaro kwararru daga fannoni daban-daban, da suka hada da masanan kimiyyar zuwa sama jannati da likitan kashi da kuma ita Parkes, karkashin jagorancin Dolly Singh, wadda ta kirkiro kamfanin.

Parkes ta ce abin da suke so su yi shi ne, suna kokarin hada kwararrun ne domin samar da wani tsari daya na kayan ado (takalmi) wanda kuma ya kunshi fasaha.

Hakkin mallakar hoto Bryan Derballa
Image caption Amanda Parkes ta dukufa aikin kirkirar fasahar zamani a kayan sawa

Sai dai Parkes ta ce, za a dauki lokaci kafin kayayyakin sawa su bunkasa da fasaha in ji Parkes. A duba yadda intanet ta fara a lokacin da aka kirkiro ta.

''Lokacin da aka kirkiro ta da farko, an dauke ta a matsayin hanyar sadarwa kawai, ba mu taba tunanin yadda mutane masu basira za su yi irin abubuwan da ake yi da ita ba a yau. Amma dai mun san tana kunshe da abubuwa da yawa.''

Haka shi ma wannan yunkuri na kirkiro kayayyakin ado ko na sawa masu fasaha a jiki, masana na na cewa abu ne da zai fadada sosai. Kuma tuni kamfanoni na tururuwar shiga a dama da su a fannin.

Hakkin mallakar hoto Hutton ArchiveGetty Image
Image caption Lakataye mai hasken lantarki a rigar Filippo Tomasso Marinetti a shekarar 1919

Ana sa ran kayayyakin sanya wa da jama'a ke amfani da su masu na'urorin fasaha a jikinsu, kama daga awarwaro mai na'urar da ke sa a gano duk inda yake, zuwa agoguna masu Bluetooth da zobuna masu mashigar shafukan intanet (apps), ana sa ran za su kai miliyan 110 zuwa karshen wannan shekara, kuma za su kai miliyan 237 da dubu 100 a shekarar 2020, kamar yadda binciken kamfanin fasaha na IDC ya yi.

Parkes tana ganin ainahin kayan sawa masu fasaha za su kunshi tufafi ne ka makamantansu, ''idan muna maganar zayyana domin sadarwa tsakanin kaya da jiki, ba magana ce ta kirga sawu ko bugun zuciyar mutum ba.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gabriel Platt dauke da riga me shokin (jan lantarki) domin kariya daga masu fyade

A yanzu dai wannan fasaha ita ce take tashe. Misali rigar Polo ta Ralph Lauren, tana lura da bugun zuciya da numfashin da sauran abubuwa na jikin wanda ya sa ta, sannan kuma ta aiki bayanan zuwa wayar iPhone ko agogon Apple. Ana sayar da ita a kan farashin dala 295.

David Norton ( marubucin littafin ,'Digital Context 2.0: Seven Lessons in Business Strategy, Consumer Behavior and the Internet of Things) ya ce, ''mun tunkari wani lokaci ne da duk abin da ka saya wanda za ka sanya a jikinka zai zama ko dai mai kunshe da wata fasaha ko kuma maras fasaha a jikinsa.

Duk da cewa za a cigaba da sayyar da kaya marassa fasaha a jikinsu, masu fasaha za su zama sun mamaye kasuwa kuma za a rika sayar da su da tsada, bayan kuma irin tasirin da za su rika yi a kan rayuwar mutane ta hanyoyin da ba a taba tsammani ba.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Riga mai kwanfuta

Todd Harple na kamfanin Intel, ya ce, ''mutanen da suke aiki a wannan fannin sai sun kasance kwararru a fannoni daban-daban, ciki har da ilimin kwamfuta a bangaren kaya da yin tufafi da fahimtar bukatar masu amfani da kaya, da kuma yadda za a yi amfani da fasaha a kirkiri abin da jama'a za su ji dadinsa a kullum.''

Ga masana fasaha, lokacin da mutum zai dankwafe a dakin bincike shi kadai ko da wasu abokan aikinsa domin kirkiro wata na'ura kila ya kusa zuwa karshe. A makarantar nazarin ilimin kayan ado ta New York (New York's Fashion Institute of Technology), babu wani fannin karatu a kan kayan sawa masu fasaha har yanzu.

A maimakon haka makarantar tana bin tsarin hada fannoni da dama da suka shafi wata fasaha da ake ganin za a iya hadawa a wani abu na sawa, kamar yadda Joanne Arbuckle ta makarantar ta ce. T kara da cewa ko ba komai, ''duniyar da su kansu daliban suke ciki ce.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. The people who want your shirt to power your phone