Ka san daƙiƙa 30 mafi muhimmanci a rayuwarka ta aiki?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Irin yadda ka gabatar da kanka da farko ka iya sa ka samu nasara a ganawar da za a yi da kai ta daukanka aiki ko kuma ka barar da damarka. To amma wace hanya ce ta fi wadda za ka iya samun nasarar birge masu daukar aikin?

Masu amfani da shafukan tambaya da amsa na intanet sun bayyana sirrinsu na yadda ake nasara a wannan rana.

Inina? Rikicewa? Sake nazarin matsalolin da ka gamu da su a baya?

A'a wannan ba ita ce ranar farko ba- barka da zuwa zagayen farko na tantancewar daukar aiki.

Da zarar ka shiga dakin ganawar, kana da dakika 30 ne kawai ka fayyace kanka, wato ka birge jami'an ko kuma ka watsa wa garinka kasa.

Za ka iya jin cewa yanayin kwarjininka shi kadai ya isa ya birge wanda zai shugabanci wannan ganawa ta daukar aikin, to amma akwai wasu kurakurai da mutane suke yawan yi tun daga farkon ganawar.

Domin sanin dabarun yadda za ka bullo wa wannan kalubale mun mika wannan tambaya ta cewa me za ka yi tun da farko ka burge lokacin da ka gabatar da kanka ga wanda zai maka tambayoyin daukanka aiki?

Kadan mai jan hankali

Da zarar ka shiga dakin ganawar kana da dakika 30 kacal da za ka nuna kanka kamar yadda mai daukar ma'aikata Adam Seabrook ya rubuto.

To amma burge wanda zai yi maka tambayoyin daukar aikin zai fara tun kafin ka shiga dakin. Ya ce, '' ka mutunta kowa. Ina da wani wanda nake nemo masa ma'aikata, wanda yake zuwa ya tambayi mai karbar baki a wurin aikin yadda mutanen da suka zo ganawar suka yi da suka shigo wurin tun kafin ganawar. Idan ya ji mutumin bai nuna kamala da mutunta ta ba, daga nan sai ya fitar da mutumin daga jerin wadanda za a tantance.

Idan ka nuna wa mai karbar bakin taurin kai da rashin girmamawa, to ka yi tsammanin cewa za ka iya yi wa duk wanda ka fara haduwa da shi kwatsam. In ji Seabrook

Kada ka yi ta dogon surutu

Mai daukar ma'aikata Mira Zaslove ta bayar da shawara ne cewa gabatarwarka ta zama mai kyau kuma mai sauki, kada ka je kana ta dogon surutu, kana dabur-dabur.

Maimakon haka ka yi gabatarwar daidai da yanayin masu ganawar da kai, ka mayar da hankali wajen fito da muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarka ta aiki, da abubuwan da kake sha'awa da nasarorin da ka samu da iliminka da kuma abubuwan da kake sha'awa na nishadi, wadanda suka dace da kamfanin da kuma mai ganawa da kai.

''Ka mayar da hankalinka kan abin da ya shafi aikin da za a gana da kai a kansa da kuma mutumin da zai yi maka tambayoyi. Ka sani cewa ita ganawar daukar aiki ba wai aba ce ta shafi sanin yadda kake da kwarewa ko menene matsayinka ba. Magana ce ta dacewarka da aikin kawai.''

Jami'ar ta yi gargadin cewa yawancin mutanen da ke zuwa tantancewar daukar aiki ba sa tsayawa su natsu sosai, saboda haka duk wanda zai je wata ganawa ta neman aiki ya tabbatar ya yi amfani da lokacinsa da kyau.

Ta ce,. ''kada ka dauka cewa mutumin da zai gana da kai ya ga takardar da ke kunshe da bayananka (CV ko resume). Kuma idan za ka gabatar da wadanna bayanai ka da ka yi kamar haddace su ka yi.

Ka zama mai barkwanci

Yaya za ka gabatar da kanka? ''Kamar yadda kowa yake,'' In ji Chris Lynam. ''Masu daukar aiki suna son mutane su zama kwararru, amma ba wasu butun-butumi ba.'' Ya bayar da misali: ''Akwai wata yarinya wadda ta zo neman aiki sunanta Fatima,'' kamar yadda ya rubuta. ''Ina son in san yadda ya kamata in rika fadin sunanta, na tambaye ta, 'ya kike faden sunanki 'fah-tima' ko 'fateema'? Amsar da ta ba ni ita ce, 'duk yadda ka ga dama, kana ma iya kirana Fatty idan kana so'.''

Sai kawai na yi dariya kuma na kaddara a zuciyata cewa wannan ta yi, 'nasara kawai!' Wannan ya faranta ran Lynam.

Ka zama da alkaluma a tare da kai

Ba wai sai ka bayyana wani abu na musamman a kanka ba, amma wajibi ne ka nuna cewa kana da akalla mafi kankantar ka'idar neman wannan aiki, kamar yadda Valerie Cooper ta rubuto kenan.

Ta ce, ''Wani abu kwakkwara da ya kamata ka tanada shi ne alkaluma kan irin cigaban da gudummawarka a wurin aikin da ka yi ta bayar. Ka san karin kason da aka samu na ciniki a kamfanin sakamakon aikinka, a misali?

Cooper ta ce idan ba ka san irin gudummawar da ka samar a wurin aikin naka ba, to ka yi kokarin samu wannan bayini, abu ne yake da muhimmanci wurin cigaban aikinka.

Kada ka takura kanka a kai.

Ba wani abu bane na cewa sai da shi za a dauke ka aiki, idan ba za ka iya gabatar da wata sheda ta alkaluman gudummawar da ka bayar a wurin aikinka ba, musamman idan kana neman a dauke ka a matsayin mai neman sanin makamar aiki ne a kamfanin. Za su ga cewa hakan dai zai kara wani armashi ne a kan yadda za a dauke ka.

Kai dai ka yi kokari ka je wurin cikin zama da doki. Ka kaddara idan dai an gayyace ka ganawar kamar ka samu aikin, kawai dai magana ce ta yanayin mutum ko dacewa da ala'adar wurin, ta yadda za a zabi wanda ya fi dacewa.

Idan kana son karanta wannan aharshen Ingilishi latsa nan The most important 30 seconds of your career?