Ka san ƙasar da ta fi dacewa da ma'aikata 'yan waje?

Hakkin mallakar hoto AFP

Za ka yi mamakin ƙasa ta farko idan ana magana kan waɗanda suka fi samun albashi da rayuwa mai kyau da inganci da sauran abubuwan jin daɗi waɗanda ma'aikaci ɗan ƙasar waje zai so.

Mark Johanson ya yi mana bincike

Singapore ce ake dauka kasa ko birni mafi tsadar rayuwa a duk duniya, amma kuma duk da haka nan ne wurin da ma'aikat 'yan kasshen waje suka fi so su je su yi aiki ko ma su zauna, kamar yadda wani bincike na kamfnin HSBC ya yi.

Masana na yaba wa da kasar a kan irin albashin da ake biya da irin damar cigaban aiki da kuma ingantacciyar rayuwar da ma'aikata ke samu a kasar.

Duk da irin tsabar tsadar rayuwar da ake fama da ita a kasar, abin da ya hada da tsadar abin hawa wadda ta linka ta New York sau uku, sama da kashi daya bisa hudu na ma'aikata 'yan waje da ke kasar wadanda aka tambaya, sun ce suna samun sama da dala dubu 200 a shekara.

Binciken na HSBC, ya gano cewa neman karin albashi ko samun damar cigaba a aikigalibi su ne suka fi sa ma'aikata neman tafiya wata kasa aiki, amma a yanzu wasu ma'aikatan suna tafiya wasu kasashen saboda wasu dlilai na kashin kai maimakon dalilai na kudi.

A duk mutane uku cikin biyarda aka tambaya sun ce ba su ga wani karin albashi ba daga komawarsu kasar, amma dai sama da rabinsu, wato kashi 53 cikin dari, sun ce rayuwarsu ta inganta bayan da suka koma can.

Hakkin mallakar hoto AFP

Kasashen da galibi ma'aikata 'yan kasashen waje za su fi son komawa domin samun rayuwa mai kyau, su ne, New Zealand da Spaniya da Portugal, yayin da Sweden ke zaman kasar da ma'aikata 'yan waje masu iyali za su fi son komawa, saboda kyawawan tsare-tsaren kula da yara da makarantarsu.

Jumullar mutane 21,950 daga kasashe 39 suka amsa tambayoyin binciken na bankin HSBC wanda aka yi a 2015. Bankin ya nemi su bayyana ra'ayinsu a kan komai kama daga aikinsu da wadatarsu ta kudi da kuma ingancin rayuwa.

New Zealand da Sweden da Bahrain da kuma Jamus su ne kasashe biyar da ke kan gaba wadanda ma'aikata suka fi son zuwa, yayin da Masar da Italiya da Brazil su ke kasa.

Binciken bai yi la'akari da batun 'yancin dan adam ba, abin da kungiyar kare hakkin bil adma ta duniya; Human Rights Watch ta ce babban abin damuwa ne a Bahrain ( wadda ta ke ta hudu a jerin kasashen) da kuma Hadaddiyar Dular Larabawa (ta tara).

Tsare-tsaren kyautata ryuwa da aka fi samu suna kasashen Gabas ta tsakiya ne.Wasu kashi 80 cikin dari na ma'aikata 'yan kasashen waje da aka tattauna da su a Oman suna samunn alawus din tafiye-tafiye a jirgin sama zuwa kasashensu, kuma a Qatar kashi 75 cikin dari suna samun alawus din gidaje. Akasarin ma'aikata a kasashen duniya kashi 33 cikin dari ne kawai suke samun wadannan alawus-alawus biyu.

Ba kasafai ake samun wasu tsare-tsare na musamman na kyautata jin dadin ma'ikatan kasashen waje a kasashen da ba na yankin Gabas ta tsakiya ba ne.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Birnin Singapore da daddare

Binciken na bankin HSBC ya bambanta sosai da wani irinsa wanda aka bayyana a watan Agusta na 2015, wanda InterNations Expat Insider ya sanya Ecuador, a matsayin kasar da ma'aikata suka fi son zuwa, saboda saukin rayuwa da saukin harkar kula da lafiya da kuma jin dadin rayuwa.

Mexico da Malta su ma suna gaban Singapore, wadda ta zo a matsayi na hudu. ''Maganar albashi da ingancin rayuwa a kasa kamar Singapore yawanci suna da kyau, amma kuma akwai wasu abubuwan da ake la'akari da su wajen yin tasiri ga rayuwar ma'aikata, in ji wanda ya kirkiro InterNations din Malte Zeeck.

Ya ce, ''wani abin da muke dauka da muhimmancin gaske shi ne, yadda 'yan kasa suke martaba baki, da kuma yadda bakin ke saurin sabawa da al'ummar kasa. Wannan zai iya zama daban a kasashe irin su Ecuador ko Mexico, idan aka kwatnta da kasashe kamar Switzerland da Jamus ko Singapore.''

A rahoton binciken bankin HSBC, a wasu lokutan a tsakanin kasashe goma da ke jerin farko, ma'aikata 'yan kasashen waje ba sa jin cewa sun saba da al'ummomin kasashen.

A kasashen Hadadiyar Daular Larabawa da Switzerlnd, wadanda suke ta tara da ta goma, kashi 42 cikin dari da kashi 43 ne cikin dari kawai suke jin cewa sun saba da al'ummomin kasar da suke zaune da su.

Kuma duk da kasancewarta ta daya a sakamakon, kashi 54 ne kadai na ma'aikat 'yan waje a Singapore suka ce sun jin dadin cakuduwa da l'adar kasar.

Idan kana son karant wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Is this the best place in the world to be an expat?