Kuɗi na ƙarfafa wa mutane guiwa a aiki?

Hakkin mallakar hoto Getty

Bincike na nuna cewa bayar da wani ladan kuɗi ko ƙarin albashi ko alawus-alawus ba lalle ya ƙarfafa wa ma'aikata guiwa ba kamar yadda ake cewa idan ana maganar kuɗin da ake ba wa ma'aikatan banki da shugabannin kamfanoni.

Ga nazarin Carinne Piekkema

Shin manajan banki daya ya kai darajar ma'aiakatan jiyya 1,000? Wannan tambaya mai ban haushi ita ce ta taso a farkon shekaran nan, a lokacin da aka byyna cewa Bob Diamond, shugaban bankin Barclays yana karbar albashin kusan fam miliyan 25, ko dala miliyan 40.

Wannan kudin ya kai a biya ma'aikatan jiyya 1,019 ko ma'aikatan jin dadin jama'a 859 ko ma'aikata masu kula da masu rauni ko tsofaffi 2,165 kamar yadda wani bincike na kwadago ya nuna.

Bankin na biyan shugaban wadannan makudan kudaden ne kuwa duk da cewa ribarsa ta kafin biyan haraji ta yi kasa da kashi uku cikin dari zuwa fam biliyan biyar da miliyan 500 ko dala biliyan tar da miliyan 500.

Tun daga bayyananar matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita shekara biyar da ta wuce, 'yan siyasa suke ta sukar ma'aikatan banki. Misali an ruwaito Shugaba Obama na cewa makudan kudaden da ake biyan ma'aikatan banki ya wuce hankali.

Su kuwa masu goyon bayan tsarin biyan makudan kudaden suna cewa ne, ba abu ne da ya kamata a rika kallonsa ta wata sigar dacewa ko rashin dacewa ba, magana ce ta yadda yadda za a rike kwararrun ma'aikata da kuma karfafa musu guiwa.

Duk da cewa babu wani abu na a-zo-a-gani da fannin kimiyyar dabi'u ya samar na bincike da zai a kan shedar cewa biyan kudaden na da tasirin da ake nufi, maganar abar a bincika ce.

Wannan tsari ya riga ya samu karbuwa da gindin zama har ta kai mutane kadan ne suke ja da shi. Inda yawancinmu muka yarda cewa ba wa mutane ladan kudi na karfafa musu guiwa su kara kokari sosai a aikinsu.

Sai dai kuma wani bincike da ake ci gaba da yi a yanzu a fannin tattalin arziki da tunanin dan adam da makamantansu na nuna wata alaka mai sarkakiya a tsakanin dangantakar kudi da karfafa guiwa da kuma kwazon ma'aikaci.

An fara gudanar da bincike a wannan fanni a farkon shekarun 1970, inda Edward Deci, masanin tunanin dan adam a jami'ar Rochester da ke New York ya yi nazari a kai.

Masanin ya gano cewa daliban da aka ba su ladan kudi kan su lalubo amsar wata tambaya ba kasafai suke ci gaba da aikin ba bayan an ba su kudin, yayin da su kuwa wadanda ba a ba wani kudi ba suke ci gaba da kokarin gano amsar.

Wannan nazari na Deci ya taimaka wajen gano bambanci tsakanin yin abu domin sa kai d kuma yin abu domin samun wani lada (sa kai ya fi bauta ciwo).

Malamin ya ce, ''mutane suna da bukatu guda uku (a hankalinsu), bukataun su ne, mutum ya ji yana da 'yancin kansa, ya ji ya cancanta, sannan kuma ya ji yana da alaka da sauran mutane.''

Biyan kudi kamar yadda binciken Deci ya nuna ba ya biyan wadannan bukatu. Dogaro da yawa a kan ladan kudi yana kawo cikas ga 'yancin mutum wato ra'ayinsa na sa kai na gamu da nakasu kenan, kamar yadda ya ce.

Ya kara da cewa, ''wannan illar da kudi yake yi wa kwarin guiwa yana da tasiri sosai, domin kana bukatar kwazo sosai daga ma'aikatan banki. Kana bukatar masu tunani, da magance matsala, mutane masu basira, wanda kuma amfani da kudi ba zai sama maka irin wadannan mutane ba.''

Wani abin mamaki ma kuma, wasu masana tattalin arziki suna tababar yadda za a ce kudi zai karfafa wa mutum guiwar yin wani abu.

Dan Ariely na jami'ar Duke ta North Carolina a Amurka, ya bayar da wani kyakkyawan misali, inda y ce, ''Idan na roke ka ka sauya min tayar motata, za ka iya taimaka min, amma idan na ba ka dala daya a kan kayi min wannan aikin, ba lalle ka ce 'ah! Bari in taimaki mutumin nan domin in ci wannan kudin nasa ba'.

Maimakon ka yi hakan, sai dai ka ce: 'dala daya kawai a'a ba zan yi wannan ikin a dala daya ba' sai ka ga ba ka da sha'awar yin hakan.'' Abin da ake nufi a nan, idan bangare daya ya bayr da ladan kudi ga bangare daya a wani aiki, hakn n iya karya kwarin guiwar wanda aka ba wa kudin ya yi aikin.

Amma watakila rashin yawan kudin da ake bayar wa a nazarin da Ariely da Deci suka yi, shi ya sa ba za a ce lamarin haka yake hatta a rayuwa ta zahiri ba a harkokin kasuwanci da kudade na duniya.

Domin fayyace lamarin, Ariely da abokan aikinsa, sun dauki wasu kauyawa a Indiya domin su yi wasu wasanni na auna basira da kuzari, inda suka kasa rukunin mutane uku, ake ba su ladan kudin kasar na rupee hudu ko 40 ko 400 a duk wasa daya da suka yi, idan sun samu maki mafi yawa.

Babban ladan da ake bayarwa (rupee 400) daidai yake da kudin da yawancin mutane ke kashewa a yankunan karkara na Indiya a cikin watanni biyar.

Masu binciken sun gano cewa wadanda ake ba wa lada mai yawa sun fi rashin kokari, inda suka samu yawanci kashi 20 cikin dari na abin da aka ware musu.

Su kuwa wadanda aka ware musu lada mafi karanci da na tsaka-tsakiya sun samu kashi 36 cikin dari ne. Ariely ya ce, ''sakamakon da muka samu ya kalubalanci yadda aka dauka cewa kara wa ma'aikaci kwarin guiwa lalle zai sa ya kara kwazo a aiki.''

Daga binciken masanin ya kuma fahamci cewa, yawan ladan kudin da ake ba wa wadannan 'yan Indiya da suka yi nazari a kansu ya shashantar da su kan su dage a kan aikin ta yadda suka mayar da hankalinsu kusan kacokan a kan kudin.

Kuma wannan fahimta ta cewa yawan ladan kudi na sa mutum ta zaku sosai domin samun ladan har hakan ya kawo masa cikas wajen samun nasara, idan aka kara yawn kudin ko aka rage, masana tunanin dan adam ne na Amurka suka fara bayyana ta tun kusan shekaru 100 da suka gabata.

Wannan sa rai na ganin mutum ya yi kokari a yayin da yake cikin wani matsin lamba, ya fi bayyana a harkar wasanni.

Ariely ya gano cewa idan aka sanya wa mutane ladan kudi mai yawa a aikin da ya shafi amfani da jikinsu sukan ci kudi da yawa saboda sukan iya zage damtse su yi da kyau.

Amma idan aiki ne da ya shafi tunani da basira ba sa samun cin kudin da yawa, saboda ba su da iko da kwakwalwarsu sosai kamar yadda za su yi da jikinsu misali, kafa ko hannu.

Hasali ma abin koma baya yake haifarwa, domin idan ka yi kokarin tilasta wa kwakwalwarka domin ta samu natsuwa da basira da kirkirar wani abu sai ta kasa domin aiki ya takura mata.

Masanin tunanin dan adam Kou Murayama na jami'ar California da ke Los Angeles da farko ya yi nazarin kwarin guiwa yadda ya danganci koyo da ilimi.

A yayin wata tattaunawa da masanin kimiyyar aikin kwakwalwa Kenji Matsumoto na jami'ar Tamagawa da ke Tokyo, ya gano cewa fannin nazarinsu yana kallon kwarin guiwa a matsayin wani abu daban.

Murayama ya ce, ''na yi mamaki yadd na ga cewa fannin kimiyyar aikin kwakwalwa na daukar kwarin guiwa a matsayin wani abu kwaya daya mai zaman kansa wanda kawai aiki ne na bayar da lada.''

Shi da Matsumoto daga nan sai suka shirya wata jarrabawa, inda suka bukaci mutanen da za su yi jarrabawar da su su rika danna wani maballi, a duk lokacin da suka ga wani agogo na kwamfuta y kai dakika biyar.

Burin masu binciken shi ne mutanen su yi hakan a cikin kashi daya bisa ashirin na dakika daya (da sauri kenan).

An kasa mutanen rukuni biyu ne, inda rukuni daya suke samun ladan kudi a duk lokacin da suka yi yadda ake so, daya rukunin kuwa ba a ba su ladan komi.

An yi musu jarrabawar ne a cikin wata na'ura mai nuna yadda sassan kwakwalwa ke aiki. Hoton bidiyon kwakwalwarsu ya nuna cewa bangaren kwakwalwar da ke kula da kwarin guiwa ya yi ta aiki sosai a wadanda aka ba su ladan kudi fiye da na wadnda ba a ba su kudin ba.

Murayama ya ce, ''wannan ya nuna kenan ladan kudi yana zaburar da bangaren kwakwalwar da ke kula da kwarin guiwa. Bayan sun yi hutu an sake dawo da su jarrabawar, amma a wannan lokacin ba wadanda za a ba wa wani ladan kudi.

A nan kuma sai hoton bidiyon aikin kwakwalwar tasu na bangaren kwrin guiwa ya nuna cewa wadanda aka ba wa ladan kudi a karon farko, a yanzu kwakawlwarsu ba ta yi aiki kamar a wancan lokacin ba (wato kenan saboda ba maganar ba su ladan kudi).

Wannan ya nuna kenan bayar da ladan kudi yana karfafa wa mutum guiwa yin aiki. Murayama ya ce, ''gaskiya ne cewa bayar da ladan kudi a tsarin gwaji na nuna kwarin guiwa, amma abin da muke bukata shi ne mu tabbatar da kasancewar hakan a yanayi n rayuwar gaske.

A yanzu Muarayama da abokan aikinsa sun fara jarraba haukar hoton bidiyo na aikin kwakwalwa su ga ko wasu abubuwan da ba kudi ba, kamar burin cimma abin da muka sa a gaba ko burin ganin mun fi wasu su ma za su iya shafar aikin kwakwalwa wanda ya shafi kwarin guiwa wanda kuma zai sa mutum kara kwazo.

Dukkanin wadannan nazarce-nazarce ba su ce Bob Diamond da sauranmu za mu fi kwazo idan ba a ba mu ladan kudi ba. Ba shakka kudi yana karfafa wa mutane guiwa su kara kwazo a aiki, amma kuma ladan da ke sa mutne kwazo sosai na iya rage mana sha'warmu ta aiki, kuma hakan ka iya rage kwazonmu.

Deci ya ce, ''ba ina bayar da shawarar cewa kada a biya mutane albashi mai yawa ba a kan aikin da suke yi, abin da nake cewa shi ne ya kamata mu bar tunanin cewa hanyar karfafa wa mutane guiwa shi ne mu ba su lada kan wani aiki da suka yi musamman.

Muna bukatar mu yi tunani a kan yadda za mu mayar da wurin aiki ya zama inda mutane za su samu biyan bukatarsu, kuma su zage damtse a aikinsu su yi da kyau.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Does money really motivate people?