Ko hidimar safiya na iya taimaka ma wurin aiki?

Hakkin mallakar hoto Getty

Yayin da wasu mutanen suke fama domin tashi da safe da wuri, wasu kuwa har motsa jiki, ko darasi da sauran abubuwa suke zuwa, duk kuma kafin su tafi aiki.

Renuka Rayasam ta yi nazari a kai

Tim Powell ba irin mutanen nan ba ne da ke tashi da sassafe. Wanda wannan abin mamaki ne domin yawancin kwanaki yana tashi kafin karfe shida na safe.

A ranakun aiki yakan tashi da karfe shida saura kwata na safe a lokacin da yawancinmu ke ta sharar barci, ya motsa jiki, sanna ya shirya ya nufi wurin aikinsa.

Kafin ya shiga ma'aikatarsa sai ya yi dan tattaki a wani dandali d ke kusa da wurin, domin ya samu natsuwa, kafin ya shiga ya zauna aiki da karfe tara na safe.

A ranakun Alhamis yana tashi daga barci tun karfe biyar da minti 20 na asuba domin ya samu ya halarci darasin koyon Jamusanci.

Powell yana aikin sa'o'i 70 ne a mako a matsayin lauyan kamfani a Nottingham da ke Burtaniya. Yanayin aikin nasa ya sa dole ya yi wani tsari na musamman na abubuwan da yake yi da safe kafin ya fita aiki.

Abubuwan da yake yi da safen suna taimaka masa ya iya yin ayyukansa na rana (na ofis), kamar yadda ya ce.

Duk da haka tashin da yake yi da sassafe ba abu ne da ya zamar masa jiki ba, domin ya ce da wuya a ce bai rama barci ba can gaba a ranar.

Ya ce a hankali a hankali ne ya saba da wannan tsari na abubuwan da yake yi da safe a kullum, domin ba za ka tashi rana daya ba ne ka ce za ka zama wani gwani na gwanaye a ofis ba.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library

Ba Powell ne kadai ba yake da wannan tsari. Ma'aikata da dama masu fama da aiki, wadanda suka yi nasara a harkokinsu, masu tashi da sassafe ne, wadanda za su tashi tun da asuba su yi wasu abubuwan d ke gabansu ba tare da sun rikita tsarin aikinsu ba.

Babbar editar mujallar Vogue, Anna Wintour ta yi suna wajen tashi tun da karfe shida saura kwata na safe ta fara zuwa wasan kwallon tennis kafin ta tafi aiki.

Masana sun yi amanna cewa lokacin da yake tsakanin tashin mutane daga barci da kuma lokacin da za su tafi ofis, lokaci ne da ya dace ka gudanar da wasu ayyukanka wadanda ba su danganci aikin ofis dinka ba.

Wasu motsa jiki suke yi, wasu ganawa da iyalansu suke yi ko kuma rubuta wani littafi. To amma ta yaya za ka iya zama mai sammakon tashi.?

''Yin wani abu kullum abu ne da ya danganci dabi'a,'' in ji Martin Hagger farfesa a fannin nazarin tunanin dan adam a jami'ar Curtin da ke Perth a Australiya.

Hagger ya yi nazarin yadda mutum zai iya tsara dabi'arsa ne. Nazarinsa ya nuna cewa yin tsarin wani abu na yau da kullum, ka iya kasancewa wata hanya mai kyau ta kirkirar dabi'a, domin hakan na rage lokacin da za ka bata na yanke shawara kan wani abu.

''Idan kana da wani tsari na yin abu kullum yadda ka shirya, to ko da kai mutum ne da ba ka kwanciya da wuri za ka iya tashi da sassafe kuma ka yi ayyuka masu wuya da safe.''

Hagger ya yi amfani da bincikensa a rayuwarsa ta yau da kullum. Yawancin kwanaki yana tashi da karfe shida na safe ya motsa jikinsa sannan ya karya kumallo kafin ya hallara a wurin aikinsa da karfe takwas na safe.

Ya ce idan har ya bai motsa jikin nasa ba ya bari sai ya dawo daga aiki, ya san cewa zai gaji a lokacin sosai, ko kuma wasu abubuwan su dauke masa hankali.

Hakkin mallakar hoto iStock

Saboda haka ya ce tun kafin ya kwanta sai ya ware kayan sawarsa na motsa jikin, ya saita kararrawar agogonsa, domin ya tashi da safe a kan lokaci.

To amma fa a sani babu wasu ka'idoji na lalle. Kwararru sun ce babu wani tsayayyen lokaci da ya dace mutum ya fara harkokinsa da safe, domin kowane mutum yana da tsarin abubuwan da yake son yi da burinsa da irin harkokin da ke gabansa da kuma yanayin rayuwarsa, muhimmin abu dai shi ne ka ware lokacin da za ka rika yin abubuwanka da safe, wanda ya dace da kai.

Kuma idan tashin da safe yana neman ya gagare ka, to sai ka saita kararrawar agogon naka, lokacin ya dan dawo baya kullum har sai ka saba tashi da wuri daidai yadda kake so.

''Lokaci ne da ba za a iya dauke maka shi ba cikin sauki,'' in ji Laura Vanderkam marubuciyar littafin 'What the Most Successful People Do Before Breakfast', ta ce sauran al'ummar duniya za su samu abin da suke bukata da rana. Safiya ce lokacinka.''

Abin da ka ba fifiko

Vandekam ta yi nazarin rayuwar mutanen da suke da ayyuka masu cin lokaci inda ta gano cewa, mutanen suna amfani da safiya ne, su yi ayyukansu na kashin kansu wadanda suka ba fifiko da kuma ayyukan da ke gabansu wadanda suke bukatar natsuwa da kwarewa.

Ta ce, ''idan kana da wani da kake son yi, amma ba ka samun wadataccen lokaci a rayuwarka, to ina ba ka shawara ka jarraba yinsa da safe.''

Ta kara da cewa tsara yin ayyukanka da safe zai sa ka rika samun damar kwanciya da wuri, kuma ka yi watsi da lokutan da ba sa tsinana maka wani abu ko ba ka iya yin komai da yamma, kana shiga intanet da kallon talabijin.

Hakkin mallakar hoto iStock

Mutanen da ta yi bayaninsu a littafinta suna amfani da safiyarsu ne wajen motsa jiki ko ibada ko zama da iyalansu.

Haka kuma mutanen da ba sa kwanciya da wuri da daddare za su iya yin ayyukansu da dama da safe kamar yadda mutumin da yake sammakon tashi yake iya yi kamar yadda Mareike Wieth ta sashen nazarin kimiyyar tunanin dan adam a kwalejin Albion da ke Michigan ta ce, wadda ta yi bincike kan yadda lokacin rana zai shafi yadda za a magance matsala.

Ta bayyana cewa a lokacin mutane na rana wato ganiyar lokacinsu, sun fi natsuwa da kuma kauce wa duk abin da zai dauke musu hankali.

Roy Baumeister da ke jami'ar jihar Florida, ya ce, ''kudiri abu ne mai muhimmanci wajen kaucewa abin da zai dauke maka hankali, da sabawa da bukatu na waje da yanke shawara, wanda duk abubuwa ne da kake bukata ka cimma nasara.''

Amfani da wata dabara taka da safe zai ba ka damar adana kudurinka domin ka yi amfani da shi wajen aiwatar da ayyuka masu wuya.

Ya ce, ''abu mafi kyau da ya kamata ka yi shi ne ka tsara safiyarka da kyau.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can a morning routine make you better at your job?