Me za ka yi in ba ka jin daɗin aikinka?

Hakkin mallakar hoto SPL

Wasu ma'aikatan ba sa jin daɗin aikinsu saboda aikin ya gundure su, to idan ka samu kanka a irin wannan yanayi, za ka ajiye aikin ne ka bazama neman wani ko kuma ya za ka yi?

Chana R Schoenberger ta duba mana lamarin

Tambaya: Na yi shekara da shekaru a aikin da nake ba tare da an yi tunanin sauya mini wuri ba, har ta kai ina iya aikin kusan cikin sauki ba da wata wahala ba sosai.

A ranakun da nake aiki daga gida, kusan in ce kamar ma ba na aiki ne. Saboda haka na yi tunanin ma na bar aikin, to amma sai na ga idan na bar aikin ba tare da wani a hannu ba, wani kamfanin ba zai dauke ni da daraja ba.

Me ya kamata na yi?

Amsa: Akwai hanyoyi biyu kawai da za ka iya barin aikinka domin radin kanka: ka nemi wani aikin ko kuma ka bar wannan aikin ka tafi neman wani sabon mukamin.

Yadda har yanzu mutane ba su manta da matsalar tattalin arziki da ta afka wa duniya ba a 'yan shekarun baya, ma'aikata da dama suna matukar jin tsoron barin aikin da suka dade suna yi idan ba wani suka samu ba a hannu ba.

Duk yadda lamari ya kasance, abu ne da bai dace ba ka sassauta yadda kake aiki, in ji Gail Golden, kwararriya a kan tunanin dan adam a harkar ma'aikata, kuma kwararriya a kan shugabanci, wadda ke Chicago a Illinois.

Golden ta ce, ta fannin ka'idar aiki abu ne da yake a zahiri wanda kuma ya dace ka sadaukar da kanka ga aikinka. Wannan shi ne abin da albashinka ke saya. 'abu ne da ya dace a yi.'' In ji Golden.

Idan ka ki yin aikinka, za ka iya bata suna da mutuncinka, wanda ya samo asali daga alfaharin da kake na irin nasarar da ka samu a aikin.

Golden ta ce, ''idan ya kasance ba ka samu wani aikin ba nan da nan, to tarihin rashin kokarin da ka yi a aikin zai iya haifar maka da maras ido. Za ma ka ji cewa kana son sauya shawara ka tsaya a wurin aikinka.''

Wani kalubalen: yin aiki daga gida wata dama ce ta musamman, idan aka same da laifin rashin kiyaye ka'idar da aka yi maka, ta hanyar yin wasu ayyukan na wasu daban, ko kuma kana fafutukar neman wani aikin da ya fi wannan, za ka iya bata tsarin aikin da aka shirya na wasu a kamfanin naku, in ji masaniyar.

Zabin da kake da shi a bayyane yake: ko dai ka rika neman wani aikin a lokacin hutunka (na rana) ko kuma ka bar aikin da farko.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. When professional boredom hits, is it fair to coast?