Yadda ya kamata shugaba ya kasa

Daukar alhakin kuskure ko matsala idan ta faru ita ce babbar alama ta shugaba na-gari. Ka san yadda za ka iya bullo wa lamari har ka yi galaba idan abubuwa suka daburce?

Eric Barton ya yi mana nazari

Tun kafin fara gasar kofin Amurka a Oman a watan Fabrairu, Sir Ben Ainslie ya gamu da kalubale. Ainslie, dan wasan tseren kwale-kwale da ya fi samun lambobin gwal na Olympics a tarihi, inda yake da lambobi biyar, shi ne kyaftin din kungiyar tsere ta Land Rover BAR, wanda ya yi suna wajen tasowa daga baya ya zo ya yi nasara.

A ranar karshe ta tsere a Oman a watan Fabrairu, iska ba ta da karfi, amma Ainslie ya yi kuskuren fahimtar hakan, ya yi gaggawar tashi a tseren, wanda hakan ya sa aka hukunta shi, wanda hukuncin laifin hakan shi ne ya bari abokan tserensa su fara tashi kafin ya biyo su daga baya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan tseren kwale-kwalen Ben Ainslie a gabar tekun Oman

Duk da wannan hukunci da aka yi masa, a zagaye na uku Ainslie ya dage daga matsayi na uku har ya zo na farko tawagarsa ta yi nasara.

A waiwayen da ya yi yanzu, Ainslie ya ce akwai babban dalilin da ya sa tawagarsu ta iya samun nasara a wannan gasa. A matsayinsa na kyaftin, Ainslie bai yi wata-wata ba a lokacin ya dauki nauyin kuskuren da ya faru, wannan ya sa suka mayar da hankali kan tseren ba tare da sun yi ta sukar juna da laifi ba.

Kyaftin din ya ce, '' da wasu 'yan tseren ne da ban dace da su ba, da sai su yi ta suka na cikin fushi. Amma wadannan sun fahimci cewa haka lamari yake za a iya samun kuskure, amma kuma yin kuskure ba yana nufin karshenku ba kenan.''

Wannan ba abu ne mai sauki ba a wurin yawancin shugabanni, su dauki nauyin kuskure. Ka amsa cewa kai ne ka jawo aka samu kuskuren da ya sa kamfani ko hukumarku ko rundunarku ta yi rashin nasara ba abu ne da kowane shugaba zai iya ba.

Amma idan ka daure ka amsa laifinka kuma hakan ya zamar maka darasi, to wannan ita ce alamar shugaba na-gari.

Yadda da kuskure

Al'adar mutane ce idan aka samu nasara a abu su ce su ne sanadi, idan kuma aka samu sabani, wato aka yi rashin nasara sai su dora laifin a kan wani, in ji Oliver Donoghue, manajan darektan kamfanin daukar ma'aikata na Nonstop Recruitment Schweiz AG a Prague.

A kamfanoni da yawa wannan ke haifar da al'adar da ke sa mutane ba sa daukar alhakin wata matsala, domin gudun hukunci.

Donoghue, ya ce, ''abin da kake bukata ka koya a nan shi ne ba wai cewa kuskuren ne zai nuna yadda kake ba, yadda ka yi da kuskuren shi ne ke da muhimmanci.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amsa laifin kuskuren tawagarsu ta sa kyaftin Ben Ainslie ya kai su ga nasara

Kusan duk mutane ko kungiya haka suke son kauce wa daukar laifi idan an samu kuskure in ji Jan Hagen farfesa a makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta ESMT da ke Berlin.

Hagen ya yi nazari kan martani ko matakin mutane daban-daban, kama daga ma'aikatan ofis da na jirgin sama, wadanda ke cikin damuwa. A bangaren matukin jirgin sama, Hagen ya gano cewa yawanci ma'aikatan jirgi ba sa ba wa babban matukin jirgin rahoton wani abu maras kyau, saboda fargabar abin da lanbari maras kyau zai iya sa mutum.

A fannin kasuwanci, yawanci matsakaitan manajoji sukan sadda kansu kasa ne wato ba sa fada idan matsala ta faru, domin gudun kada a dora musu laifi idan suka bayar da rahoto, in ji Hagen. Ya ce, ''ba abu ne mai sauki ba wani ya amince da daukar laifi ko da kuwa a babban kamfani ne.''

Hagen ya ce matsalar irin wannan hali na kin amsa laifi shi ne, za ka rasa damar gyara kuskurenka. Abin da ya fi shi ne ka yarda da gazawarka, ka yi nazarin abin da ya haddasa kuskuren, wanda hakan zai sa ka san yadda za ka kaucewa yin hakan a gaba.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Abu ne da yake da muhimmanci manajoji su rika daukar nauyin kuskure idan ya faru in ji David Rodnitzky, shugaban kamfanin harkokin yada watsa labarai na 3Q Digital, a California da ke Amurka.

A lokacin da ka dauki nauyin kuskuren, sai ka bayyana yadda lamarin ya faru, da darasin da ka koya, da kuma yadda za ka kauce wa sake aukuwar hakan a gaba.

Irin wannan bayani zai taimaka maka a wurin shugabanninka ko masu hannun jarin kamfaninku, haka kuma amincewa da kuskuren zai kyautata tsakaninka da ma'aikatan da ke karkashinka in ji Rodnitzky.

Dora wa kanka laifin wani kuskure, maimakon wani a cikin ma'aikatanka na jawo maka biyayya. Shugabanni na-gari a ko da yaushe su kan fahimci cewa daukar nauyi ba ta hada da nasara ba kadai in ji Rodnitzky.

Ajiye ra'ayinka

A kwanannan Cristina Mariani-May ta san yadda abu ke da wuya ta yarda cewa ta yi kuskure. Kamfanin barasa na Banfi Wines da ke New York, wanda ke kai barasar Italiya zuwa kasashen duniya tun shekara ta 1919 mallakar gidansu ne, kuma tun 1978 suka mallaki gonar Tuscan vineyard.

Hakkin mallakar hoto Banfi Vinters
Image caption Yardar Cristina Mariani-May ta yi kuskure ta ba kamfaninsu damar cigaba.

Mahaifinta ne John Mariani shekara bakwai da ta wuce ya kawo shawarar su bude otal a wani filinsu a Italiya. A yayin tattaunawar ne, ya ba da shawarar cewa kamfanin nasu shi zai tafiyar da otal din, amma ita kuwa Mariani-May ta ce a'a kamata ya yi su kawo wani kwararre ya gudanar da shi.

Bayan sun kasa cimma matsaya ne, sai ta yarda ta yi nazari a kan lamarin kuma bayan shekara biyu, sai ta sheda wa mahaifin nata cewa ta yi kuskure, shawararsa ita ce daidai.

Hakkin mallakar hoto Castello Banfi il Borgo
Image caption Otal din Castello Banfi il Borgo

A yanzu wannan otal Castello Banfi il Borgo wanda yana daya daga cikin wadanda suka yi fice a kasar ta Italiya da bai tabbata ba, idan da a ce ba ta ajiye ra'ayinta ba, ta kuma yarda da kuskurenta.

''Wannan na daya daga cikin tsarin kyakkyawan shugabanci. Kada ka kudiri aniyar yin wani gagarumin aiki da wani ra'ayi na kanka, kuma ya kasance a shirye kake ka amince da kuskurenka idan ka yi

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to fail like a leader